Mabudan Soyayyar Maigida

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A yau kuma za mu shiga wani sabon maudu’in da ke bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda kullum zai kasance tsundum cikin kogin so da kaunarta kuma zai dunga marmarinta ya kasance ba ya son rabuwa da ita kuma […]

Mabudan Soyayyar Maigida
Mabudan Soyayyar Maigida

Assalamu Alaykum makarantanmu. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A yau kuma za mu shiga wani sabon maudu’in da ke bayani akan yadda uwargida za ta bude kofofin soyayyar maigidanta, ta yadda kullum zai kasance tsundum cikin kogin so da kaunarta kuma zai dunga marmarinta ya kasance ba ya son rabuwa da ita kuma duk abin da take so zai yi mata. Za mu fara da gabatar da wannan dan takaitaccen labari mai suna mowar mata don kara fito da ma’ana:

Mowar Mata.
Lallai yau na yarda da maganar da ake cewa wai mai hakuri bai iya fushi ba. Matana uku: Haulatu Harira da Bushira. Tun lokacin da na auro Bushira sai su biyun suka hade mata kai, kullum cikin yarfa mata habaici da bakaken kalamai suke, amma a iya sani na ba ta taba ramawa ba, sai dai ta maida abin wasa ta share su kawai.
Da ma da suka ji zan auri Bushira sai  suka same ni:  “Yanzu Maigida ka yi mana adalci ke nan? Sai ka auro mana wacce ta fi mu ta ko’ina kuma ka ce kana son a zauna lafiya? Mu dai mun yarda ka auro ko mata biyu ne amma ‘yan dai-dai mu ko ‘yan kasa da mu, amma ba irin su wannan ba!“
“Ta ya aka yi kuka san cewa ta fi ku? Bayan kuwa Allah Ya ce mafi karramawar cikinku a wajen Allah shi ne wanda ya fi takwa? Kuma Allah ne kadai Ya san wanda ya fi wani takwa, to ya aka yi kuka san ta fi ku takwa?
‘Haba Maigida! Kai ma ka san banbancinmu da nata ba daya ba ne… Ta yi karatu mai zurfi mu ba mu yi ba, ta haddace kur’ani ta iya Larabci sannan ga shi ta zauna a kasashen waje, kai ma ka san wayewarmu da nata ba daya ba ne…“ Inji Uwargida Haulah.
“Sannan ga shi an ce Uwarta tsohuwar kilaki ce, komi na rudar da mijin mutane ta iya shi.” Inji Barira, na cika da mamaki, domin ban san wannan labarin ba na wai Uwarta Kilaki ce, amma zan je in bincika.
“To karatu ai ku kuka hana kanku, na yi, na yi ku yi karatu, ba irin makarantun da ban saku ba amma kun ki, zuwanku gidana, yadda na nuna ina sonku da karatu, da haka kuma kuka so, to da ba abinda za ta nuna maku ta wannan fannin.”
“To mu dai gaskiya maigida ba mu yarda ka auro mana rikon kilaki ba, ko don gudun kar a cakuda mana zuriyya da iri marar kyau.” Na ce da su to na ji, zan yi tunani a kai, don dai su shafa mani lafiya kawai amma ba wani tunanin da zan yi, don na riga na gama tunani na.
Da na je hira gidan su Bushira, kai tsaye na tambaye ta: “An zo an ce mani wai zan auri goyon kilaki, da gaske ne?“
“Mhm, dama na san sai wani ya fada maka haka.   A iya sani na, gaba daya danginmu na wajen uwa da na uba ba wacce ta taba yin kilaki. Amma Dangin Mijin Mama Amurka haka suke cewa wai ita kilaki ce saboda irin yadda take wa Abbanmu.“
Ai kuwa ko ni na ga yadda Mama Amurka ke wa mijinta, in dai yana waje, to shi kadai ta sa a gaba ba ta damu da kowa ba. Ko don saboda zaman da suka yi a Amurka ya sa suke yin haka? Ko a gaban waye in mijinta ya dawo, Mama Amurka za ta ruga kamar karamar yarinya, ta taryo shi tare da oyoyo sannan ta rungume shi, in dai mijinta na gabanta, to kowa ma bace mata yake. Ranar da hakan ta faru a gaba na, ji na yi kamar in nutse kasa don tsananin kunya, amma su duka har Bushira, ko a jikinsu, ba su ma san ina jin kunyar ba.
Mama Amurka babbar ’ya ce ga Baban Bushira, Allah bai sa ta samu haihuwa ba, don haka ana yaye Bushira aka ba ta ita. Bushira ta yi karatun sakandare a Amurka, suna dawowa kuma ta yi karatun digirinta na daya da na biyu. Mama Amurka ba ta son aurena da Bushira saboda ina da mata biyu, tana jiye mata rikice rikicen da ka iya faruwa, amma Bushira ta dage sai ni, na san ba don komi ba sai don irin kyakykyawar fahimtar junan da ke tsakaninmu ne.
Ko don ba ita ta haife ta ba, Bushira ba ta da irin halayen Mama Amurka na tarairayar da namiji da kula da shi, domin na sha aika mata da sakonnin soyayya ta wayar tafi- da- gidanka, amma ko sau daya ba ta taba aiko min da irinsu ba. Saboda tsananin yadda take jin kunya ta, har ya sa nake zaton kila ba ta iya tantance fuska ta sosai, domin har aka daura mana aure ba ta taba bari mun hada ido da ita ba. Mhm…! Ai Sai bayan daura aure ne na sha mamaki, domin Bushira ta zarce duk inda nake zato wajen iya tarairayar namiji, duk da cewa ita ba ta yin haka a gaban kowa kamar yadda uwar goyonta ke yi.  
Sai mako na gaba za mu karasa wannan labarin in sha Allah.