Mabudan Sha’awar Uwargida (7)
Matukan Sha’awar Uwargida, ci gaba daga makon jiya: 1. Jin Dadin Zuciya: To maigidan da yake son ya ji matarsa ta himmatu cikin ibadar aurensu, to zai fara kamfen ne tun da safe, ko ma tun jiya, da maganganu masu dadi irin wadanda ya san tana son ji, da kalamai masu jika zuciya, kulawa da […]
Matukan Sha’awar Uwargida, ci gaba daga makon jiya:
1. Jin Dadin Zuciya: To maigidan da yake son ya ji matarsa ta himmatu cikin ibadar aurensu, to zai fara kamfen ne tun da safe, ko ma tun jiya, da maganganu masu dadi irin wadanda ya san tana son ji, da kalamai masu jika zuciya, kulawa da kyautatawa da yabo, a kula sosai da yawan yaba wa mace, domin yana da tsananin tasiri ga jin dadin zuciyarta wanda shi ne babban matukin sha’awarta.
Saboda tsananin alfanun tabbatuwar kyakykyawar zamantakewa tsakanin ma’aurata, shari’a ta amince wa miji ya yi ‘yar karamar karya don dadada ran matarsa; don haka ku riki dabi’ ar yawan yaba wa matanku, da koda su ko da da abin da kuka san ba hakan ba ne a zahiri. Misali, kamar ka ce da ita: “Kai, ai da kika yi murmushin nan sai na ga har hasken rana ya dishe don tsananin hasken murmushinki!” Wannan dole ya sa ta ji dadi ya kwaranya a zuciyar har ta kara yi maka wani murumushin.
To irin wannan jin dadin shi ake so kodayaushe maigida ya rika nomawa tsakaninsa da iyalansa. Wannan sinadarin ne mayaudaran maza ke amfani da su wajen bata yaran mutane, da sun haifar da jin dadin zuciya da kalamansu da kyautukansu da kulawarsu, sai ka ga yarinya tagari ta zubar da mutuncinta, da fatan Allah Ya tsare dukkan Musulmi daga mummunan aiki, amin.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa: ‘Mafi alkhairin cikinku, su ne mafiya kyautatawa ga iyalansu.’ Domin wani abu ne na jarumtaka, saboda yanayin halin da namiji, irin abubuwan da ‘ya mace ke so, wadanda ta dauka da mahimmanci, shi ba su ne a gabansa ba, kuma ba su ya ba mahimmanci ba. ‘Ya mace ba ta gajiya da jin kalamai masu dadi daga wajen mijinta, kuma ba ta ki kullum ya furta mata kalmar so akalla sau uku a rana ba, in ba irin wadannan sai ta yi ta kokwanton son da yake mata, duk kuwa ga wasu abubuwan nuna kaunar yana yi mata a kai-a kai, amma da yake ita ba su ta ba mahimmanci ba, sai ka ga ‘yan kananan abubuwan da maigida bai kulawa da yi, don a ganinsa ba su da muhimmanci sun rufe sha’awar uwargida.
Yadda za a fahimci hakan shi ne, namiji ko yana jin haushin matarsa, wannan bai hana ya yi sha’awarta ba, musamman in ya ganta cikin yanayi mai jan hankali, amma ita mace, in tana jin haushin mijinta, to wata ko son ganin sa ma ba ta yi balle har ta yi sha’awarsa!
2. Wasannin Ibadar Aure: Akwai matan da suka aiko sakonninsu ga wannan fili suna ganin kamar ba su da sha’awa ne, domin mazansu na aiwatar da wasannin kafin gabatarwa gare su amma duk da haka ba su jin motsuwar sha’awa, kamar yadda wasu mazan ke korafin suna gabatar da wasanni ga matansu amma ba su ganin wani canji; to hakan na faruwa ne in ya kasance maigida bai san abin da ya fi kayatar da uwargida ba game da irin wadannan wasannin, domin kowace mace irin abin da take so daban, kuma abu ne da yake canzawa; abin da ta ji yau, gobe kuma sai ka tarar ba shi ba ne, wani abin ne daban, yawancin magidanta irin wasannin da suke wa matansu, su matan ba shi suke so ba, kuma wannan bai sa su ji komai ta fannin habakuwar sha’awarsu, wata sa’in sai ma ya haifar da rashin jin dadi ga uwargida, ta kagara a yi a gama ko ta huta. Maganin wannan shi ne maigida ya san dabarar da zai yi, ya san hanyar da zai bi har ta bayyana masa irin abubwan da take so, kuma ya rika lura, in sun canza, sai ya kara tambayar ta.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah sauran bayani na zuwa, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.