Mabiya Zakzaky barazana ne ga zaman lafiya – Farfesa Mahdi

Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mahdi ya ce kungiyar Shi’a ta Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky wata babbar barazana ne ga zaman lafiya da tsaron Najeriya.Kuma ya bayyana kasar Iran wadda yake zargi da mai daure wa Shi’anci gindi a matsayin “Babbar abokiyar gabar Najeriya.”Farfesa Mahdi ya […]

Mabiya Zakzaky barazana ne ga zaman lafiya – Farfesa Mahdi
Mabiya Zakzaky barazana ne ga zaman lafiya – Farfesa Mahdi

g Gwamna Nasir El-Rufa’i na Jihar KadunaTsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mahdi ya ce kungiyar Shi’a ta Harkar Musulunci (IMN) ta mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky wata babbar barazana ne ga zaman lafiya da tsaron Najeriya.
Kuma ya bayyana kasar Iran wadda yake zargi da mai daure wa Shi’anci gindi a matsayin “Babbar abokiyar gabar Najeriya.”
Farfesa Mahdi ya bayyana haka ne lokacin da yake bayar da shaida a gaban Hukumar Binciken Rikicin Sojoji da ’ya’yan kungiyar IMN ta ’yan Shi’a mabiya Zakzaky a Zariya a ranakun 12 zuwa 14 ga Disamban bara, inda ya ce kungiyar tana gudanar da harkokinta a matsayin wata kasa a cikin kasa.
Farfesa Mahdi ya kawo tarihin kafuwar kungiyar ta Shi’a kan gabatar da ita da wani malami dan kasar Pakistan mai suna Islamul-Hak wanda ya koyar a sashin tattalin arziki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarun 1970 zuwa 1980.
“A gaskiya ya yi kokarin ya sanya ni a Shi’a, amma na ki. Sai ya samu nasarar sanya Ibrahim Zakzaky wanda dalibi ne a sashin tattalin arziki. Gidan Islamul-Hak ya zamo wata cibiya ta dauka da shigar da mutane Shi’a,” inji shi.
Ya ce a 1979 ne mutanen Zariya suka wayi gari wata rana suka rika ganin an bi kan allunan talla da gine-ginen gwamnati da na jama’a da kan kwalta an rurrubuta taken “Musulunci kawai.”
Farfesa Mahdi ya ce daga abin da ya gani da kuma bayanan da ya samu, tashe-tashen hankula sun fi ayyukan zaman lafiya a cikin harkokin Shi’a a garuruwan Zariya da Sakkwato da Gombe da sauransu.
Ya ce kungiyar tana da tsari kuma tana gudana ne kamar wata gwamnati a cikin gwamnati.
Game da yadda kungiyar ta Shi’a ke gudanar da ayyukanta, Farfesa Mahdi ya ce “Galibi suna gudanr da ayyukansu ne boye cikin sirri, boyayyun wuraren sun watsu a sassan kasar nan musamman a Arewa. Kuma akwai wani babban kwamiti da yake zama a kai – a kai a karkashin jagorancin Zakzaky, sannan a matakan jihohi kowace jiha tana da gwamna da sakatariyarta. A matakin kasa da jihohi suna da kwamitoci kamar na ilimi da na kudi da na daukar ma’aikata da na samar da kayayyaki.”
Ita ma kungiyar Raya Masarautar Zazzau (Zazzau Emirate Debelopment Association – ZEDA ta zargi magoya bayan kungiyar IMN ta Sheikh Ibrahim Zakzaky da gallaza wa mutanen Zariya. kungiyar ZEDA ta ce kungiyar ta ’yan Shi’a ta rika fitinar al’ummar masarautar a tsawon shekaru.
Mai magana da yawun kungiyar ZEDA, Muhammad Balarabe wanda ya bayyana a gaban Hukumar Binciken Rikicin Sojoji da ’yan Shi’a na Zariya da ke zama a Kaduna, ya ce, kungiyar tana daukar doka a hannunta tare da rufe hanyoyi a lokacin da suke gudanar da jerurrukan gwano a birnin.
Balarabe ya ce duk lokacin da kungiyar ta Shi’a ta fito, takan tilasta su (mutanen Zariya) zama kamar matan kulle.
Ya ce rikicin 12 ga Disamba a tsakanin ’ya’yan kungiyar Shi’a ta IMN da sojoji ba shi ne karo na farko ba, inda ya ce kungiyar ta sanu wajen tashin hankali.
Kakakin na ZEDA ya kawo misali kan yadda ’ya’yan kungiyar suka tozarta Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Ramalan Yero. Kuma ya ce kungiyar ta sha yin rigima da gwamnatocin da suka gabata.
Ya ce jagoran ’yan Shi’ar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da magoya bayansa ba ’ya’yan kungiyar ZEDA ba ne, inda ya ce sun ki yin rajista da kungiyar.
Ya ce: “Muna sane da aikace-aikacen kungiyar a shekara 20 da kafuwarta. Kuma a matsayina na wanda ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, mun san inda daki yake yoyo. Duk lokacin da suka fito, sai dai mu zauna ko mu sake hanyoyi, domin kauce wa yin fito-na-fito, suna jawo wahalhalu kuma suna rufe hanyoyi.”