Ma’auratan da suka yi shekara 35 za su rabu saboda mace daya ce ta shayar da su
Wasu ma’aurata a kasar Saudiyya za su fuskanci rabuwar aure bayan suyn shafe shekara 35 a tare, a daidai lokacin da wata gyatuma ’yar shekara 80 ta bayar da shaidar cewa mace daya ta shayar da su, tun suna kananan, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.Wannan gyatuma ’yar kasar Yemen, ta bayyana wa […]
Wasu ma’aurata a kasar Saudiyya za su fuskanci rabuwar aure bayan suyn shafe shekara 35 a tare, a daidai lokacin da wata gyatuma ’yar shekara 80 ta bayar da shaidar cewa mace daya ta shayar da su, tun suna kananan, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta ruwaito.
Wannan gyatuma ’yar kasar Yemen, ta bayyana wa wata kotun Najran cewa wadannan miji da matar da ke da ’ya’ya takwas a tsakaninsu, bai kamata su ci gaba da zaman aure ba, bisa tanadin shari’ar Musulunci.
Akwai yiwuwar kotu ta yi watsi da hukuncin, ganin cewa mace ce ta bayar da shaida, al’amarin da masana addinin Musulunci suka dade suna ta takaddama a kai.
Mabiya mazahabar Hanafi, sun dauka cewa za a iya amfani da wannan shaidar ne idan maza biyu ko namiji da mace suka bayar da ita, amma a Shafi’iyya kuwa, za a iya amfani da shaidar mta hudu.
Su kuwa mabiya mazahabar Malikiyya, sun yadda da cewa mace daya namiji daya za su iya bayar da irin wannan shaida a amince da ita, kamar yadda wata majiya ta bayyanawa jarida.
Sai dai mabiya mazahabar Hanbali, sun doge kan cewa sai matar da ta shayar da su ta bayyana sannan a iya yanke hukunci. Kuma idan hukuncin ya tabbata, duk da cewa matar da mijin ba su da masaniya kan cewa mace daya ta shayar da su, to zai ci gaba da daukar dawainiyar ’ya’yan da aka samu a zaman da suka yi.
Mijin wannan mata da wannan al’amari ya auku a kansu, ya bukaci a kawo kwakkwararn
hujja, don bai kamata su ci gaba da zama are ba, kamar yadda majiya ta bayyana.
Ya ce: “Dole ne hukumar shari’a ta shigo ciki wajen raba auren, sannan mika hukuncin ga kotun daukaka kara, wadda za ta iya amincewa ko ta yi watsi da shaidar da aka gabatar.”
A watan da ya wuce ne, wata kotu a Al-Rass da ke Madina ta yanke hukuncin raba auren wasu, bayan da suka shafe shekara 25 suna tare. Su ma wadannan ma’auratan da aka raba aurensu, sun samu ’ya’ya bakwai.