Mabarata na wasan ɓuya da hukuma a Abuja
Kamen ya haɗa har da ’yan bola-jari da mahaukata—Hukuma
Mabarata a yankin Birnin Tarayya Abuja sun samu kansu a cikin halin tsaka mai wuya, bayan cikar wa’adin da ma’aikatar kula da birnin, ƙarƙashin Ministan Abuja, Mista Nyesom Wike ta ba su na su guji ayyukansu a kan titunan yankin, tun daga ranar Litinin da ta gabata.
Cikar wa’adin ke da wuya, jami’an hukumar ƙarƙashin Hukumar Duba Gari da ta samu rakiyar jami’an tsaro ciki har da sojoji sun yi ta bin tituna a cikin ƙwaryar birnin da kuma kewayensa, inda suka yi ta kama masu bara, suna jefa su a cikin motocinsu na a-kori-kura.
Lamarin wanda aka bayyana a matsayin mafi zafi tun bayan wanda aka saba gani a lokacin tsohon ministan birnin, malam Nasir Ahmad Elrufa’i ya jagoranta, ya ta da hankalin mabaratan, inda suka fara ɓuya, a yayin da wasu daga cikinsu kuma suka koma yankunansu na asali, don gudun fadawa komar masu kamen.
A zantawarsa da Aminiya kan lamarin a shekaran jiya Laraba, Daraktan Hukumar Kula da Walwalar Jama’a ta Birnin Tarayya Abuja, wanda lamarin ke ƙarƙashin ofishinsa, malam Sani Amar ya ce, ya zuwa ƙarshen ranar Talata, an kama mabarata da ba za su gaza dari uku 300 ba, wanda a cewarsa sun ƙunshi masu barar da ’yan-bola da kuma mahaukata.
Aminiya ta ba da labarin cewa, matsalar tsaro da wasu yankunan Arewa ke fama da ita, ta sa masu bara na ƙara yawaita a Abuja, wadanda mafiya yawansu ba su da larurar naƙasar jiki a zahirance.
Wasu daga cikinsu na tsayawa wuraren ba da hannu da zaran yamma ta yi, inda suke zuwa wurin wadanda ke cikin motoci na alfarma, suna neman taimako.
Wasu kuma na yin dafifi ne a wuraren ibada har da majami’u, a yayin da wasu kuma ke zuwa kantunan alfarma suna yin dafifi a mashigar wuraren a lokutan da suka hada har da dare.
Aminiya ta zanta da wasu da ke fama da larurar naƙasa ta jiki da suka bayyana ɓacin ransu a kan lamarin tare da cewa, suna yin barar ne a dalilin rashin samun tallafi na yin sana’a da za su iya yi don kula da kansu da kuma iyalansu.
Sun yi ƙorafin cewa, sun shiga halin uƙuba da kuma damuwa a tsawon kwana biyu da dokar ta fara aiki dalilin rashin abin da za su ci bare wata buƙatar ta daban.
Aminu Sani na daya daga cikin masu larurar naƙasar da ke bara a garin Kubwa Abuja, daya daga cikin wurare da hukumar ta gudanar da aikin kamen.
Matashin wanda dan asalin yankin Gwarzo ne a Jihar Kano ya ce, lamarin ya ƙara jefa rayuwarsu a cikin halin wahala, inda ya zargi hukuma da rashin yi masu adalci.
Ya ce, “wannan barar da muke yi, larura ce ta samu yin ta, ba wai don muna jin dadinta ba. Idan za a taimaka mana da wani aikin yi, to ba wani dalili da zai sa mu ci gaba da yin ta.”
Ya ci gaba da cewa,“Allah ne Ya kiyaye da an wuce da mu, ba a jima ba da barin wurin nan sai ayarin masu kamen suka taho. Ba mu sake fita ba sai can ƙarshen yini, muka fito ala tilas don neman abin da za mu ci.
“Kamun da suke yi na wulaƙanci ne, za su kama mutum, su jefa shi a cikin mota ba tare da nuna halin tausayi ba. Sai a yau ne muka iya fitowa kamar yadda muka saba yi tun bayan fara kamen, sai dai fa cike muke da fargaba.”
