Mabudan Sha’awar Uwargida 10

Assalamu Alaikum makarantanmu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, za mu ci gaba da bayani kan mataki na biyu da maigida zai hau don bude sha’awar uwargidansa, wato koyi Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarshi kuma ya amfanar da su, […]

Mabudan Sha’awar Uwargida 10

Assalamu Alaikum makarantanmu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, za mu ci gaba da bayani kan mataki na biyu da maigida zai hau don bude sha’awar uwargidansa, wato koyi Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarshi kuma ya amfanar da su, amin:

Sunnoni Maigidantaka:

1. Iya bayyana Soyayya

Annabinmu Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya kasance baya shakka ko kunya wajen bayyana soyayyarsa ga matansa RA, kuma ba garesu kadai ba, har ga jama’ar da ke tare da shi (RA). Amr bin Al-As RA, ya tambayi Annabi SAW cewar ‘Wa Ya fi so a duniya duka?’ Annabi SAW Ya bashi amsa da cewa ‘Aisha’ Radhiyallahu Anha, ya sake tambayar shi: ‘Cikin Maza fa?’ sai Ya ce ‘Babanta.’ Mu lura da cewar: ‘Babanta’ Maimakon Ya ce: ‘Abubakar Saddik (RA),’ domin hakan wani salon kaurara kauna ce gareta Radhiyallahu Anha. 

*Ummuna Aisha RA ta ba mu labarin cewa wata rana ta taba tambayar Annabi SAW ya karfin sonta ya ke a cikin zuciyarsa? Sai ya ce da ita kamar kullin da aka yi ne da igiya mai tsananin kauri; (domin zai yi wuya ya kwance, kila ma ba zai kwantu ba sai dai a yanke shi, yankan ma sai da wuka mai tsananin kaifi). Kuma lokaci-lokaci ta kan tambaye shi ‘ya kullin nan yake dai?’ Sai Ya amsa mata da cewa ‘ya na nan da karfinsa.’

*Kuma wata rana ta ce da shi SAW: ‘Ya Manzon Allah! Yanzu ace ka sauka a wani gandu, ga ciyawar da wasu dabbobin sun yi kiwo a kanta, ga kuma wata sabuwa wacce ba ayi kiwo a kanta ba, daga cikinsu a ina za ka bar rakuminka ya yi kiwo?’ Sai ya bata amsa da cewa: ‘Zan kai shi ga ciyawar da ba a yi kiwo a kanta ba!’ A nan Uwar Muminai RA na son ta tabbatar da tafi sauran matan daraja a wajen shi SAW, domin ita kadai ce ya aura tana budurwa.

Mu lura yadda Annabinmu SAW bai yi shiru ya share ta ba; sannan kuma ya bata gamsashshiyar amsa wacce za ta kwantar mata da hankali, domin shi Sallallahu Alaihi Wasallam ya san yanayin halayyar ‘ya mace, komin yadda ta tabbatar da irin so da kulawar da mijinta yake mata, lokaci-lokaci ta kan yi kokwanto, sai ta ga kamar ko ya daina sonta? ko son ya ragu ba kamar da ba? Jibi dai yadda Ummuna Aisha ke kara tamabaya: ‘Ya kullin nan yake dai?’ Mace ta tabbatar da cewa mijinta yana tsananin sonta da ji da ita, yana taimakawa ga wanzuwar nishadi da wadatar zuci cikin zuciyarta, wadanda sinadaran bude sha’awar ‘ya mace ne kamar yadda bayani ya gabata. 

Don haka yana da matukar alfanu ga magidanta su fahimci cewa bayyana soyayya ga uwargida ba rauni bane, domin da rauni ne da Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallam bai yi ba, kuma koda mutum yana da mata fiye da daya, ba laifi ko wacce ya rika bayyana mata so da matsayinta a zuciyarsa lokacin da suka kebanta; ba laifi in ma ya dan kara gishiri da magi wajen yin haka din in dai wannan zai kwantar mata da hankali ya kwararo da nishadi cikin zuciyarta. Don haka bayyana soyayya wata sunna ce mai kyau kuma mai dadi wacce ta cancanci a rayar da ita cikin rayuwar aure; bayyana soayayya abin burgewa ne kuma abun bajinta ne; duk namijin da ya iya bayyana soyayyarshi ga iyalinshi, kuma bai shakkun yin hakan, to ya cancanci a kira shi da: Jarumi!

2. Nuna so da kulawa: Salo-salo!:

In muka yi zurfin nazari kan irin salo-salon da Annabinmu Sallallahu Alaihi Wasallam ya rika nuna kauna da kulawa ga matansa Radhiyallahu Anhunna, za mu gane cewa duk duniya ba wani kwararren masoyi kamarsa Sallallahu Alaihi Wasallam. Jibi yadda yake yawan sumbatarsu; ya yi wanka tare da su; ya sha abin sha da modan da suka sha, har ma sai ya daidaici inda suka sa bakinsu sannan ya sa na shi bakin (mai albarka) a dai-dai wajen ya sha; ya kanyi wasa da dariya tare da su; Ya taimaka masu da ayyukan gida; ‘yan hidimominsa na cikin gida da kan shi ya kan yi abin shi bai cewa dole sai sun yi mashi; ya kan tara su su duka ayi hira gaba daya, a gidan wacce ke da aiki ranar.

Sai mako na gaba sauran bayani na zuwa in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.