Mabudan Soyayyar Maigida (12)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani cikin darasi na 2 a makarantar mowar mata daga inda muka tsaya makon jiya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo ciki, amin. Bayan bayanin daliba Asma’u, sai wata daliba ta daga hannu […]

Mabudan Soyayyar Maigida (12)
Mabudan Soyayyar Maigida (12)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani cikin darasi na 2 a makarantar mowar mata daga inda muka tsaya makon jiya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo ciki, amin.

Bayan bayanin daliba Asma’u, sai wata daliba ta daga hannu ta ce Malama ina da tambaya, ni ma ina matukar son ya zamana ayyukan addini sun kasance sama da komai a cikin rayuwata, amma koyaushe na yi kokarin haka abin bai zuwa ko ina sai ya rushe. Misali, Ina son da na gama Sallar Asuba kar in tashi sai na yi adhkar da karatun kur’ani, amma kodayaushe hakan bai samuwa gareni. Ya zama ka’ida sai na hado wa maigida shayi yana dawowa daga Masallaci, kuma dole sai na zauna mun sha tare, bai son in bar shi ya sha shi kadai. Da mun gama shan shayi kuma zan fara batun shirya yara makaranta da hada masu kayan karin kumallo. A haka sai ki ga safiyar, har ma rana da daren sun wuce ban aikatar da komai ba na daga ayyukan addini sai wadanda suka zama dole. To Malama don Allah a taimaka min yadda zan warware wannan matsala, Wallahi ina matukar son in ga ina adhkar da karatun kur’ani a kullum kuma a lokaci mafi dacewa.
Yadda za ki warware wannan matsala ita ce, sai ki rika zama ku yi adhkar da karatun kur’anin tare da juna, wannan wani sirri ne dake kara dankon soyayya tsakanin ma’aurata. Daga baya sai ku sha shayin tare. In kuma  maigidanki ya ki amincewa da wannan, to ki sani yin adhkar da karatun kur’ani ya fi shan shayin asuba tare da Maigida mahimmanci a rayuwarku duka ke da shi. Eh, tabbas mijinki shi ne oga kwatakwata amma Allah Shi ne Mahaliccinku kuma Ubangijinku duka ke da Ogan naki, sai kin daidaita ayyukan addininki sannan komai na rayuwar ki zai tafi cikin tsari yadda kike so. Don haka kamar yadda kika ji ‘yar’uwa Asma’u ta fada, sai ki rika tsayar da komai don yin ayyukan Allah ba ki tsayar da ayyukan Allah ba don yin ayyukan bayinSa. Da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa, amin.
Sannan Malama Bushirah ta cigaba da bayani kamar haka:  “Sai wata kuma ta fito ta bayyana mana alfanun da ta samu wajen aikatar da aiki na biyu na makon jiya. Wajen mutum biyar suka daga hannu  amma sai Malama Bushira ta nuna wata daliba da ke can gefe wacce ta lura ba ta taba sa baki ba in ana tattaunawa a ajin, ‘Yar’ uwa Fatimah ba ki yi naki aikin ba ne?”  “Na yi Malama,” ta amsa kanta a duke.” “To fito gaban allo ki ba mu labarin alfanun da kika samu?”
“Malama don Allah in rubuta mana sai ki karanta wa ‘yan ajin?”  “Haka zai cinye mana lokaci Fatima, bari…, “Malama Bushirah ba ta karasa magana ba sai ga abokiyar zaman Fatimah ta taso ta kawo mata takardar fuskaf (foolscap) kunshe da rubutun Fatimah a ciki. Malama Bushirah ta yi murmushi, sannan ta ce” lallai kin cika Bafullatana ‘yar’ uwa Fatee, wannan irin kunya haka!” Ta bude takardar ta fara karantawa ga sauran ‘yan aji kamar haka:
“Ba abin da yake burge ni game da Maigidana kamar iya kwalliya, iya sa kaya da iya shigarsa. Shi mai son kure adaka ne da tsananta ado kodayaushe, mutane da yawa na yaba iya shigarsa. Hatta  diyarmu Khadijah wata ran takan ce’ Baba ka yi kyau.’Amma ni ban taba yaba wa kwalliyarsa ba duk da  irin burge nin da yake yi in ya ya yi shiga. Bayan darasinmu na makon jiya na dauki niyyar ko sau daya ne sai in yaba wa mijina ko da kuwa kunya za ta kashe ni. Ina ta rokon Allah cikin sujjada da Ya karfafe ni Ya ba ni ikon zartar da wannan kudiri nawa. Amma duk da haka na kasa zartarwa har sai bayan kwana hudu, ya yi shiga zai fita, na tsaya ina kallonsa, ina kallon yadda shigarsa ta kawata shi kuma ta kara inganta surarsa, har ya lura ya tambaye ni lafiya dai ko? Na yi murmushin alkunya, na ce ba komai.
Bayan ya fita na yi karfin hali na aika masa sakon tes, ina yaba kwalliyarsa da yadda ya burge ni. Ai sai ya dawo, ya ce da ni ke kika aiko wannan sakon, kunya kamar ta kashe ni na kasa daga kai, ya tsare ni sai da na karanta masa da bakina ya ji, ya yi murna sosai har sai da ya dauke ni ya yi juyi da ni. Daga ranar duk in ya yi shiga sai na yaba masa in ma ya ji shiru zai zo ya ce min ko shigar yau ba ta yi ba ne? A hankali yanzu kunya ta fara tafiya game da wannan, har na fara yaba masa a wasu abubuwan ba wannan kadai ba. A dalilin wannan ne na fahimci ashe maigidana yana da kishirwar yabo, yanzu yawan yaba masa da nake ya kara kulawarsa sosai gare ni, wannan ya bude wani sabon shafin soyayya a cikin rayuwar aurenmu. “
“To mun gode ‘yar’ uwa Fatimah, sarkin kunya. Daga wannan za mu fahimci cewa duk wata kunyar da za ta shiga tsakanin jin dadin zamantakewar aure tsakanin ki da mijinki ba ta da amfani, dole ki yi dukkan kokarin yaki da ita ki ga cewa kin kawar da ita daga cikin yadda kike mu’amulantar mijinki.
Sai mako na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.