Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Ga bayani mai kunshe da kyawawan ayyukan da ya kamata ma’aurata su dage gabatarwa don inganta so, kauna da zamantakewar aurensu cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, da fatan […]

Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)
Ma’aurata: Abubuwan Gabatarwa cikin Ramadan (2)

Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikin sa, amin. Ga bayani mai kunshe da kyawawan ayyukan da ya kamata ma’aurata su dage gabatarwa don inganta so, kauna da zamantakewar aurensu cikin wannan wata mai albarka na Ramadan, da fatan Allah Ya sa mu dace da dukkanin alheran dake cikin wannan wata, amin

Yawaita yabo da godiya ga Allah Madaukakin Sarki: Ma’aurata su tuna dimbin ni’imomi da rahamomin da Allah Ya azurta su da shi, su yi maSa godiya jikakkiyar godiya daga can kasan ransu. Misali Allah mun doge maKa da Ka ba mu kaza da kaza, Allah mun gode maKa da Ka azurta mu da kaza; Allah muna matukar godiya da Ka yaye mana kaza; ba dole sai kayan alatu ba, har ta kyakykywar danganta da kyawawan shauki da ilimi da karfin imani da damar karatun Kur’ani da zikiri da Sallah duk abubuwa ne da ya kamata dukkan Musulmi su rika yawan tunano su suna nanata godiyarsu ga Allah; alfanun haka shi ne ita kanta godiya ga Allah ibada ce sannan Allah Madaukakin Sarki Ya yi alkawarin kari kan ni’mar da bawa ya gode maSa game da ita. Don haka in kana son ka kara yawan tsayar da Sallah da yawan ibada, ka gode wa Allah a kan wacce Ya ba ka ikon yi yanzu.

* Bude hanyoyin sadarwa tsakanin juna; domin sadarwa ita ke raya zumunta kuma zumunci na tsakanin miji da mata yana da matukar muhimmanci a rayuwarsu da addininsu; don haka sai ma’aurata su bude hanyar sadarwa da ke tsakaninsu sosai ta hanyar yawan zama suna tattauna abubuwan rayuwarsu, matsalolinsu da hanyoyin magance su; sannan su watsar da duk wani abu da ke kawo cikas ga dorewar sadarwa a tsakaninsu, in ma wani laifi ne, sai a yafe wa juna kuma a mance da shi take yanke. Kuma ma’aurata su zauna su rubuta burin da suke so su cimmawa a cikin dangantakarsu, kuma su yi ta kokarin aiwatar da shi a cikin wannan wata da kuma bayansa.

* Yin ayyukan ibada tare da yin ayyukan gida, musamman na hada abincin buda-baki tare, duk abubuwa ne da za su kara dankon so da kauna a tsakanin ma’aurata.

* Yin buda-baki waje daya, maigida ya hada iyalinsa duka, a zauna a ci abinci cikin kwano daya; yin haka zai yi matukar kara dankon zumunci da kauna a cikin iyali duka.

Abubuwan kara dankon soyayya

* Zuwa Sallar Tarawihi tare da kuna karatun Kur’ani da saurare ko yin wani zikiri kamar addu’ar da ake karantawa in an kama hanyar zuwa masallaci.

* Bayan kammala gabatar da Sallah, maigida maimakon ya yi tasbihi da yatsunsa, sai  ya kama yatsun uwargidansa ya yi tasbihin da su, haka uwargida ma na iya yin haka.

* Maigida ya riki al’adar kullum ya rika rungumar uwargidansa kafin ya fita zuwa wajen aiki ko masallaci; wannan koyi da Sunnah ne domin Ya tabbata cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yakan sumbaci iyalinsa lokacin da zai fita zuwa masallaci. Uwargida kuma ta riki al’adar tarbar maigida da murmushi da shiga mai kyau, tare da ’yar karamar sumba ko da ta saman goshi ne ko a kumatu.

* Ma’aurata su samu wani lokaci na musamman su ci abinci tare komai kankantarsa, cikin kwano daya, suna masu ciyar da junansu, kuma suna masu kallon kwayar idon junansu cikin kauna da bege, wannan zai kwararar da soyayyar juna cikin zuciya.

* A tanadi lokaci na musamman koda minti 15 a kowace rana don raya soyayya, ta hanyar yin hirar raha mai cike da kalaman nuna so da kauna da yaba wa juna da sauran abubuwan da suka dace da ma’aurata da yanayinsu.

* Ma’aurata su riki dabi’ar aika wa juna sakonnin tes masu dadi da kwantar da rai.

* Haka nan ma’aurata na iya samun Hadisai masu kalmomi kadan masu cike da bushara ga muminai su rika aika su a sakonnin tes ga junansu.

* A dage da karin kyautata wa juna da karin hakuri da juna da karin taimaka wa juna cikin wannan wata, wannan zai kara dankon soyayyar da ke tsakanin ma’aurata.

Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.