Mabudan Sha’awar Uwargida (5)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani daga inda muka kwana makon jiya; bayani ya tsaya ne a kan hanyoyin da uwargida za ta bi don tafiyar da tsananin kunya lokacin […]

Mabudan Sha’awar Uwargida (5)

Assalamu Alaikum makarantan mu, barkan mu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani daga inda muka kwana makon jiya; bayani ya tsaya ne a kan hanyoyin da uwargida za ta bi don tafiyar da tsananin kunya lokacin ibadar aure, don buduwar sha’awarta. A yau za mu duba wasu abubuwa da suka danganci lafiya da yanayin jiki, wadanda su ma na iya danne makunnin sha’awar uwargida:

 

1. Jin Zafin Ibadar aure: In ya kasance uwargida na jin zafi lokacin ibadar aure, musamman in zafin mai tsanani ne, to fargaba da tsoron wannan zafin zai dakusar mata da sha’awarta har ya kasance ta daina jin motsuwar ma gaba daya, balle har ta iya kai wa ga biyan bukatar sha’awar ta. Abubuwan da ke haifar da jin zafi lokacin ibadar aure sun hada da:

1. Rashin isashshiyar lema a ’yammatanci: In ya kasance babu isashshiyar lema a ’yammatanci, to ibadar aure zai rika zafi da wahalarwa ga uwargida, shi wannan ruwa da yake fesowa lokacin gabatarwar ibadar aure amfanin sa kamar amfanin man grease ne a inji. Wasu cututtuka na jiki, kamar su bushewar jiki, rashin isashshiyar lema a jiki duka, wani ciwo ne da ya shafi kwada ko mahaifa, da gabatowar tsufa duk suna iya sa rashin isashshiyar lema a ’yammatanci. Sannan rashin cin lafiyayyen abinci musamman ’ya’yan itace da kayan lambu na iya haifar da karancin lema. Sannan tsoron jin zafin ma kan shi ko kin da uwargida ke wa ibadar aure na iya hana sarrafuwar ruwan da ke sa  wajen lema.

Hanyar kawar da wadannan shi ne uwargida ta dage wajen cin kayan lambu da ’ya’yan itace, ta kuma rika yawan shan ruwa, sannan ta cire duk wani tsoro ko fargabar jin zafi daga zuciyarta. In kuma da wani ciwo mai dangane da wajen sai a yi kokarin warkar da shi tukunna. Uwargida na iya amfani da man shafawa na basilin lokacin ibadar aure har kafin wannan matsalar ta kau daga gare ta insha Allah.

2. Tsukewar ’yammatanci: Wannan yanayi shi ma na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida, in an fahimci hakan ne ke haifar da matsala to sai a je a ga Likita, akwai ’yar karamar tiyatar da za a iya yi don tafiyar da matsalar.

3. Salewar Mafitsara: Saboda kusancin mafitsara da kofar ’yammatanci, salewar wajen fitar fitsari, ko ya kumbura yana zafi, na iya haifar da jin zafin ibadar aure ga uwargida, dadin abin akwai magunguna da za su warkar da wannan nan da nan in an ziyarci likita.

4. Bankarewar jijiyoyin kofar ’yammatanci: Wannan bankarewar jijyoyi lokacin ibadar aure na haifar da tsananin zafi marar misaltuwa ga Uwargida wanda dole ta ji kwata-kwata ba ta kaunar ibadar auren, sannan ga shi ba wai wata kwayar cuta ke haifar da wannan ba illa dai irin tunanin da ya yi karfi a zuciyar ta game da ibadar auren, musamman in akwai wani abu da take tsananin ki a ciki, kuma kin ya yi karfi har zai sa jijiyoyin yammatancinta, maimakon su yi lum-lum su kwanta yadda har za ta iya jin sha’awa, sai su bankare su haifar da tsananin zafi gareta da rashin samun isashshiyar gamsuwa ga maigidanta. Hanyar magance irin wannan matsalar shi ne uwargida ta daure ta kawar da duk wata kyama, wani tsoro da duk wani karkataccen tunani da ta rike a zuciyarta da ma’aikatar hankalinta game da ibadar aure, game da mijinta ko game da yanayin dangantakar da ke tsakaninsu. sannan ta daure ta rika sakin jikinta lokacin ibadar aure; ta natsu ta kwantar da hankalinta kan ibadar auren yau da gobe in Allah Ya yarda za ta ga ta yi nasara, ta daina jin irin wannan zafin. Babban maganin wannan matsalar shi ne a dage a rika motsa wadannan jijiyoyi da suke bankarewa da samfurin motsa su na kegel, sai a nemi ‘yar karamar na’urar kegel-master a rika yi a kai-a kai. Da fatan Allah Ya sa a dace, amin.

5. Kumburi da salewar kwada ma na sa jin zafin ibadar aure ga uwargida, kuma da an warkar da wannan ciwo insha Allahu za a daina jin zafin.

6.  Fitowar yadin shimfidar mahaifa: Wannan shi ma na haifar da jin zafin ibadar aure, kuma da an magance ta a asibiti jin zafin shi ma zai tafi insha Allah.

Sai sati na gaba sauran bayanin na zuwa Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.