Ma’aurata dubu 40 suka rabu a Beijin don kauce wa haraji

Ma’aurata kusan dubu 40 ne suka rabu a birnin Beijin ta kasar Sin don gudun biyan haraji, inda a ka’idar dokokin kasar ake saukaka wa wadanda aurensu ya rabu, wajen biyan harajin kadarori a kasar. Jartidar Beijin Youth Daily, ta ruwaito wani jami’in hukuma na cewa, ‘kimanin kashi 12 cikin 100 na ma’auratan birnin sun […]

Ma’aurata dubu 40 suka rabu a Beijin don kauce wa haraji
Ma’aurata dubu 40 suka rabu a Beijin don kauce wa haraji

Ma’aurata kusan dubu 40 ne suka rabu a birnin Beijin ta kasar Sin don gudun biyan haraji, inda a ka’idar dokokin kasar ake saukaka wa wadanda aurensu ya rabu, wajen biyan harajin kadarori a kasar. Jartidar Beijin Youth Daily, ta ruwaito wani jami’in hukuma na cewa, ‘kimanin kashi 12 cikin 100 na ma’auratan birnin sun rabu cikin watanni tara na bana, inda kuma aka samu kashi 41 cikin 100 na wannan kaso a bara.’
A watan Maris din bana, kasar Sin ta bullo da biyan hasrajin kasha 20 cikin 100 na ribar cinikin kaddarori (gidaje da filaye).
Wannan sabuwar doka na da tasgaro, inda aka yanke cewa idan ma’aurata suka rabu, to za su iya sayar da kadararsu ba tare da an dauki wani haraji ba, kuma ina iya sake yin aure ba tare da wata matsala ba. Jaridar dai ta bayyana cewa yawan rabuwar aure ya karu fiye da na shekarar da ta gabata. A da kashi biyu cikin 100 kawai ake karba na kudin harajin.
Ofishin rajistar aure da rabuwarsa da ke birnin Shangai, ya rubuta baro-baro, cewa: “Akwai hadarin da ke tattare da hada-hadar kasuwancin kadarori, ku yi tunani kafin ku raba aurenku,” kamar yadda Jaridar ta Beijin Youth Daily ta ruwaito.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan