Ma’aurata: Abubuwan gabatarwa ranar Sallah
Assalamu alaykum. Ga bayani kan abubuwan da ya kamata ma’aurata su dage da ba muhimmanci ranar Idin karamar Sallah in Allah Ya kai mu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.Sunnonin Shagalin Sallah:Ranar murna, ranar ibada: Mu sani ya ’yan’uwa, duk da kasancewar ranar […]
Assalamu alaykum. Ga bayani kan abubuwan da ya kamata ma’aurata su dage da ba muhimmanci ranar Idin karamar Sallah in Allah Ya kai mu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Sunnonin Shagalin Sallah:
Ranar murna, ranar ibada: Mu sani ya ’yan’uwa, duk da kasancewar ranar Sallah rana ce ta murna da shagali da jin dadi, amma abu mafi muhimmanci a cikin wannan rana shi ne kasancewarta kuma rana ta ibada. Don haka ibada ita ya kamata ma’aurata maza da mata su fi bai wa muhimmanci sama da dafe-dafen abinci da shiryen-shiryen shagalin Sallah.
1-Babbar ibada ta farko a wannan rana ita ce fitar da zakkar fidda kai tun da sassafe, a raba ga mabukata kafin a tafi Sallar Idi. In har aka makara sai bayan an sauko daga Sallar Idi aka bayar, to an rasa wannan lada ta zakkar fidda kai.
2-Babbar ibada ta biyu a wannan rana ita ce Sallar Idi, wacce take wajibi ga dukkan Musulmi maza da mata. Don haka kuskure ne abin da mafi yawa daga cikin matan Hausawa ke yi na kin zuwa Sallar Idi kawai don yin dafe-dafe da soye-soyen kayan abincin sallah. Ai zuwa Idin nan shi ya fi alfanu sama da komi. Don haka ne ma a lokacin Rayuwar Annabi SAW duka matane ke zuwa filin Idi har mata masu jinin haila Annabi SAW ya umarce su da zuwa wajen da ake Sallar Idi amma su tsaya daga baya. Haka har macen da ba ta da hijabin da za ta rufe jikinta, Annabi SAW ya umarce ta da ta nemi aron na ’yar uwarta ta tafi wajen Sallar Idin. Wannan duk yana kara nuna mana matukar muhimmancin zuwa Sallar Idi ga kowane Musulmi ba wai maza da kananan yara kadai ba. Don haka duk wata uwargida Musulmar kwarai ta tabbatar, ta karasa duk wani aikin abincinta kafin lokacin zuwa Idi; in kuma ba halin haka to sai ta yi hakuri sai ta dawo ta karasa domin zuwa Idin nan ya fi komi muhimmanci a wannan rana.
3-Daga cikin kyawawan sunnonin da Annabi SAW yake gabatarwa kafin tafiya Sallar Idi sun hada da: Yin wanka; yin asuwaki; sa sabbin kaya ko mafi kyawo daga cikin tsofaffin; sanya turare; cin mara ta dabino, watau 3, 5 ko 7; sai kuma canza hanyar dawowa gida, watau hanyar da aka bi aka je masallacin Idin, sai a canzawa a bi wata daban wajen dawowa gida in da halin yin haka.
4-Sadaka: Haka kuma yana daga cikin ibadojin murnar Sallah yin sadaka ga talakawa da mabukata; domin Annabi SAW ya yi umarni da yin hakan ga taron mata bayan idar da Sallar Idi, sai ya yi masu wa’azi kuma ya umarce su da bayar da sadaka; kuma take suka bi wannan kyakykyawan umarnin na Manzon Allah SAW, inda suka rika ciro gwala-gwalensu suna bayarwa sadaka saboda Allah. Don haka ya ’yan uwa ma’aurata, musamman mata, mu yi kokarin yin koyi da wannan Sunna ta Manzon Allah SAW ta hanyar bayar da sadaka a wannan rana ta shagalin babbar Sallah. Ba dole sai mutum ya wadata sosai ba sannan zai yi sadaka, in dai mutum ya yi ta da kyakykyawar niyya to Allah Madaukakin Sarki kuwa zai cika masa ladarsa. Misali, kamar mutum ya bayar da sadakar kudi ga masallacin unguwarsu; ko ya sayi batirori don sa wa a lasifikar masallacin; ko katuwar fitila mai haske sosai; tabarmi, butoci da sauransu. Ko taimakon wani mabukaci, ko taimaka ma gidajen marayu da kudi, sutura ko kayan abinci. Ko sayen magani ga marasa galihu a asibiti, da sauran kyawawan ayyuka da mutum ya ga sun dace sai ya aikatar don dacewa da wannan kyakykyawar Sunna ta Manzon Allah SAW.
5-Murna da Nishadi: Abu na gaba mafi muhimmanci a wannan rana bayan ibada, shi ne kasancewarta ranar murna ranar shagali da nishadi. Don haka yana da kyau kowane Musulmi yin murna a wannan rana, ta hanyar jin dadin ranar a cikin ransa, da bayyanarwa a fuska, da kokarin sa ’yan uwa da makwabta cikin nishadi ta hanyar kyakykyawar gaisuwa mai cike da raha, kalmomin kyautatawa da kuma yin abubuwan kyautatawa da jinkai ga kowa a wannan rana. Haka nan ya halatta yin wakokin nishadi masu dauke da kyawawan kalmomi, musamman mata da yara kanana, Sunna ce mai kyau su aikatar da wannnan a ranakun murnar Sallah. Misali, yana da kyau a tara yaran unguwa a gabatar da wani abun wasa da jin dadi wanda zai sanya su cikin murna da farin cikin zuciya; ko macen aure ta tara ’yan matan unguwa su yi wasannin gada ko wakoki cikin wasa da dariya da raha, wannan duk ayyukan alheri ne wadanda in mutum ya aikata su zai samu lada ga kuma nishadi da jin dadin da zai ji a zuciyarsa.
6-Ranar Soyayya: In muka bibiyi sunnonin Manzon Allah SAW za mu ga cewa, ranar Idin Sallah rana ce ta soyayya da romansiyya da kyautatawa tsakanin ma’aurata. Kamar yadda aka ruwaito Uwar Mumunai A’isha Radhiyallahu Anha ta ce, a ranar wata Idin, ya kasance mutanen Habasha suna wasa da sulke da mashi a harabar masallaci, sai Annabi SAW Ya katangeta da jikinsa, ta yadda kuncinta yana bisa kuncinsa kuma ya yi ta jiran ta har sai da ta kalla ya ishe ta. Wannan darasi ne mai kyau kuma abin koyi ga ma’aurata ta yadda za su sadaukar da lokacinsu wajen nuna kauna da kulawa ga junansu a wannan rana ta Idi. Don haka yana da kyau ga duka maza da mata su yi wani abu na sadaukarwa da nuna kulawa ga junansu ranar Sallah don su dace da wannan kyakykyawar Sunna kuma su ji dadi da nishadin da ke cikin kyautata wa ga juna.
7-Sauran kyawawan ayyuka a wannan rana ta Sallah sun hada da kure adaka wajen kwalliya da kuma yawon sada zumunci ga ’yan’uwa da abokan arziki.
Da fatan Allah Ya sa a yi shagalin Sallah, a kare lafiya, amin. Kuma Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.