Mabaracin da ke raba kudi a kullum ga Coci-coci da gidajen marayu

Wani tsoho mai shekara 99 a kasar Bulgeriya, yana yawon bara a kowace rana, amma da ya tara kudinsa, sai ya raba wa coci-coci da gidajen marayu. Dattijon mai suna Dobreb, masu wucewa a kan titi na yi masa ganin “bakon waliyi.Kafar sadarwa ta SaintDobry.com da Yahoo, a wani shafi da aka bayanin Dobreb, an […]

Mabaracin da ke raba kudi a kullum ga Coci-coci da gidajen marayu

Wani tsoho mai shekara 99 a kasar Bulgeriya, yana yawon bara a kowace rana, amma da ya tara kudinsa, sai ya raba wa coci-coci da gidajen marayu. Dattijon mai suna Dobreb, masu wucewa a kan titi na yi masa ganin “bakon waliyi.
Kafar sadarwa ta SaintDobry.com da Yahoo, a wani shafi da aka bayanin Dobreb, an gnao cewa, wani mutum ne da ya kumurce a zamanin yakin duniya na biyu. Kuma yana zaune ne a wajen garin Sofia, daga inda yakan yi tattaki a kasa, amma a halin yanzu yana hawan bas, inda yake shafe yini yana rokon mutane kudi, amma ba ya tarawa.
Wannan mutum mai bayar da kyautar sadakarsa, yana karbar fenshon yuro 80 (daidai da Dala 100), iyakar abin da yake ci ken an, amma duk abin da ya karba a hannun mutane sai ya raba su ga coci-coci da gidajen kula da marayu.
A bara, wani ma’abocin shafin sadarwar, Nullboid123, ya yi rubutu a shafin, inda ya bayyana cewa ya sha haduwa da Dobreb, inda ya bayyana masa cewa, “a da na taba aika mummunan abu,” a mma yanzu yana kokarin ya wanke kansa, ta hanyar taimakon al’umma.
Dobreb ya sha yin irin wadannan kyaututtuka, amma babbar kyautar da ya taba bayarwa, ta kimnanin kudin Bulgariya Leb dubu 35, wato daidai da Dala dubu 24, wadanda ya bai wa cocin St. Aledander Nebsky Cathedral, kamar yadda wani hoton bidiyon da cocin ya fitar, ya tabbatar da hakan.
Ya ce, yasan mutumin ya sha bai wa gidajen marayu taimakon kudi don biyan kudin wuta da ruwa.
“Wannan kyakkyawan aiki nagari. Komai nasa mai kyau ne,” a cewar Dobreb, a wani fim mai taken “kwaro ko kudin cizo – mite,” wanda aka yi a shekarar 2000. “Dole mu daina karya, ko aikata zina.  Lallai mu kaunaci junamu kamar yadda Ubangiji ke kaunar mu,” inji shi.