Mabudan Sha’awar Uwargida (8)

Matukar sha’awar uwargida, ci gaba daga makon jiya… 3. Natsuwa: Maigida, da ya ji motsuwar sha’awa, to samun biyan bukatar nan ita ce a gabansa, kuma bai tunanin komai a lokacin sai hakan, kuma abu kadan, musamman duk abun da zai ja hankalinsa na daga matarsa, na iya motso mai da sha’awarsa nan take; amma […]

Mabudan Sha’awar Uwargida (8)

Matukar sha’awar uwargida, ci gaba daga makon jiya…

3. Natsuwa: Maigida, da ya ji motsuwar sha’awa, to samun biyan bukatar nan ita ce a gabansa, kuma bai tunanin komai a lokacin sai hakan, kuma abu kadan, musamman duk abun da zai ja hankalinsa na daga matarsa, na iya motso mai da sha’awarsa nan take; amma ita uwargida, ko da sha’awarta ta motso har ma ta yi nisa, to motsi kadan, wata ‘yar magana kadan, kai koda wani tunani ta yi daban a cikin zuciyarta wanda bai danganci ibadar aure ba, to nan da nan kuma sha’awarta na iya sulalewa, ta yi sanyi.

Sannan kuma yana iya kasancewa uwargida tana cikin natsuwar zuciya, ga shau’uka masu kyau sun wanzu, sannan ga kulawa da wasanni daga wajen maigida, amma har in akwai wani abu da ke dauke mata hankali, ko fargabar faruwar wani abu, ko takasa tsaida hankalinta ga ibadar auren, tana tunanin wani abu, kamar wani aiki da ta fara bata ida ba, ko tana tunanin ayyukan da za ta yi gobe, to wannan duk suna iya hana bayyanar sha’awarta.

Don cin cikakkiyar nasarar ibadar aure ga duka bangarorin biyu, wato maigida da uwargida; sai maigida ya tabbatar da lallai ba wani abu da zai iya bijirowa har ya dauke hankalin uwargida lokacin gabatar da ibadar aure; yana iya tabbatar da haka tun cikin hirarsu kafin lokaci, sai ya bincika har ya tabbatar cewa komai ya yi tsaf-tsaf cikin zuciya da ma’aikatar hankalin uwargida; idan ya ji akwai wani aiki da bata karasa ba, kuma tana son karasawa: ko misali kamar ya ji tana son ta goge kayan yara na makaranta, sai ya je ya tayata su goge koma ya goge mata, wannan zai haifar da jin dadi biyu cikin zuciyarta: Ga shi dai maigida ya sauke mata wannan nauyi gashi kuma ya yi jarumta ya taimake ta da aikinta, wanda alama ce ta nuna kulawa da so da kauna.

Idan kuma maigida ya gano wani abu ne ke damunta a zuciya, ko wani daga cikin yara yana mura ko tari, kuma ya fahimci abin ya tsaya mata a rai, to sai ya san yadda zai kawar mata da wannan damuwar da kalamai masu dadi, koma ya je ya dauki yaron ya rungume ya tofa masa addu’a, ya dai yi abin da zai kara mata kwarin gwiwar da za ta kawar mata da wannan damuwar, daga nan sai ya yi jan ta da hira mai dadi wacce za ta  kade duk wata birbishin damuwa daga zuciyarta har ta samu cikakkiyar natsuwa mai kai wa ga cimma cikakkiyar nasarar ibadar aure; to a irin haka sai duka bangaren biyu su ji dadi kuma su more a ibadarsu. A takaice dai karkade duk wata damuwa daga cikin zuciyar uwargida na daya daga cikin manyan mabudan sha’awarta; don haka magidanta sai a dage domin sunnah ce mai karfi mai haifar da dan karen jin dadi marar misaltuwa!

Domin taimaka wa uwargida ta kasance cikin natsuwar zuciya musamman game zamantakewarta da maigida, sai maigida ya rika kiyayewa da taka tsan-tsan wajen furuci ga uwargida, ya kasance yana mai zaben kalaman da suka dace a kowane lokaci, domin yana da cikin dabiar ‘ya mace nanata tunanin abin da ya bata mata ko wanda bai yi mata daidai ba, sai ka ga dan abin da bai taka kara ya karya ba ya hana mata samun natsuwar zuciya na wasu kwanaki, saboda yanayin da maigida ya yi kalamin, yanayin sautin muryarsa, kallonsa da shimfidar fuskarsa a lokacin da yake wani furucin duk suna da tasiri da samun natsuwar zuciyar uwargida ko akasin haka.

Misali: uwargida ta same ka tana neman izinin zuwa wani waje, yadda ka amsa mata zai kara kaunarka take yanke ko kuma ya haifar da tsananin jin haushinka: idan ka amsa da ‘a’a’ kawai ba wani karin bayani kuma tare da kallon inda take, kila ma kana duba waya ko wani abin daban ka amsa mata, to take za ta ji zafin yanayin da ka bata amsar kuma za ta yi ta nanata tunanin abin cikin zuciyarta wanda hakan zai sa ta kasa samun natsuwar zuciya. Amma idan ka kalleta cikin ido, tare da yi mata murmushi na musamman, sannan ka ce “yi hakuri ranki ya dade (ko gimbiya), ba yau ba don Allah kin ji?” to take yanke wani sabon kaunarka zai sauka a zuciyarta kuma ya samar mata da natsuwar zuciya. Duk da ka hana ta zuwa inda take son zuwa, amma yanayin da hana ta din cike da mutuntawa da romansiyya ya fi muhimmanci gareta da ace ka ba ta izinin zuwa a wata siga kishiyar hakan.

Wadannan abubuwa guda uku: Jin dadi cikin zuciya, wasanni da kuma natsuwa, dole sai sun kammalu kafin sha’awar Uwargida ta budo ta tumbatsa gaba daya, da fatan Allah Ya bada ikon kula da dagewa, amin.

Zan dakata a nan, sai mako na gaba In sha Allah Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.