Mace mace mai ilimin addini da na zamani son kowa ce – Lubabatu Ladan
Hajiya Lubabatu Ladan babbar ma’aikaciya ce a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi ta shafe sama da shekara 25 tana aiki a asibitin. Cikin tattaunawarta da wakilinmu a Bauchi ta yi fashin baki game mahimmancin karatun ’ya’ya mata. Sannan ta yi kira ga mata da su bada kulawa ta musamman wajen […]
Hajiya Lubabatu Ladan babbar ma’aikaciya ce a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi ta shafe sama da shekara 25 tana aiki a asibitin. Cikin tattaunawarta da wakilinmu a Bauchi ta yi fashin baki game mahimmancin karatun ’ya’ya mata. Sannan ta yi kira ga mata da su bada kulawa ta musamman wajen neman ilimin addini da na zamani ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Tarihin rayuwarki?
Sunana Hajiya Lubabatu Ladan. An haifeni a shekara ta 1970 a garin Bauchi. Na fara makaranta a Kobi Primary School. Na yi makarantar sakandare a Gombe Doma inda na kammala a shekara ta 1986. Daga nan na zarce zuwa makarantar Bakas, bayan na gama sai na fara aiki a Asibitin kwararru na jiha wato (Specialist Hospital Bauchi) da yanzu ya koma a asibitin koyarwa.
Daga nan na sake komawa karatu a Kwalejin Koyon Kiwon Lafiya da ke Ningi kuma yanzu haka ina cigaba da aiki da kuma cigaba da karatu. Hausawa sun ce gemu baya hana karatu. Babban abinda yake gyara rayuwar dan adam shine ilimin addini da na zamani babu wata al’umma da za ta samu cigaba sai da ilimi.
Aminiya: Wadanne matsaloli kika fuskanta lokacin da kike karatu?
A gaskiya na fuskanci dimbin matsaloli a lokacin da nake karatu. Gidana babu kowa, na bar mijina da yara, shi yake kula da wasu dawainiyyarsu a wasu lokutan idan na tafi makaranta saboda haka na fuskanci kalubale amma yanzu muna godiya ga Allah tunda mutum yana da rai da lafiya.
Lokacin da nake karatu a makarantar kiwon lafiya da ke Ningi a can nake kwana duk ranar Juma’a nake dawowa gida domin duba mijina da ‘ya’yana ranar Lahadi da yamma na sake shiga mota zuwa makaranta Ningi. Ga shi yau na kammala sai labari.
Aminiya: A wace shekara kika yi aure?
Na yi aure a shekarar 1990 a watan Disamba. Yanzu haka ina da ‘ya’ya shida da mijina kuma muna zaune lafiya muna cigaba da soyayya da mutunta juna.
Aminiya: Akwai bambanci a tsakanin ingancin ilimin da da na yanzu?
Tabbas akwai bambanci tsakanin yadda mata suke karatu ada da kuma yanzu. Lokacin da muke makaranta babu batun satar jarrabawa amma yanzu wannan matsala ta zama ruwan dare game duniya. Wasu ba sa karatu sai satar jarrabawa don haka wasu ke zargin cewa yanzu akwai ilimi a tsakanin al’umma amma kuma ilimin ba shi da inganci kamar da. Kuma yanzu akwai wasu daga cikin malaman yadda suke karantar da daliban ba sa bin wasu ka’idoji don haka kowa yake abinda ya ga dama a wasu daga cikin makarantun kasar nan amma muna fatar dalibai su guji satar jarrabawa domin ba zai haifar musu da da mai ido ba.
Aminiya: Wadanne matsaloli kike ganin matan arewa suke fuskanta a bangaren ilimi?
Gaskiya wasu daga cikin matan arewa suna fama da koma baya a bangaren ilimi domin akwai wasu daga cikin maza idan suka auri mace tana karatu da zarar ta shiga gidan mijinta shi kenan ta yi ban-kwada da neman ilimin addini da na zamani. Wadannan abubuwa suna daga cikin matsalolin matan Arewacin kasar nan. Akwai kuma wadanda suke so matansu su cigaba da karatu amma saboda matsalar talauci babu yadda za su yi sai dai su zauna a gida su cigaba da yin girki da kula da gida.
