Mabiya addinin gargajiya sun nemi a riƙa rantsuwa da gumakansu

Hakan zai dawo da tattalin arzikin ƙasa da kuma shawo kan matsalolin da suka addabi ƙasar.

Mabiya addinin gargajiya sun nemi a riƙa rantsuwa da gumakansu

Kungiyar Mabiya Addinin Gargajiya ta Ƙasa da Ƙasa (ICIR) ta buƙaci sarakunan Yarbawa su koma wa abubuwan bauta na gargajiyar ƙabilar da kuma yin amfani da ‘Isese’ na gargajiyarsu na gado kaka da kakanni.

Haka kuma ma’aikata da sauran  masu riƙe da muƙamai su koma ga ɗaukar rantsuwar kama aiki da abubuwan bauta na addininsu na  gargajiya domin samun daidaito.

Shugaban Ƙungiyar a Nijeriya da Ƙasashen Duniya, Dokta Fayemi Fatunde Fakayode ne ya faɗi haka a jawabinsa a wajen bikin Ranar Addinan Gargajiya ta shekarar 2024 da 2025 da aka gudanar a babban ɗakin ibada a Oke-Itase a garin Ile-Ife a Jihar Osun.

Ya ce baya ga dogaro da samun daidaiton yin amfani da addinan nasu wajen aiwatar da abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan adam, zai sa a ga sauyin al’amura musamman martabar Sarakunansu kuma hakan zai dawo da tattalin arzikin ƙasa da kuma shawo kan matsalolin da suka dabaibaye ta baki ɗaya.

Shugaban ya jinjina wa gwamnatocin jihohin Legas da Ogun da Osun da Oyo a kan amincewarsu da keɓe ranar 20 ga watan Agusta na kowace shekara a matsayin ranar hutu domin girmama addinan gargajiya.

Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi ne ya jagoranci wasu sarakuna da shugabannin ƙungiyoyin mabiya addinan gargajiya zuwa wajen bikin na bana.

An kuma baje-kolin kayan al’adun gargajiya da mabiyan suke amfani da su wajen gudanar da ibadarsu, kayayyakin da aka baje sun haɗa da suturu da murjanai da warwaro da jigida da wuri da gumaka da layu da makamantan su.