Ma’aurata sun rasu rana daya bayan sun yi zaman aure na shekara 6o
Wadansu ma’aurata masu suna Tom da Delma da suka kwashe shekara 60 suna zaman aure sun rasu a rana daya. Ma’auratan sun rasu ne da bambancin sa’a daya a tsakaninsu suna rike da hannun juna a gadon asibiti. ’Yar mamatan mai suna Donetta ta ce wannan shi ne babban burinsu bisa yadda suka dade suna […]
Wadansu ma’aurata masu suna Tom da Delma da suka kwashe shekara 60 suna zaman aure sun rasu a rana daya.
Ma’auratan sun rasu ne da bambancin sa’a daya a tsakaninsu suna rike da hannun juna a gadon asibiti.
’Yar mamatan mai suna Donetta ta ce wannan shi ne babban burinsu bisa yadda suka dade suna rayuwa tare tun kafin su yi aure, “Babban burinsu a duniya shi ne su bar duniya rana daya. Wannan shi ne abin da suka dade suna fata, wato su bar duniyar nan tare, kamar yadda suka zauna tare a cikinta. Babu wani abin da suka fi fata kamar yiwuwar hakan, kuma sun samu,” ’yarsu Donetta Nichols ta shaida wa kafar yada labarai ta Click 2 Houston.
Ma’auratan sun rasu ne a asibitin lura da wadanda suka dade suna jinya na Tedas, kuma sun rasu ne mijin yana da shekara 84 ita kuma matar na da shekara 82.
’Yarsu Nicholas ta ce iyayensu sun hadu ne tun suna kusan shekara 20 a duniya ta sanadin abokansu da suke zaune a Florida.
Mamatan sun rasu suna da ’ya’ya biyu da jikoki bakwai da tattaba kunne bakwai.