Kuma ya kamata a fahimci cewa akalla kashi 85 cikin 100 na maza sun fi son auren mace wadda take da ilimi domin ilimin zai amfani mijin da ‘ya’yanta saboda haka duk lokacin da nake zaune da ‘yan uwana mata babu abinda nake fada musu kamar a cigaba da neman ilimi. Amma akwai wasu daga cikin maza sun fi bada fifiko wajen ilimin maza kamar yadda neman ilimin yake kan maza haka yake kan mata.
Aminiya: Me za ki ce game da matan da shugaban kasa ya ba su mukamin minista?
Tabbas shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada mukaman minista ga mata shida wadanda suka bada gudunmawa wajen kafa wannan gwamnati Duk mace tana son ‘yar uwarta mace, saboda haka muna taya su murnar samun wannan mukami. Allah Ya ba su damar sauke nauyin da aka dora musu.
Aminiya: Menene burinki a rayuwa?
Babban burina a rayuwa shi ne na cigaba da neman ilimin addini da na boko domin yanzu duniya ta sauya, abubuwa da dama sun koma kan yanar gizo intanet kuma duk wanda yake son cigaba a rayuwa dole ya rika tafiya da zamani daidai bakin gwargwado.
Aminiya: Wadanne abubuwa kike so gwamnatin jiha da ta tarayya su yi a bangaren ilimi?
Babban abinda gwamnati ya kamata ta fara yi a bangaren ilimi a Arewacin Najeriya shine dole a bullo da wani sashe na musamman da zai rika wayar da kan matan karkara da kuma wadanda ke zaune a birane. Akwai rahotanni da ke nuni da cewa yankin Arewa maso Gabas yana fama da koma baya a bangaren ilimi sakamakon tashe-tashen hankula wanda ya yi sanadiyar lakume dimbin rayuwar al’umma. Don haka akwai bukatar gwamnati ta karkata akalarta wajen wannan yanki don a tallafa musu wajenb farfado da ilimi da kuma bunkasa shi a yankin.
Saboda haka dole sai gwamnati ta tashi a tsaye kafin a samu cigaba a sashin ilimi a arewacin kasar nan. Iidan mutane suna da ilimi akwai dimbin matsaloli da za su rage ga gwamnati kowa zai yi abinda ya kamata a kasar.
Aminiya: Idan kika ga tarin mata suna zaune basa karatu ba sa aiki yaya kike ji a zuciyarki?
Kamar yadda ba na kaunar ganin matashi yana zaman kashe wando a tsakanin al’umma haka kuma ba na kaunar ganin mace tana zaune ba ta neman ilimin boko da na addini. Saboda haka ba na kaunar zama da mace wacce ba ta aiki sannan ba ta karatu, sai zaman tsegumi daga nan zuwa can.
Aminiya: Me ya baki sha’awar shiga aikin kiwon lafiya?
Babban abinda ya sa na shiga aikin kiwon lafiya shi ne don na bayar da gudunmawata ga marasa lafiya musamman ga mata a lokacin haihuwa. Aikin asibiti ba wani aiki ba ne da mutum zai tara abin duniya. Aiki ne wanda idan mutum ya rike tsakaninsa da Allah bayan ya samu lada duk wanda ya samu lafiya ta sanadiyyarsa yana da lada a wajen Allah.
Domin tun ina yarinya nake sha’awar aikin asibiti kuma ga shi Allah ya amsa addu’a ta shekara ta 25 ke nan ina aiki a asibiti kuma muna zaune lafiya da al’umma.
Aminiya: Idan kin yi ritaya wadanne abubuwa za ki yi a rayuwa?
