Ma’auratan da ke da kanjamau sun haifi laifiyayyun ’ya’ya uku a Kongo
Wasu ma’aurata, Hubert da Jeanne Mwangaza da ke fama da cutar kanjamau, sun haifi ’ya’ya uku lafiyayyu a Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo, kamar yadda jaridar The Huffington ta ruwaito daga Hukumar Kula da Ilimin Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF).A wani bincike da Hukumar UNICEF ta gudanar, a Afirka Yamma da Sahara, an gano cewa duk […]
Wasu ma’aurata, Hubert da Jeanne Mwangaza da ke fama da cutar kanjamau, sun haifi ’ya’ya uku lafiyayyu a Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo, kamar yadda jaridar The Huffington ta ruwaito daga Hukumar Kula da Ilimin Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF).
A wani bincike da Hukumar UNICEF ta gudanar, a Afirka Yamma da Sahara, an gano cewa duk kokarin da miji zai yi wajen tallafa wa matarsa a lokacin da take rainon ciki, babu tabbacin cewa zai kare abin haihuwa daga kamuwa da cutar kanjamau ko mai karya garkuwar jiki, kamar yadda cibiyar nazari ta Aidsmap ta ruwaito.
“Tallafin iyaye maza ba za a ce ba shi da amfani ba, a lokacin da mace ke dauke da juna biyu, musamman a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar kanjamau,” a cewar Dokta Chewe Luo, wani Babban Jami’in Bayar da Shawara kan cutar kanjamau da mai karya garkuwar jiki.
A tsakanin shekarun 1999 zuwa 2005, wasu ma’aurata, Witness da Edward suka yi aure bayan da aka tabbatar sun kamu da cutar kanjamau. “Muna da zummar ci gaba da jin dadin rayuwa duk da irin halin da muke ciki,”a cewar Edward, don haka ma ya sayi keke da yake amfani da shi, wajen daukar iyalinsa zuwa cibiyar kula da lafiya. Don haka ’yar da Witness ta haifa har ta kai shekara hudu babu wata alama da ta nuna ta kamu da cutar kanjamau ko mai karya garkuwar jiki (HIb/AIDS).
A cikin al’ummomi da ke Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda Hubert da Jenne ke zaune akwai dimbin jama’a da ke fama da cutar kanjamau, don haka ake yi wa mata masu juna biyu gwaji, ta kayadda za a hana jariransu su kamu da cutar. Kuma koda an samu mace na dauke da kwayoyin cutar, matukar mijinta ya kamu da cutar, to babu wanda zai nuna amta kyara , ballantan a tsangwameta. Kuma ma’aurata irin wadannan kan tsara rayuwarsu wajen kula da ’ya’yan da suka haifa. Domin a irin wannan shirin ne ya sanya kullum sai Jeanne ta sha kwayar magani daya. Saboda haka ta yi sa’ar haihuwar ’ya’ya wadanda ba su dauke da kwayar cutar.