Mabudi Na 3: Mafi girman bukatar maigida
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina mana Barka da Sallah, Allah Ya maimaita mana da alheri, amin. Ga ci gaban bayani kan mabudan soyayyar maigida daga inda muka tsaya kafin zuwan watan azumi, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.Bayan ta yi sallama […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ina mana Barka da Sallah, Allah Ya maimaita mana da alheri, amin. Ga ci gaban bayani kan mabudan soyayyar maigida daga inda muka tsaya kafin zuwan watan azumi, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Bayan ta yi sallama ga dalibanta sun amsa, Malama Bushirah sai ta ci gaba da bayani kamar haka:
A yau za mu shiga bayani a kan mabudi na uku cikin mabudan soyayyar maigida. Wace ce za ta gaya mani ko wane abu ne mafi muhimmaci da kowane maigida yake tsananin bukata sama da komi? daliba Zainabu ta daga hannu, Malama ta ba ta izini:
“Kowane maigida yana tsananin bukatar nuna soyayya daga wajen iyalansa.”
Wannan haka ne amma ba shi ne mafi tsananin bukatar maigida ba. Bismillah Hajiya Binta:
“A gani na, mafi tsananin bukatar maigida ita ce gamsuwar ibadar aure.”
kwarai kuwa, samun gamsuwar ibadar aure bukata ce mai girma a wajen kowane maigida amma kuma akwai wacce ta fi ta. Bismillah Hafsah:
“Malama, to ina ganin samun lafiyayyen abinci a kan kari shi ne mafi soyuwar bukatar maigida”
Malama Bushirah ta yi murmushi tare da girgiza kanta. Wannan ma bukata ce mai girma amma ba kamar wacce aka gina ruhin dukkan da namiji a kanta ba. Kowa ya san da shahararriyar ayar nan ta cikin Suratun Nisaa’i, wacce Ubangiji Madaukakin Sarki yake cewa:
“Watau Maza su ne masu tsayuwa a kan mata…” A nan Allah Ubangiji Yana bayyana mana cewa maza su ne masu tsayuwa a kan mata ga dukkan bangarori na rayuwarta gaba daya. Don haka shi ne shugaba kuma jagoranta a cikin rayuwar aure da ma gaba daya rayuwar duniya. Shi ne mai tsayuwa gare ta game da kula da dukkan bukatocin rayuwa; kulawa da samar mata kayan bukatun rayuwa; kulawa da tarbiyyarta da rainon hankalinta; da sauran al’amuran yau da kullum na rayuwar aure da rayuwar duniya gaba daya.
Don haka, Allah Madaukakin Sarki Ya kagi halittar da namiji da tsananin bukatar son yi da kuma zartar da wannan aiki na tsayuwa da shugabantar matarsa, kamar yadda aka halicci mace da tsananin bukatar nuna kyakykyawar kulawa da tsanani kauna ga ’ya’yan da ta haifa.
Duk macen da ta fahimci wannan mabudi na uku kuma ta iya zartar da shi cikin rayuwar aurenta da mijinta, to ta rike mabudin ingantacciyar soyayya ga maigidanta. Zai rika ji da ita da biya mata dukkanin bukatunta. Domin wannan bukata ita ce abincin ruhin dukkan wani da namiji kuma mafi tsanani daga cikin bukatun zuciyarsa.
Wannan bukata kuwa ita ce bayyana tsantsar yabawa ga halayen namijintakarsa a kodayaushe. Idan uwargida na yawan nuna yabawa da kuma nuna wa maigida yadda yake burge ta da halayen namijintakarsa, wannan zai haifar da jin dadin zuciya da natsuwar rai ga maigida, kuma za ta kosar da yunwar ruhinsa game da tabbatuwa da daukakar namijintakarsa. Hakan zai sa ya saki jiki da ita sosai ya kuma shigar da ita cikin sirrukansa. Za ta kasance wajen samun amincinsa duk lokacin da ya shiga rudani.
Amma duk wannan ba zai yiwu ba har sai ta fahimci yadda a ake murda wannan mabudi a kofar zuciyar maigida. Ga bayanin yadda uwargida za ta aiwatar da haka:
1-Kamar Yadda Allah Madaukakin Sarki Ya bayyana, shi ne a gaba da ita, sai ta dauke shi a matsayin shugabanta a zuci da bayyane, a cikin ayyukanta da maganganunta, da kuma cikin mu’amalarta da shi.
2-Ta amince hankalinsa ya fi nata kuma ra’ayinsa da fahimtarsa a kodayaushe na sama da nata, koda kuwa ra’ayi ko fahimtarsa tana da rauni a zahirance bisa ga nata ra’ayi da fahimtar. Wannan ba domin karantar da hankalin uwargida ba ne sai dai domin wannan ita ce mafi ingancin tabbatuwar zaman aminci da samar da natsuwa tsakanin ma’aurata. Domin in uwargida tana yawan bayyana wa maigida yadda ta fi shi ilmi, wayau ko fahimtar abubuwa, tana yanka wani ciwo ne mai wuyar warkarwa a ruhin maigida. Yawan yanka irin wannan ciwo shi ke sa maigida ya nisanta kansa da uwargidansa, ya kasance bai shigar da ita sirrukansa kuma bai yin hira da ita, domin tana yawan kushe maganganunsa da nuna rashin ingancinsu; ko kuma abin har ya kai ga ya janye kula da ita ta wasu bangarorin rayuwa saboda da irin zurfin raunukan da take datsawa ga ruhin namijintakarsa. Don haka duk mai son ta bude kofar soyayyar maigidanta sai ta yi fatali da dukkan dabi’un da na ambata a sama haka kuma dole ta guji yawan yin gardama da maigida da kokarin son nuna ta fi shi gaskiya a cikin al’amura, musamman wadanda suka dangaci bangaren da maza aka sani da fada a ji a cikinsa ba mata ba, kamar bangaren sana’o’i da ayyukan maza, bangaren siyasa, labarun duniya, wasanni, ilmi da sauransu.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.