Da yake aikin gwamnati shekara 35 ake yi sai mutum ya yi ritaya bayan na kammala idan muna cikin masu rai da lafiya babu abinda nake bukata kamar noma da kiwo domin na fahimci cewa akwai alheri sosai a harkar noma da kiwo domin duk al’umma da take noma abinda za ta ci to tabbas za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Aminiya: Wadanne abubuwa ke haifar da mutuwar mata a lokacin haihuwa?
Abubuwan dake haddasa mutuwar mata a lokacin haihuwa suna da yawa.
Mace mai ilimin addini da na zamani son kowa ce – Lubabatu Ladan
Akwai jahilci da rashin zuwa asibiti akan lokaci da rashin zuwa awo a kan lokaci da mace ta samu juna biyu suna daga cikin abubuwan dake haddasa wannan matsala.
Amma yanzu haka a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi an samu raguwar wannan matsala na mutuwar mata a lokacin haihuwa. An samu wannan nasarori ne sakamakon wayar da kan mata da muke yi daga lokaci zuwa lokaci ta kafafen watsa labarai.
Aminiya: Menene sakonki ga matan Najeriya musamman na Arewa?
Babban sakona ga matan arewa shin e mu hada kanmu waje daya domin babu wata al’umma da za ta samu cigaba mai amfani sai da hadin kai. Sannan kuma matan da suka yi aure su cigaba da kula da mazajensu wajen tsafta da gyara abinci su kuma zamo masu ladabi da biyayya.
Bayan haka ina kira da babbar murya ga maza da su cigaba da yin hakuri da mata domin Allah ya yi mu masu rauni. A wasu lokutan babu abinda yake da wahala kamar zamantakewar aure. Kowa da irin tunaninsa, da ma hausawa sun ce zo mu zauna, zo mu saba.
Aminiya: Menene sakonki ga mata ma’aikata?
Sakona ga mata ma’aikata sh ine ya kamata mu sauya tunaninmu, mu fahimci cewa bayan mutum ya kammala aikin gwamnati akwai wani rayuwa daban bayan ritaya a rika hadawa da wasu kananan sana’oi domin yin haka zai sa mace ta samu karbuwa a wajen mijinta. Da yawa daga cikin maza ba sa son ba ni-ba ni kullum. Idan mace tana aiki wasu lokutan za ta tallafa wa mijinta da wasu abubuwa na cefane musamman idan yana fama da rashin kudi.
Aminiya: Yaushe kika fara karanta jaridu?
Tun ina karatu a makarantar Sakandare na ke karanta jaridu da mujallu domin suna kara wa mutum ilimi. Kuma wadannan jaridu na hausa tun lokacin da aka fara bugasu a Najeriya an samu gagarumin sauyi a bangaren hausa mutane da dama sun fi fahimtar jaridar hausa fiye da ta turanci.
Bayan haka ina kira da babbar murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewacin kasar nan da su yi wa Allah su tallafa wa matan da suka rasa mazajensu sakamakon tashe-tashen hankula. Wannan shiyya ta arewa muna da dimbin marayu wadanda suke bukatar daukin gaggawa.
Kyautatawa marayu yana rage dimbin masifu a tsakanin al’umma don haka dole sai kowa ya bada tasa gudunmawa kafin a samu magance wannan matsala. Da yawa daga cikinsu ba sa zuwa makaranta domin masu daukar nawainiyarsu sun kwanta dama.
Aminiya: Daga karshe menene sakonki ga matan Najeriya?
Babban sakona ga matan Najeriya duk da cewa ni ba ’yar siyasa ba ce ya kamata mu cigaba da addu’a ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin ya zo da manufofi masu kyau na inganta rayuwar ’yan Najeriya. Kowa ya ga abubuwan da suka faru a shekara shida. Muna fatar Allah Ya ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Duk masu neman zagon kasa ga kasa, Allah Ya tona asirinsu a duk inda suke.
Wannan jarida ta Aminiya na yi matukar farin ciki bisa wannan dama da kuka ba ni domin tofa albarkacin bakina game da abubuwa da dama nagode sosai.
Aminiya: Muma mungode.