Mabuxan Soyayyar Maigida 5

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili.  Insha Allahu yau za mu leqa makarantar mowar mata da Malama Bushirah, tare da taimakon kishiyoyinta  biyu Haulatu  da Barira ke gabatarwa don koyar da matan aure yadda za su gyara zamantakewar aure tsakaninsu da mazajensu, yadda za su zama ‘yan lele ga mazajensu ya kasance […]

Mabuxan Soyayyar Maigida 5
Mabuxan Soyayyar Maigida 5

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haxuwa cikin wannan fili.  Insha Allahu yau za mu leqa makarantar mowar mata da Malama Bushirah, tare da taimakon kishiyoyinta  biyu Haulatu  da Barira ke gabatarwa don koyar da matan aure yadda za su gyara zamantakewar aure tsakaninsu da mazajensu, yadda za su zama ‘yan lele ga mazajensu ya kasance kullum suna cikin so da begensu.

Dukkan xaliban sun hallara lokacin da Malama Bushirah ta shigo cikin ajin, bayan ta yi sallama sun amsa, sai ta fara bayani kamar haka: “Ya kamata mu san junan mu kafin mu shiga cikin darasi na farko, ni sunana Bushirah, zan koyar da ku darussa goma daga cikin goma sha ukun dake cikin jadawalinku. Bari mu fara daga dama.” Bayan duka xaliban sun gama gabatar da kansu, sai malama Bushirah ta shiga bayanin darasi na farko kamar haka:
Mabuxi na farko da zai buxe maki soyayya da dukkan kulawar da kike buqata daga maigidanki yana da matuqar muhimmanci sosai, domin shi ne qinshiqan dukkan darussan da za su biyo baya akan yadda ake mallake miji, in har babu wannan sinadari na farko, to sauran sinadaran ba za su yi tasiri ba duk irin qwazon da aka yi akansu. Ga wannan Sinadari:” Sai Bushirah ta xauki abin rubuta ta rubuta sinadarin farko a jikin allo tare da ja masa layi a qasa:
Farar Qauna: “Ko akwai wacce za ta gaya mana ma’anar wannan kalma?” Wata daga can baya mai suna Maijidda ta xaga hannu:  “Farar qauna ita ce ka so mutum tsakani ga Allah ba saboda siffarsa ko wani abu da ya mallaka ba.”
“Qwarai kuwa, wannan babban vangarene na ma’anar wannan kalma. Wa kuma zai qara ba mu wata ma’anar.”
Zainab ta xaga hannu sannan ta ce: “Farar qauna shi ne ka so mutum kamar yadda kake son kanka.” “Wannan shi ma wani muhimmin vangare ne na ma’anar wannan kalma, sai dai har yanzu da saura. Wai zai bayyana mana wata ma’anar kuma?” Lantana ta xaga hannu, sannan tace: “Farar qauna ita ce irin qaunar da uwa take wa xanta, uwa tana son xanta ko ya yake kuma ba za ta tava qin sa komai munin hali ko halittarsa ba.”
Yawwa! Da kyau Lantana, haka farar qauna take a ma’anance, amma a aikace akan maigida ta wuce nan, irin qaunar da za ki yi wa maigidanki sai ta wuce wacce kike wa xanki.   Shi maigida akwai wasu ginshiqai da suke tarbe da irin farar qaunar da ake masa har in har ana son ta buxo cikakkiya kuma ingantacciyar soyayya da kulawarsa, wannan ginshiqai guda uku ne:
1.  Ki aminta da halayensa gaba xayansu,  masu kyau da marasa kyau. Watau ki karve shi, ki yi na’am da shi a zuciyarki da mu’amalarki da shi gaba xayansa ba tare da cire wata xabi’a ko wani hali daga cikin gundarin halayyarsa wacce kike ganin ba ta dace ba, kuma ki riqa bayyanar da jin haushinki da qyamarki da wannan halayya, ki riqa son ki ga ya canza ya bar wannan halayya. Alal misali a ce mijinki yana da vangare guda biyu, xaya fari mai kyau, watau shi ne kyawawan xabi’unsa, xaya kuma baqi marar kyau, watau munanan xabi’unsa.   Duk mace mai son ta buxo tsantsar soyayyar mijinta gareta, dole sai ta maida hankali da tunananinta  ga kyawawan halayensa kaxai.  Ya kasance da su take mu’amalantarsa, xaya vangaren kuma ta juya masu baya ta daina kula su, lokacin da suka bayyana da lokacin da ba su bayyana ba. In ta yi haka ta maida hankalinta kacokan akan kyawawan halayensa, to a hankali tasirin munanan halayen za su vace daga cikin dangantakarsu, domin rashin kula su zai rage masu tasiri a hankali har su vace ya zamana kamar ba a tava yin su ba.
Wannan shi zai bijiro da wasu kyawawan halayen da za su maye gurbinsu. Don haka jin haushin munanan xabi’un maigida, da bayyanar da wannan jin haushin, da son ta qaqa sai ya canza halinsa ya yi kamar yadda kike so, guba ce da ke kashe daxin zamantakewar aure, tun da kin san mijinki  ya kai munzalin da har ya isa ya nemi aurenki, ya kuma aure ki, sannan kika same shi da wannan xabi’a da ba ki so daga cikin xabi’unsa, to duk wata mitarki da nuna jin haushinki ba za su tava sawa ya canza ba. tunda kika ga har ya bar gaban mahaifiyarsa bai canza ba, to ya za a yi ke rana xaya ki so canza shi kuma ya canzu maki alhali mahaifiyarsa ta kasa canza shi?

Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.