Mabudi na 5: Yin ladabi ga shugabancin maigida
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga cigaban bayani kan mabudan soyayyar maigida daga inda muka tsaya satin da ya shige. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani Ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya zan ya amfanar da su, amin. Bayan ta yi sallama ga dalibanta sun amsa, Malama Bushirah […]
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga cigaban bayani kan mabudan soyayyar maigida daga inda muka tsaya satin da ya shige. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani Ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya zan ya amfanar da su, amin.
Bayan ta yi sallama ga dalibanta sun amsa, Malama Bushirah sai ta cigaba da bayani kamar haka:
“Makulli na 5 wajen bude soyayyar maigida shi ne tabbatar wa maigida cikakken ikon shugabanci, Jagoranci da jan ragamar gudanarwar gida da iyali duka da ma gabadaya rayuwar Uwargida. A baya mun karanta daga shahararriyar Ayar nan ta cikin Suratul Nisaaa’ inda Allah Madaukakin Sarki Yake cewa: ‘Maza su ne ke tsayuwa da shugabanci akan mata saboda abin da Allah Ya daukaka dayansu akan daya kuma saboda ciyar da su da suke yi daga dukiyoyinsu…’
Wannan Aya yana da kyau kowace mace ta haddace ta, ta san ma’anarta, ta ajiye kalmomin cikinta kusa da zuciyarta ta yadda za ta rika tuno su akai akai don su taimaka mata ga kwarewa wajen kwantar da kai da yin kyakykyawan ladabi da biyayya ga mijinta.
Allah mai Girman Karamci da Jalala, Ubangijin komi da kowa, Shi ne yake sanar da dukkan matan aure cewa mazajensu su ne masu tsayuwa da shugabanci akansu saboda falalar da Allah Ya ba su ta karfin jiki, karfin basira da nisan hankali wanda ya dara na ‘ya mace, kuma saboda ciyar da kula da ku da suke yi daga dukiyoyinsu. Don haka duk macen da ke son ta more rayuwar soyayya da maigidanta a nan duniya, sannan ranar lahira ana sa ran ta dace da gidan Aljannar ni’ima, to dole sai ta aje duk wani girma da jiji da kanta na ‘ya mace ta bi mijinta sau da kafa, ta bar shi ya yi cikakken mulki a gidansa da rayuwar iyalinsa duka ba yawan jayayya da gardandami daga wajenta. Duk wani hukunci da ya yanke tayi aiki da shi dari bisa dari, duk wani umarni da ya bayar ta yi iyakar kokarinta don ganin ta zartar da shi, duk wani hani da ya yi mata ko ya yi wa yara, to ta hanu ta kuma tabbatar cewa yara su ma sun hanu.
Sannan yana daga cikin tabbatar wa maigida cikin ikon shugabanci mace ta tsaya matsayinta na uwargida ga mijinta da kuma na kula da gida da kuma kula da yara, kar ta ce za ta rika wuce wuri tana zartar da abubuwan da suke cikin hurumin zartarwarsa na maigida. Kar ta ba yara dama zuwa wata unguwa ko wani gida da sunan ziyara ba tare da saninsa da amincewarsa ba. Kar ta sa a yi wani muhimmin aiki ko gyara a cikin gidansa ba tare da amincewarsa ba. Kar ta bayar da damar shiga gidansa ba tare da amincewarsa ba. Haka kuma bai kamata ta gewaye a bayan fage tana gabatar da wata harka ta neman kudi, kasuwanci ko adashi ba tare da sani da izininsa ba.” Malama Bushirah ta dakata don ba wata daliba damar yin tambaya:
“Malama anya wannan mabudi zai yuwu mu iya murda shi a mazajen wannan zamanin kuwa? Gaskiya mazan zamanin in ka ce za ka yi masu haka kashinka ya bushe. Maimakon su darajjaka su girmamaka sai dai su wulakantaka su mai da kai ba kowan komi ba, abin tausayi.”
Malama Bushirah ta yi murmushi: “Yo su mazan zamanin nan me ye banbancinsu da mazan sauran zamunna? Namiji namiji ne a kowane zamani yake. In dai Allah Ya sa mutum ya zama mijinki to dole ki yi masa cikakkiyar biyayya in dai kina fatan dacewa da rahmar Ubangiji, domin Allah Ya san da zuwan wannan zamanin da irin mazan auren cikinsa, amma duk da haka Ya ce su dai mazan su ne shugabanni akan matansu a kowane lokaci. Kuskuren da muke mu kan mance da cewa biyayyar aure itama ibada ce, kamar yadda mace ba ta iya cewa ba za ta kyautata sallah ko azuminta ba saboda zamani ya canza, to haka bai kamata ta ce ba za ta yi cikakken ladabi ga shugabancin maigidanta ba saboda canzawar zamani. Mace ta yi la’akari da girman wanda ya nada namiji a matsayin shugaba, ta juya baya ga karantar wanda aka nada din. Shi ladabi ga shugabancin mijin farkonsa Ladabi ga Allah SWT ne”
“To ni dai na gamsu da bayaninki, kuma gaskiya ina kokarin yin ladabi ga shugabancin mijina da bin umarninsa, waje daya ne muke saba wa, shi ne wajen kula da yaranmu, ya cika takura wa wasu daga cikinsu da dora masu tsatstsauran hukunci akan laifin da bai kai ya kawo ba, to a irin haka ne wata sa’in sai in tanka in nuna masa hukuncin da ya yanke masu ya yi tsanani da yawa, in kuma wani horo ya aza masu zan matsa masa sai ya daga masu shi. To Malama ya ya kamata in yi irin wannan yanayin?
Sai sati na gaba insha Allah za mu ji amsar da Malama Bushirah ta bayar. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.