Mace-macen da suka fi girgiza Najeriya a 2020

Manyan mace-mace 20 da ba za a manta ba a shekarar 2020 mai bankwana

Mace-macen da suka fi girgiza Najeriya a 2020

Gwamna Zulum yayin da ake sallar jana’iza

Masu iya magana kan ce rayuwa ba ta yi dadi ba tunda ba a kashe mutuwa ba.

An yi rashe-rashen da suka girgiza mutane a Najeriya matuka a shekarar 2020 mai yin bankwana.

Mace-macen shekarar sun shafi dukkannin bangarori da suka hada da sarakuna, malamai, ’yan kasuwa, jami’an tsaro, jami’an gwamnati, ’yan siyasa, talakawa, da fitattun mutane da sauransu kamar haka:

1. Kisan Zabarmari

A safiyar Asabar 28 ga watan Nuwamba, 2020,  mayakan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa yankan rago a Zabarmari, Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno.

Mayakan sun ritsa manoman ne a gonakinsu da ke kauyen Koshebe, suka daddaure su, suna ta yanka wasu, wasu kuma ana fille kansu.

Hukumomin Najeriya sun ce mutum 43 ne aka kashe, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutum 110 ne, Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau kuma ya ce mutum 78 ne mayakansa suka hallaka, wasi saboda sun kama wani mayakin kungiyarsa sun damka wa sojoji.

Zulum yana taimakawa wajen ajiye gawa
Kisan gillan na Zabarmari ya fusata jama’a tare da shan la’anta daga sassan duniya.

Baya ga kiraye-kirayen Shugaba Buhari ya kori Manyan Hafsoshin Tsaro, harin Zabarmari ya sa Majalisa bukaci Shugaban Kasar ya je ya yi mata bayani, ko da yake ya soke zuwan da ya shirya yi Majalisar.

Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris

2. Sarkin Zazzau

Dubun-dubatar mutane sun yi dafifi a Fadar Sarkin Zazzau da ke birnin Zariya cike da alhinin rasuwar Sarkin Zazzau na 18, Alhaji Dokta Shehu Idris.

Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya rasu ne a ranar Lahadi 20 ga watan Satumba bayan fama da rashin lafiyar da aka yi jinyar sa a Babban Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna.

Sallar Jana’izar margayi Sarki Shehu Idris mai shekar 83 ta tara mutane har babu masaka tsinke.

Ya rasu bayan shekara 45 yana Sarautar Zazzau kuma ya fito ne daga Gidan Katsinawa, daya daga cikin gidajen sarautar Zazzau.

3. Abba Kyari

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a 17 ga Afrilu yana da shekara 67.

Ya rasu ne sakamakon cutar COVID-19 da ake zargin ya kamu da ita a ziyararsa zuwa kasar Jamus don tattaunawa batun gyara wutar lantarkin Najeriya.

Shi da kansa ya sanar da kamuwarsa da cutar kuma rashin lafiyara ta kawo tsaiko a harkokin gwamnati —sau biyu ana dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa.

Marigayi Abba Abba Kyari

Daga baya ya zabi ya dauki nauyin jinyarsa daga aljihunsa inda aka yi jinyar shi a asibitin First Cardiological da ke Legas har ya rasu.

Kamuwarsa da cutar da ta kasance annobar duniya ta sa aka yi wa Shugaba Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnati, Boss Mustapha da sauran jami’an da suka yi hulda da shi gwajin cutar.

Bayan binne shi sai da Fadar Shugaban Kasa ta umarci ma’aikatanta da suka halarci jana’izarsa su killace kansu na sati biyu kafin su dawo aiki.

4. Sarkin Biu

Sarkin Biu a Jihar Borno, Alhaji Umar Mustapha Aliyu, ya rasu ranar Litinin 14 ga Satumba da dare bayan fama da rashin lafiya.

Sarki Umar Mustapha Aliyu ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da ke Gombe, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayi Sarkin Biu Alhaji Umar Mustapha Aliyu

5. Sheikh Ahmed Lemu

Fitaccen Malamin Musulunci kuma alkali, Sheikh Ahmed Lemu ya rasu ranar Alhamis, 24 ga Disamba, 2020.

Sheikh Ahmed Lemu ya rasu ne Minna, Jihar Neja, mahaifarsa bayan fama da jinya.

Mashahurin malamin ya bar duniya yana da shekara 91, shekara guda bayan rasuwar matarsa Aisha Lemu, mai wa’azi kuma marubuciyar Musulunci wadda ta rasu a watan Janairun 2019.

Sheikh Ahmed Lemu a lokacin da yake karbar Kyautar Sarki Faisal na Saudiyya

6. Balarabe Musa 

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PRP na Kasa, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ma ya rasu a 2020.

Tsohon dan takarar na Shugaban Kasar jam’iyyar PRP a zaben 2003 ya rasu ne a Kaduna yana da shekara 84 sakamakon rashin lafiya a ranar Laraba 11 ga Nuwamba.

Marigayi Abdulkadir Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kaduna

A 1979 Alhaji Balarabe Musa ya zama zababben Gwamnan Kaduna na farko kafin a 1981 Majalisar Dokokin Jihar ta tsige shi ya kuma zama gwamnan da aka fara tsigewa a Najeriya.

7. Abiola Ajimobi

Sanata Ishaq Abiola Ajimobi, tsohon Gwamnan Jihar Oyo, ya rasu bayan fama da cutar COVID-19 da wasu cututtukan da suka taba bangarorin jikinsa.

Ajimobi ya rasu a ranar Alhamis, 25 ga Yuni, yana da shekara 70 a asibitin da aka yi jinyar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari a Legas.

