Mabarnata sun tona rami a titin saukar jirgin sama

Zauna-gari-banza sun tona rami a kan titin saukar jirage da ya hana zirga-zirga a filin jirgin saman Jihar Ondo. Wakilin Aminiya ya ziyarci filin jirgin inda ya lura an tona ramin ne a karshen makon jiya. Irin barnar da ’yan daban #EndSARS suka yi a Ondo Jirgin farko zai sauka a filin jirgin Inugu Ya […]

Mabarnata sun tona rami a titin saukar jirgin sama

Zauna-gari-banza sun tona rami a kan titin saukar jirage da ya hana zirga-zirga a filin jirgin saman Jihar Ondo.

Wakilin Aminiya ya ziyarci filin jirgin inda ya lura an tona ramin ne a karshen makon jiya.

Ya yi kokarin jin ta bakin Manajar Filin Jirgin, Joke Olatunji, amma ta ce ba ta da izinin yin magana da ’yan jarida.

Kakakin Hukumar Filayen Jirgin Sama ta Kasa (FAAN), Henrietta Yakubu, ta ce sun lura da ramin ne a lokacin da suke zagayen yau da kullum a ranar Litinin kuma ramin bai hana sauka da tashin jirgi ba.

Sai dai wakilinmu ya ce babu alamun hada-hada a filin jirgin wanda yake hasashen na da nasaba da tashin hankalin da zanga-zangar #EndSARS ta haifar.

Za a yi jana’izar jagoran addinin Iran Ali Khamenei a watan Yuli

Fiye da ƙungiyoyi 60 sun yi zanga-zanga kan taron G7 a Faransa

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba