Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43
Kotu ta ce auren da ake yawan saki, sannan a sake daura auren a tsakanin ma’auratan cin zarafin doka ne.
Wasu ma’aurata ’yan kasar Australia da suka yi aure kuma suka sake rabuwa da juna har sau 12 a cikin shekaru 43 da suka gabata, a yanzu ana gudanar da bincike a kan zargin zamba tsakaninsu.
’Yan sanda a birnin Vienna na kasar Australia a halin yanzu suna gudanar da bincike a kan wani lamari mai ban mamaki, inda wasu ma’aurata da suka yi aure sannan suka rabu har sau 12 a tsawon shekaru 43, domin yin amfani da wata doka da ta ba su damar karbar makudan kudade.
- Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa
- Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna
Ana zargin tsofaffin ma’auratan da laifin kitsa kowace rabuwa ce a takarda don matar ta samu a biya ta kudin sallama Dala 28,300 kwatankwacin Naira miliyan 43 da dubu dari 440 da dari 783, da aka ba ta bayan mutuwar mijinta na farko ta 1981.
Sun yi amfani da wata dokar kasar Australia da ta ba wa matan da ba su da aure damar a biya su kudin sallama matukar ba ta yi aure ba.
A kowace shekara biyu da rabi, za ta karbi fansho sau 2.5 na zaman zawarci na shekara-shekara, don haka duk shekara uku ko fiye da haka ita da mijinta na biyu za su rabu don ta sami kudin, sa’an nan kuma su sake yin wani auren.
Dabarar yaudarar ma’auratan ta bayyana ne a watan Mayun 2022 lokacin da Cibiyar Inshorar Fansho ta ki sake biyan matar da mijinta ya rasu kudin fansho, duk da rabuwarta a karo na 12 da mijinta na biyu.
Wani bincike ya nuna cewa, ma’auratan sun sake rabuwa, sannan suka yi gaggawar sake daura wani auren duk bayan shekaru uku, a daidai lokacin da matar za ta karbi kudin sallamarta.
Wani bincike da Hukumar Binciken Laifuka ta Graz ta gudanar ya nuna cewa, masu rabuwar auren sun kasance tare a gida daya, suna dafa abinci tare, har ma da kwanciya a gado tare.
A cewar makwabtan nasu, wadanda akasarinsu ba su da masaniya kan al’adar aurensu, sun kasance ma’aurata abin koyi kuma ba su taba rabuwa ba.
Halin nasu ya ankarar da hukuma gano cewa, suna amfani da wannan dabara sama da shekara arba’in.
Hukuncin da Kotun Koli ta yanke a ranar 12 ga Maris, 2024 ya bayyana cewa, “auren da ake yawan saki, sannan a sake daura auren a tsakanin ma’auratan cin zarafin doka ne, idan ba a fasa auren ba, kuma aka yi saki ne kawai don a tabbatar da biyan diyyar kudin fansho ga gwauruwar.”
Ma’auratan na fuskantar zargin yin zamba, inda masu gabatar da kara suka yi zargin cewa sun yi almubazzaranci da kudin sallamar da ya kai Dalar Amurka 341,000 kwantankwaci Naira miliyan 516 da dubu dari 761 da dari 483 da 37 a cikin shekara 43 da suka gabata.
Sai dai, hukumomin Australia ba su amince da rabuwar aure na 12 da ma’auratan suka yi ba, don haka ma’auratan za su fuskanci tuhuma tare.