Mace da ‘yan uwanta sun halaka makwabciya a taron dangi

A makon da ya gabata ne al’umar unguwar Ja’en suka kasance cikin alhini saboda rasuwar wata mata mai kimanin shekaru 35 sakamakon dukan kawo wuka da makwabciyarta tare da ‘yan uwanta suka  yi mata saboda rigimar yara.Lamarin  ya faru ne a yammacin ranar Juma’a inda wata mata mai suna Na’ima G. Garba, wacce aka fi […]

Mace da ‘yan uwanta sun halaka makwabciya a taron dangi
Mace da ‘yan uwanta sun halaka makwabciya a taron dangi

A makon da ya gabata ne al’umar unguwar Ja’en suka kasance cikin alhini saboda rasuwar wata mata mai kimanin shekaru 35 sakamakon dukan kawo wuka da makwabciyarta tare da ‘yan uwanta suka  yi mata saboda rigimar yara.
Lamarin  ya faru ne a yammacin ranar Juma’a inda wata mata mai suna Na’ima G. Garba, wacce aka fi sani da Maman  ‘Yanbiyu, ta shiga gidan makwabciyarta marigayiya Maryam Alasan tana zazzaga mata masifa tana cewa ta gaji da dukan da ‘ya’yanta ke yi wa nata ‘ya’yan, a inda ita kuma ta ba ta hakuri tare da alkawarin yi wa tufkar hanci.
Sai dai kamar yadda wadanda al’amarin ya faru a kan idanunsu suka shaida wa Aminiya sun nuna cewa hakurin da marigayiya ta ba Na’ima bai gamsar da ita ba, inda ta ci gaba da zage-zage har tana cewa idan har ‘ya’yan marigayiyar  suka sake dukan mata ‘ya’ya to wallahi sai ta dauko mata ‘yan sanda. “Jin haka daga bakin makwabciyartata ya sa marigayiyar ta mayar mata da martani cewa me ya yi zafi da har za a hada da ‘yan sanda? Daga nan sai suka shiga cacar baki, a nan sai ita Na’ima ta dauki kujera (‘yar tsugune)ta kwada wa marigayiya Maryam a wuya, ita kuma sai ta sa hannu ta kwashe ta mari.”
Majiyarmu ta kara da cewa, “jin hayaniya ta yi yawa a gidan ne ya sa wata makwabciyarsu ta shiga gidan ta fito da Na’ima waje.  Daga nan sai Na’iman ta kira ‘yan uwanta a waya cewa su zo, ba tare da bata lokaci ba kuwa sai ga su har su shida, ciki har da mahaifiyarta, inda suka afka gidan marigayiyar suka hau ta da duka. Da marigayiyar ta ga abin ya yi yawa sai ta shige daki ta kulle kofa, amma hakan bai sa sun hakura ba sai da suka farfasa mata gilasan taga tare da karya kofar gidan.”  Inji majiyarmu.
Rahotanni sun bayyana cewa, bayan wannan lamari ya faru sai ‘yan sanda suka zo suka tafi da matan da suka yi fadan zuwa ofishin ‘yan sanda na Sharada. A nan ne aka sulhunta su. Sai dai tun daga wannan lokaci sai Maryam ta samu ciwon wuya sakamakon kwada mata kujera da Na’ima ta yi, har ya kasance ba ta iya juya wuyanta gaba daya.
Aminiya ta jiyo cewa, yayin da ciwon wuyan ya yi wa marigayiyar tsanani sai ‘yan uwanta suka kai ta Asibitin kwararru na Murtala inda aka kwantar da ita tsawon kwana uku kafin daga bisani ta ce ga garinku nan.
Lubabatu Alasan ‘yar  marigayiya Maryam ce, wacce ita ma ta samu nata rabon na duka, ta bayyana wa Aminiya yadda makwabta suka kwace ta a hannun wanann makwabciyartasu lokacin da ta yi niyyar jefa ta a rijiya. “lokacin da aka yi duk wannan hayaniyar ba na gida, ina dawowa kafin na shiga gida sai wata kanwata take gaya min abin da ya faru. Ni kuma sai na rika fada ina cewa me ya sa su kuwa su Mama suke irin wannan don dai su jawo mana abin kunya a unguwa. Ashe ita Na’ima ta ji abin da nake fadi, nan da nan sai ta fito daga gidanta ta hau sirfa min zagi wai inje in gaya wa mahaukaciyar uwata maganar da nake fadi, ni kuma a take na mayar mata da zagin da ta yi min. sai ta dauko hannu za ta doke ni, ni kuma sai na gudu wani gidan makwabtanmu, inda ta bi ni a guje ta same ni ta shake min wuya tana kokarin jefa ni a rijiya, tana cewa wai za ta kashe ni. A nan dai mutanen gidan suka kwace ni da kyar a hannunta. Tun daga wannan shakewar da ta yi min ban sake sanin abin da ke faruwa ba, sai farkawa na yi na ga mutane na yi min fifita.” Inji ta.