Malam Aminu wanda ke matsayin wada a ɓangaren naƙasarsa da ta sa shi yin barar, ya ce, ’yan uwansa kamar uku da ke da larura irin tasa, sun wuce zuwa gida, gabanin ƙarewar wa’adin a ranar Litinin da ta gabata.
Abokin zamansa da ya rage a wajen mai suna Sabƙilu Muhammad wanda dan asalin Ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ce da ke fama da matsalar tsaro, ya ce ya bar gida ba dadi, “gashi nan din ma ba dadi.”
Ya ce, Allah ne ya tsare su da a yanzu suna cikin wadanda aka kama, saboda an kama takororinsu da dama.
An kama wasu ’yan’uwanmu da dama da ke zama ta unguwar phase 3 da Dutse da kuma inda ake aikin fasa dutse a unguwar da kan tintin Arab a nan Kubwa,” in ji shi.
Sai dai ya ce, sun fito a ranar a karo na farko kasancewar wadanda suka saba taimaka masu ba za su iya sanin inda suka maƙale ba, har sai idan sun fito.
Hukuma ba ta sanar da mu ba — Sarkin Guragun Abuja
A zantawarsa da Aminiya kan lamarin, Sarkin Guragun Abuja, Alhaji Muhammad Sulaiman Katsina ya bayyana mamakinsa kan yadda hukuma ta gaza sanar da su lamarin a hukumance, da nufin tattaunawa da su. Sai dai kawai suka ji shi ta kafofin yada labarai.
Ya ce, duk da ƙoƙarin da fadarsa ke yi wajen zaburar da mambobinsu kan su rungumi sana’a a maimakon bara, zai fi kyau idan akwai shiri irin wannan a sanar da su don ƙara wayar wa jama’a kai.
Alhaji Muhammad Sulaiman Katsina ya zargi yawancin masu bara a Abuja masu lafiya ne da ba su da alamar wata larurar naƙasa ta jiki.
“Wasu daga cikinsu dattawa ne, wasu kuma matasa masu ƙarfi a jika, amma sai su riƙa tsayawa a gefen titi, suna gudu ta inda duk mota ta tsaya suna yin bara,” in ji shi.
Sannan ya zarge su a matsayin masu yi masu kutse a lamarin. Sai dai ya ce, mafiya yawan mabarata da ke garin Karmaji inda fadar tasa take da ke matsayin unguwa da Hukumar Kula da Birnin Abuja ta ware don masu larurar naƙasa, yawancinsu ’yan kasuwa ne, kamar yadda ya bayyana.
Suna ɓata tarbiyyar yara tare da takura wa al’umma — Hukumar Abuja
Daraktan Hukumar Kula da Walwalar Jama’a na Yankin Birnin Tarayya Abuja, malam Sani Amar ya zargi masu harkar bara a birnin da ke tafiya da ’yan jagora a matsayin masu ɓata tarbiyyan yara. Sannan masu ƙarfi a jika da mutuwar zuciya da takura wa sauran jama’ar birnin.
Ya ce, wasu daga cikinsu ba su da tarbiyya bare masu taimaka wa yaran da ke hannunsu da tarbiyar, a yayin da wasu kuma suke dauko su daga jihohin Arewa, suna ba da hayar su ga masu buƙatar jagoranci ko ayyukan gida.
Ya ce, a ranar Litinin da aka fara aikin, an kama mabarata kamar 61 sai kuma ’yan-bola 103.
Ya ce, aikin ya ci gaba a ranar Talata, inda aka kama mabarata 33, sai kuma mahaukata 34.
Ya zargi masu sana’ar bola da laifin yi wa mutane ƙwace a mota da kuma sace-sace a gidajensu. A yayin da wasu da ke matsayin mahaukata a zahiri.
Ya ce, daukacin wadanda aka kama za a tantance su a Filin Taro na Dandalin Fareti na Abuja.
Wasu daga cikinsu da suka zo daga ƙasashen ƙetare irin Jamhuriyar Nijar za a mayar da su ƙasashensu.
Wasu kuma ’yan ƙasa ne za a nemi sanin sana’ar da za su iya kuma suke sha’awa don taimaka masu tsayawa da ƙafafunsu.
Sai dai da Aminiya ta ankarar da shi halin da Cibiyar Horar da Naƙasassu da ke Bwari Abuja take ciki, sai babban jami’in ya ce ministan birnin na da aniyar sake inganta wajen.