Mabudan Soyayyar Maigida 9

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani a kan darasin farko na makarantar mowar mata daga inda muka tsaya makon jiya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu, amin. Bayan ta gama amsa tambayar daliba Hajarah, sai Malama Bushira ta cigaba da bayani kamar haka:5. Abu […]

Mabudan Soyayyar Maigida 9
Mabudan Soyayyar Maigida 9

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Insha Allahu za mu cigaba da bayani a kan darasin farko na makarantar mowar mata daga inda muka tsaya makon jiya. Da fatan Allah Ya amfanar da mu, amin.

Bayan ta gama amsa tambayar daliba Hajarah, sai Malama Bushira ta cigaba da bayani kamar haka:
5. Abu na biyar da uwargida za ta yi don gyara barnar da yawan mita game da nakasun Maigida shi ne ta yi dukkan kokarin ganin ta zama salihar mace wacce Annabi Sallallahu alaihi wa sallam ya ce itace mafi daraja, mafi daukaka akan dukkan wasu abubuwan mallaka na jin dadin rayuwar duniya. Ki yi tunani akan salihan mata magabata, rayuwarsu ta zame maki abin koyi, da a ce sun kasance masu yawan mita da korafi, da ba su kasance abin misali ga duniya duka ba. Kin taba jin ance daya daga cikin matan  Manzon Rahmah ko na Sahabbansa Radhiyallahu anhum tana yawan mita da kwakwazo? Wannan ba dabi’un salihar mace ba ne.
Wata daliba ta daga hannu alamar tana son ta yi tambaya, Malama Bushira ta ba ta dama:
“To Malama su dabi’un salihar mace Yaya suke? Ko in ce yaya mutum zai yi ya zama Salihar mace?”
Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci Zalihah. Zama Salihar mace abu ne mai saukin gaske kuma mai matukar wahala. Yana da saukin ta fannin cewa ko wane dan Adam akan salihanci aka halicce shi, illa dai al’adu da rudin duniya dake gurbata wannan salihancin. Don haka yana da matukar sauki ga rai ta koma asalin yadda aka halicce ta akan ta koma wani abu daban. Sannan abinda ke sa salihancin mace ya zama abu mai matukar wuya shi ne shaidan da dakarunsa cikin mutanen da aljannu wadanda za su yi matukar kokarin hana zartar da wannan kyakykyawar niyya.
Babban Sinadarin da zai taimakawa mace ta zama saliha shi ne a kodayaushe, komai runtsi komai tsanani, ta sa Allah Subhanahu wa Ta’ala sama da komai da kowa a rayuwarta.   In ta rike wannan dabi’a da karfin gaske da ikon Allah salihancinta ba zai gurbata ba.
Da yawan mata suna yin kuskuren saka bukatun mijinsu ko ‘ya’ yansu sama da rikon addininsu, yayin da wasu sun dauki jin dadi da kwanciyar hankalinsu gabadaya sun jingina ga mazajensu, wannan babban kuskure ne, domin duk ranar da aka wayi gari wani abu ya shafi dangantakar da aka raja’a kacokan a gareta, sai ka ga mace ta fita hayyacinta, amma in tun farko ta jingina al’amuranta gabadaya zuwa ga Allah, duk abinda zai faru sai dai ya kara mata natsuwa, ba ya watsa mata hankali da tunani ba.
Sannan wani Sinadari da zai kara taimakawa ga mace ta zama saliha shi ne guje wa cin haram musamman ta hanyar abinci, abin sha, suturu da sauran kayan bukatu na yau da kullum. Komin irin bada kaimi da dagewar da mace ta yi ga son ta zama Salihar mace ba za ta taba zama ba matukar haram na shiga cikin abinci da abin shanta. Don haka mata ya kamata mu tashi mu dage mu yaki sha’awowi da son zukatan mu na son jin dadi da more rayuwar duniya. Mu yi koyi da Matan Sahabbai Radhiyallahu Anhum wadanda in mazansu za su fita neman abinci, suna masu rakiya da kyawawan kalaman: “Ka ji tsoron Allah Madaukaki, Ka yi hattara, Ka kiyaye, Kada ka kawo mana wani abu da ba halal ba, za mu iya daure yunwa, amma ba za mu iya daure wutar Jahannama ba.”
Abin takaici sanin cewa da yawanmu matan musulmi, muna sane da almundahana da munanan dabi’un neman kudin mazajenmu, wasunmu da yawa sun san mijinsu barawon kudaden al’umma ne, amma hakan ba ya tayar mana da hankali balle har mu yi kokarin farkar da su ta hanyar yi masu nasiha da tunatar da su Girman Allah da tsayuwa gabanSa ranar Hisabi. Da fatan Allah Ya kiyaye mu, Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, amin.
Za mu rufe darasin farko da bayar da wannan aiki da za ku je ku aikatar a gida kafin zagayowar mako insha Allah. Ga assignment din, kowacce ta rubuta a littafinta kuma ta tabbatar da aiwatar da su kafin zagayowar mako insha Allah:
1.  Ki yi dukkan kokarin ganin kin zama Salihar mace ta hanyar sa Allah sama ga kowa a cikin zuciya da rayuwarki. Ki mike cikin dare ki yi sallar tsayuwar dare da niyyar neman karin kusanci ga Ubangijinki. Ki saki jiki ki zayyana dukkan matsalolinki ga Ubangijinki, lallai da sannu za ki ga amsoshin bukatunki.
2. Ki yaba wa maigidanki kullum sau daya a rana a kan daya daga cikin kyawawan dabi’o’insa ko wani suffa tasa da take burge ki.
3. Ki yi rubuta kyawawan dabi’un mijinki a wani littafi na musamman, sannan kullum ki dauko littafin kina karantawa.
4. Ki yi dukkan kokarin ganin kin yi fatali da yawan mita, korafi da kwakwazo, kar ki zama mai daga muryarki makwabta na ji  kina fada ga yara.   Maza ba su son mace mai yawan ihu da kwakwazo idan tana magana.
Alhamdulillah, karshen wannan darasi na yau ke nan, sai wani satin in Allah Ya kai mu. Kowacce ta tabbatar ta yi wannan aikin gida (Assignment) da aka ba ta.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawar Sa a kodayaushe, amin.