Lubabatu ta kara da cewa, “Yawancin lokuta a kan samu sabani tsakanin kannena Abdussamad da Imrana da kuma ‘ya’yan wannan makwabciya tamu, wato Fatima da Zainab, da yake dukanninsu kusan sa’annin juna ne, da zarar hakan ta faru Na’ima za ta biyo kannena har gida ta zazzage su. Wani lokacin ma har shigar wa ‘ya’yanta fadan take yi. Lamarin da ya sa har mamanmu take tsoron ta ga ‘ya’yan Na’ima sun shigo gidanmu, saboda tsoron abin da zai iya biyo baya. Ashe ba ta san cewa gudun kaddara guzurin tarar  da ita ba ne” Inji ta.
Malam Ibrahim Ya’u  shi ne yayan marigayiyar, ya bayyana wa Aminiya matsayin iyayenta a kan lamarin, inda ya ce ba su yafe ba, kuma za su nemi hakkinsu har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi, musamman ma ganin cewa wannan ba shi ne karo na farko da Na’imar ke zuwa har gida tana ci wa marigayiyar mutunci ba .”A gaskiya ba za mu yafe wannan keta haddi da aka yi mana ba. Ta yaya za a yi ta shiga har cikin gidanta ta yi mata duka ita da ‘yan uwanta har suna ikrarin cewa za su kashe ta su kashe banza, don a cewarsu, idan sun kashe ta babu abin da za a yi musu. Abin haushin ma shi ne wannan shi ne karo na uku da matar nan ke shiga har gida tana ci wa marigayiyar mutunci a duk lokacin da aka samu sabani a tsakanin ‘ya’yansu. Idan ma ban da rashin hakuri irin na mutane me zai sa mutum yin fada a kan yara? Yaran nan fa da suka yi fadan dukkaninsu ba su wuce shekaru biyar da haihuwa ba.”    
Yayan marigayiyar ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil’Adama da su shigo cikin lamarin tare da taimaka musu wajen ganin sun kwato hakkin  ‘yar uwarsu, don ya zama izina ga masu irin wannan al’ada ta yi wa jama’a taron dangi. “A yanzu haka ita kanta Lubabatu ba lafiya gare ta ba, sakamakon dukan da wannan mata ta yi mata. Ko a jiya sai da na kai ta asibiti na kuma saya mata magani. Don haka muna neman kungoyoyin kare hakkin bil’Adama da su shigo cikin wanann magana, don mu a gaskiya an zalunce mu. Bayan da ta rasu da kaina na sake komawa ofishin ‘yan sanda na Sharada na sanar musu cewa ‘yar uwata da makwabciyarta ta doke ta ta rasu sakamakon wannan duka da ta yi mata a wuya, inda suka dauki maganganuna tare da alkawarin za su nemi mu amma har yanzu mun ji shiru. Haka kuma ita matar da ta yi wanann aika-aika tana nan tana yawonta a gari, har ma tana alfahari da cewa ta kashe ta ta kashe banza. Kin ga a nan ba ta nuna  wani abu na nadama ba. “ Inji shi  
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Na’ima ko wani daga cikin ‘yan uwanta  abin ya ci tura, sakamakon guduwa da ta yi daga unguwar bayan ta samu labarin rasuwar abokiyar fadan nata.
Jama’a da dama sun bayyana marigayiyar wacce ta rasu ta bar ‘ya’ya 10, ciki har da jaririya ‘yar wata uku da haihuwa, a matsayin mace mai kamun kai da hakuri tare da yin kyakkyawar ma’amala da makwabta.     
Lokacin da Aminiya ta tuntubi rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano Kakakinta ASP Magaji Musa Majiya ya shaida wa mata cewa al’amarin bai zo teburinsa ba, tare da bayyana cewa a duk lokacin da ya samu cikakken bayani a kai zai tuntube mu. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba mu ji wani abu daga gare shi ba.