Mabudi Na 3: Mafi girman bukatar maigida (2)
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Malama Bushira ta ci gaba da bayani kamar haka:3-Abu na gaba da ya kamata uwargida ta kiyaye wajen murda wannan makulli na 3 shi ne, barin dukkan wadannan bakaken dabi’u wajen […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Malama Bushira ta ci gaba da bayani kamar haka:
3-Abu na gaba da ya kamata uwargida ta kiyaye wajen murda wannan makulli na 3 shi ne, barin dukkan wadannan bakaken dabi’u wajen mu’amularta da mijinta. Su wadannan dabi’u tasirinsu ga Soyayyar Maigida kamar tasirin dafi ne ga rayuwa, muddin uwargida na aikata daya daga cikinsu a kai-a kai, to zai yi wuya ta samu bayyanar ingantacciyar soyayya da kulawa daga maigidanta. Ga bayanin wadannan dabi’u da hanyoyin kauce masu da daina aiwatar da su cikin rayuwa aure:
1-Ya zama dole ga uwargida, mai son bude soyayyar maigidanta gaba dayanta, ta guji yawan yin mita, kyara da kwazzaba ga maigida a kan abubuwan da yake da rauni a cikinsu, ko a kan abubuwan da ya kasa aiwatarwa a cikin rayuwar aure ko a cikin rayuwa gaba daya. Musamman abubuwan da suka yi danganci namijintakarsa. Ta horas da kanta ta rika cijewa da kin wannan dabi’a a hankali har dainawar ya zama sassaukar dabi’a a gare ta.
2-Haka nan dole uwargida ta guji yin maida magana cikin fushi da nuna jin haushinta ga maigidanta lokacin da ya kasa aikatar da wani aiki daga cikin ayyukansa ko ya kasa sauke wani nauyi daga cikin nauyukan da suka rataya a kansa.
3-Haka nan babban kuskure ne kushe maganganu da kudirorinsa koda kuwa cikin wasa ne, domin wannan kina nuna masa bai da muhimmanci a gare ki ne. Ko yaro ake yawan kushe maganarsa da gwasale fahimtarsa, take yanke zai rika janye jikinsa ga wanda ya aiwatar da hakan a gare shi.
4-Uwargida kuma ta guji bayar da shawara ga maigidanta game da wani al’amari a lokacin da bai nemi jin ta bakinta ba.
5-Haka kuma ki guji nuna kin fi shi sani ko kwarewa game da wani daga cikin ayyukansa, sana’arsa ko bangaren da ya karanta na ilmi.
6-Haka kuma komin irin yadda abubuwa suka tsananta, komin irin yadda ranki ya baci, uwargida ki guji yin mita ga maigidanki a kan yadda kike hakurin zama da shi ko a kan yadda bay a samar maki da isassun kayan bukatun rayuwa. Haka nan labarta wa kawaye, makwabta ko dangi irin yadda iyayenki ko ’yan uwanki ke taimaka maku da gudunmuwar abinci ko kudi da sauransu.
7-Yaba wa wani namiji daban a kan wani hali na mazantaka shi ma yana illa ga soyayyarki a zuciyar maigida, koda kuwa shi ma maigidan naki yana da wannan hali da kika yaba.
8-A guji rashin maida hankali lokacin da yake ba ki labarin wani abu mai muhimmanci a gare shi. Ko ma mara muhimmanci ne, ko labarin wajen aiki, ko labarin abokansa ko wani abin dariya ko wata damuwarsa, ko wasu kudurorin zuciyarsa. Ya kamata ki ba shi hankalinki dari-bisa-dari ga sauraren naganarsa a kowane lokaci, ba ki basar da shi ba, ko ki share shi ko ki nuna ya dame ki da surutu ko ki nuna mashi kin kagara ya kare magana ya yi shiru.
9-Rashin yaba wa kokarinsa da dagewarsa, da rashin yaba masa lokacin da ya yi wani abu na bajinta.
10-A guji kushe wata siffa daga cikin siffofin jikinsa, kamar a ce masa ya tara teba da sauransu.
11-Nuna masa fin iyawa da fin karfi cikin abubuwa da al’amuran da maza ne suka yi kaurin suna a cikinsa, kamar faskare, shugabanci da jan ragamar iyali duka, da sauransu.
12-A guji yin bagu ga maigida da da zurfin ilminki, ko ki rika nuna iliminki da fahimtarki sun fi nasa yawa ko muhimmanci.
13-A guji yin aikin gwamnati alhalin maigida bai so ko ya hana. Haka kuma a guji bayyana wa mutane ai yin aiki ya zama dole don taimakawa ga kayan bukatun gida, wannan kamar kina nuna wa mutane cewa mijinki bai isar da ke ba, bai kosar da ke kuma ya kasa ga sauke nauyin da ya rataya a kansa.
Duk irin wadannan bakaken dabi’u suna zama kamar kaskantawa ne ga namijintakar maigidanki. Suna karkade masa kwarjinin zuciyarsa da karfin gwaiwarsa kamar yadda iska mai karfi ke dibar kura ta kadar. Hakan zai sa maigida ya kullaci uwargida, ya rika hantararta da bayyanar mata munanan dabi’unsa koda kuwa ya san hakan da yake yi bai dace ba kuma koda yana son ya rika nuna wa uwargida soyayya da kulawa ba zai iya ba saboda zurfin raunin wadannan bakaken dabi’u ga ruhin mazantakar da namiji.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.