Mabudan Sha’awar Uwargida (3)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani daga inda muka kwana makon jiya…   Ga Uwargida mai jan aji wajen ibadar aure ta sani, wannan kauyanci ne cikin […]

Mabudan Sha’awar Uwargida (3)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani daga inda muka kwana makon jiya…

 

Ga Uwargida mai jan aji wajen ibadar aure ta sani, wannan kauyanci ne cikin rayuwar aure, shimfidar aure ba wajen jan aje ba ne, waje ne na cakuduwar so da kauna da jiyar da juna dadi da kyautatawa ga juna. Jan aji kam yana da nasa wuri cikin rayuwar aure, amma ana yin sa ne a sigar wasa da soyayya kuma na wani dan gajeren lokaci.  Maigida ya san jan shi ne kawai ake yi ba wai aji ake ja masa ba. Ba a yin sa da gasken gaske, a rika nuna maigida da shi da babu duk daya, ko da ya yi da ya bari duk daya, yin irin haka wani salon cutarwa ne da kuntatawa ga maigida, kuma duk matar da ke cutar da mjinta, to tafi cutar da kanta fiye da shi illa dai ganewa ne da ba ta yi ba. 

Da yawa wasu mazajen na matukar son gwada bajinta ga matayensu, amma wasu matayen ba su son bayar da hadin kai ga maigida, ba su nuna wa mazansu ko da wata karamar alama ne, abin da ya yi masu da wanda bai yi masu ba, ko sun ji wani abu sai su danne don kar a ga raunin su, to in maigaida bai ga raunin ki ba- musamman ta wannan fannin- to waye zai gani? Mazaje da dama na aiko da tambayoyi kan ya ake gane gamsuwar sha’awar ’ya mace?  Suna fadin ko sun tambayi matan nasu ba su gaya masu, saboda da jan aji (ko kunya), to kuma wannan wani abu ne da bai da amsa daya, don kowace mace da irin yanayinta.

’Yan’uwana mu sani, nuna wa miji jin sha’awa, da bayyana masa gamsuwa ba laifi ba ne kuma ba haramun ba ne, to me ya sa  za ki haramta wa kan ki abin da Allah SWT Ya halatta miki? Kuma a dalilin haka ya kasance kin cutar da kan ki da maigidan ki? Mu sani, duk wani shauki na cikin zuciya da aka danne ko aka boye, to a hankali zai mutu, don haka duk mai danne sha’awarta wata ran za ta wayi gari ta neme ta ta rasa, da fatan Allah Ya ba mu ikon yin abin da yake shi ne daidai kuma mai alafanu kodayaushe cikin rayuwar mu, amin.

Ga matar da ke danne sha’awarta saboda zolaya ko yanayin maganganun mijin auren ta game da abin, sai ta samu hanya mafi dacewa ta sanar da shi gaskiya ba ta son hakan, ta gaya masa yana cutar da ita da irin wadannan kalaman, ta roke shi ya daina don kyautatuwar zamantakewa a tsakaninsu. in ma ta ji ba ta iyawa gaba da gaba, to ki rubuta masa wasika a takarda ki ba shi ko ki aika masa sakon tes, da fatan Allah Ya sadar da mu yin riko da kyakykyawan zance a koda yaushe, amin.

 

Hanyoyin Tafiyar Da Kunyar Ibadar Aure:

Tsananin kunya na daya daga cikin manyan abubuwan da ke rufe sha’awar da yawa daga cikin matan aure. Ga uwargidar da ke fama da rufewar sha’awa a dalilin tsananin kunyar ibadar aure, sai ta bi bayanin da zai biyo baya don ganin ta tafiyar da kunyar ko kuma ta sarrafa ta zuwa wani shauki mafi alfanu gare ta da maigidanta.

Da farko dai sai uwargida ta fara da gano shin mene ne ke haifar mata da wannan jin kunyar, shin shi mijin nata take jin kunya, to me ya sa? Ko aikin ibadar auren ko kuwa irin shau’ukan da take ji ne lokacin ibadar auren ke sa mata jin kunyar, ko kuma wani irin jin kai ne ke sa mata jin kunyar? In ta fahimci abin da ke haifar mata da jin kunyar sai ta yi kokarin ture abin nan ta hanyar tabbatar wa kanta cewa wannan jin kunyar ba ta da muhimmanci a gareta, bai amfanar da ita da komai ta fannin ibadar aure, sannan kuma ya hana mata faruwar wasu abubuwa mafi mahimmanci ga farin cikin rayuwar aurenta, su ne buduwar sha’awar ta da samun gamsuwar ta da karuwar faranta ran maigidanta.

 

Zan dakata a nan, sai mako na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.