Mabudan Sha’awar Uwargida (2)
Assalamu Alaikum makarantar mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin: Makunnin Sha’awar ’Ya mace: Matakin farko da Uwargida za ta bi don budo sha’awarta shi ne, ta fara yin zurfaffen tunani game da ita kanta, yanayinta da […]
Assalamu Alaikum makarantar mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin:
Makunnin Sha’awar ’Ya mace:
Matakin farko da Uwargida za ta bi don budo sha’awarta shi ne, ta fara yin zurfaffen tunani game da ita kanta, yanayinta da yanayin halayenta da yanayin shau’ukan cikin zuciyarta. Ta yi kokari ta fahimci mene ne yake danne mata sha’awar ta? In da hali ta samu littafi ta rubuta dukkanin dalilin da take ganin su ne ka iya rufe mata makunnin sha’awar ta, da kuma abin da take ganin zai kawar da su har sha’awarta ta bude. Na sha fada a cikin wannan fili cewa, ita ’ya mace dole sai tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali da natsuwa daidai gwargwado sun saukar mata a zuciya kafin makunnin sha’awarta ya iya kunnuwa sannan ne sha’awarta za ta budo gaba daya. Wasu halaye na nagarta kuma abin so na iya zama cutarwa ga sha’awa, misali: mace mai tsananin hakuri da kawar da kai, za a yi ta yi mata abubuwa na cin zarafi amma ta yi ta hakuri tana shanyewa, to wannan shanyewar kala biyu ce, akwai wacce in ta shanye ta shanye ke nan har ga Allah ba za ta kara tunawa da abin ba sai in ta yi dalili, akwai wacce ko za ta kyale ne kawai don ba ta son tashin hankali, don jin kai, don tsoro ko don rashin wayau, amma abin yana nan a ranta tana kullace da shi, to irin wannan ’yan kulle-kullen in aka bar su sai su nauyayya a zuciya da ruhi, nauyin da zai danne makunnin sha’awa ta yadda ko ya aka so a kunno ta ba za ta kunnu ba.
Don haka makunnin farko shi ne kwance duk wani kulli da ke cikin zuciya; goge duk wata tsatsa; hakuri da shanye abubuwa nan da nan kuma shanyewa ta gaba daya, rayar da kyawawan shau’uka da tunani cikin zuciya da yin fatali da duk wani bakin shauki mai nauyaya da sa kunci ga zuciya. Domin dai duk halin da zuciya ke ciki, shi kwakwalwa za ta shaka don tantance irin aikin da ya kamata ta zartar. A takaice dai dole sai uwargida ta koyi kasancewa cikin jin dadi da kanta, jin dadin mutanen da take tare da su da jin dadin wurin da take don wannan ne zai haifar da irin natsuwar da zai bankado da sha’awarta waje. Wannan ne ya sa wasu ke ganin masifaffun mata na da sha’awa saboda ko me aka yi masu, nan take za su mayar da martani ba su bar shi a zuciyarsu har ya nauyayar masu da makunnin sha’awarsu ba.
Makunnin na 2 : Cire Kunya
In uwargida na jin kunyar miji ko kunyar yin ibadar aure da shi, musamman in kunyar ta yi tsanani, to wannan na iya nauyayar da makunnin sha’awarta, domin ita kwakwalwa na fassara duk wani abu da ake jin kunyar sa, da abu mara kyau wanda ra’ayinta bai kamata ya yi ba, to don haka sai makunnin sha’awar mace mai tsananin jin kunya ya ki kunnuwa, don haka sai a dage a cire kunya ta fannin ibadar aure, na san kunya ba ta ciruwa rana daya, amma in aka daura niyya, a hankali, wata rana sai a yi mamakin wai an ji irin wannan kunyar.
Jan aji, ko jan wahala?
Assalamu Alaikum don Allah ina so a wayar da mata game da jan aji wurin ibadar aure wai in mace ba ta jan aji darajarta za ta ragu ga maigidanta wanda ina ganin wannan shi ma kan taimaka wajen rufe sha’awar uwargida.
-Wani Bawan Allah.
kwarai kuwa ka yi gaskiya, Allah Ya saka da alheri a kan wannan kyakykyawan nazari da ka yi. Jan aji wajen ibadar aure bai da wani amfani ko miskala zarratin, domin mace na tare da halartaccen mijinta, a kan shimfidar aure, to ai ba maganar jan aji sai dai maganar lokacin nuna kauna. Da yawa matan Hausawa na da wannan akidar ta cewa nuna ma miji ba a damu da shi ba shi zai sa mace ta fi yin kima a wajensa, sai ya kasance wasu matan komai tsananin sha’awar da suke ji ba su bari mazansu su sani, akwai wadanda suke danne sha’awarsu da karfin tsiya lokacin ibadar aure don dai kar mazansu su gane cewa ga halin da suke ciki, wai in sun gane zai zama silar wulakanci da muzgunawa daga su mazan. Kodayake in bera na da sata, to daddawa ma na da wari! domin akwai maza masu zolayar matansu kararan game da abin da suka aikata cikin magagin ibadar aure a sirrance, in wata bai damunta, wata abin zai dameta don haka sai ta yi duk yadda za ta yi don kar sha’awarta ta bayyana.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba InshaAllah, sauran bayanin na zuwa, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe amin.