Majalisa ta bukaci a sa sunan Ajimobi a filin jirgin Ibadan
Marigayi Sanata Abiola Ajimobi

8. Sarkin Rano

Mai Martaba Sarkin Rano Alhaji  Tafida Abubakar Ila II ya gamu da ajalinsa a Asibitin Kwararru na Nasarawa da ke Kano.

Ya bar duniya a ranar Asabar 2 ga watan Mayu bayan an kwantar da shi a ranar Juma’a a asibitin.

Marigayi Sarkin Rano, Dokta Tafida Abubakar Ila
Marigayi Sarkin Rano, Dokta Tafida Abubakar Ila

9. Mutanen Abadam

Akalla fararen hula 50 ne mayakan Boko Haram suka bindige daga cikin ’yan Najeriya masu gudun hijira a garin Tumuk, Jamhuriyar Nijar.

Maharan sun yi ta harbin mutanen ne daga kurkusa suna kuma kona gidajensu a ranar Lahadi 13 ga watan Disamba, 2020.

Yawancin ’yan gudun hijirar sun fito ne daga Karamar Hukumar Abadam ta Jihar Borno inda ayyukan kungiyar suka sa su yin kaura zuwa Nijar.

10. Sarkin Kaura Namoda

Sarkin Kaura Namoda a Jihar Zamfara, wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Kaura Namoda, Ahmad Muhammad Asha, ya koma ga Mahaliccinsa a safiyar 3 ga watan Maya yana da shekara 71 bayan fama da ciwon suga da hawan jini na tsawon lokaci.

Tsohon darakta ne a sashen kudi na Kananan Hukumomin Kaura Namoda da Gusau da Maru kafin ya zama sarki a shekarar 2004.

11. Dan Iyan Zazzau Yusuf Ladan

Shi ma Alhaji Yusuf Ladan, Dan Iyan Zazzau, Allah Ya yi masa rasuwa bayan fama da rashin lafiya a gidansa da ke Kaduna safiyar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2020 yana da shekara 86 a duniya.

A lokacin rayuwarsa, Marigayi Alhaji Yusuf Ladan ya kasance fitaccen dan jarida, tsohon Manajan-Daraktan Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin na Jihar Kaduna (KSMC), kuma Hakimin Kabala.

Marigayi Alhaji Yusuf Ladan

12. Sarauniyar Kyau

Tsohuwar sarauniyar kyau a Najeriya Ibidun Ighodalo ta rasu a ranar Lahadi 14 ga watan Yuni.

Ibidun Igahodalo wadda ta shahara a fannin kasuwanci a Legas kuma take auren Babban Faston Cocin Tiriniti ta Legas ta rasu ne a garin Fatakwal babban birnin jihar Ribas sakamakon ciwon zuciya a lokacin da take barci.

Marigayiya Ibidun Ighodalo tsohuwar sarauniyar kyau

13. Maikanti Baru

A cikin shekarar tsohon Shugaban Kamfanin NNPC, Maikanti Kachalla Baru ya rasu yana da shekara 61.

Maikanti Baru ya rasu ne ranar Juma’a 29 ga watan Mayu  kuma ne Shugaban NNPC daga 2016 zuwa watan Yulin 2019 lokacin da ya mika ragamar kamfanin ga Mele Kyari mai ci a yanzu.

14. Wada Maida

Tsohon hadimin Shugaban Kasa, Malam Wada Maida ya koma ga Mahallicinsa a ranar Litinin 17 ga Agusta, 2020 a gidansa da ke Abuja.

Tsohon Babban Edita kuma Manajan Darakta ne na Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya (NAN) kuma shi ne kakakin Shugaba Buhari a lokacin mulkin soja.

Kafin rasuwarsa, shi ne mai gidan jaridar People’s Daily kuma daya da cikin ’yan Majalisar Daraktoci na Kamfanin Media Trust, masu buga jaridar Aminiya da Daily Trust.

Marigayi Malam Wada Maida

14. Sama’ila Isa Funtua

Daya daga cikin na hannun daman Shugaba Buhari, Malam Sama’ila Isa Funtua ya rasu sakamakon ciwon zuciya a ranar Litinin 20 ga Yuli da dare a Abuja.

Marigayi Sama’ila Funtua tsohon minista ne a Najeriya kuma tsohon shugaban Kungiyar Masu Gidajen Jaridu ta Najeriya (NPAN).

Dan jarida ne, dan kasuwa, sannan kwararre a fannin gudanarwa.

Marigayi Sama’ila Isa Funtua

16. Ministan Tsaro Domkat Bali

Tsohon Ministan Tsaron Najeriya, Janar Domkat Yah Bali ya sheka barzahu a ranar Juma’a 4 ga Disamba, bayan fama da rashin lafiya a garin Jos, Jiharsa ta Filato.

Shugaba Muhammadu Buhari a ta’aziyyarsa ga matar marigayin, Esther, ya jajanta wa ’yan uwa da makusanta dangane da wannan rashi.

Ya ce akidar ta kishin kasa da Janar Bali ya rika a rayuwarsa ta aikin soja za ta ci gaba da karfafa gwiwar sojoji masu tasowa kuma za a rika tunawa da irin hidimtawarsa ga kasar nan a fannoni daban-daban.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Abayomi Gabriel Olanisakin.

Buhari ya tura wata tawaga karkashin Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, domin zuwa ta’aziyya ga iyalan marigayi Bali da kuma Gwamnatin Jihar Filato dangane da rashin.

17. Janar Irefin

Babban Kwamandan Runduna ta 6 ta Sojin Kasa ta Najeriya da ke Fatakwal, Jihar Ribas, Manjo Janar Olu Irefin ya kwanta dama baya nkamuwa da cutar COVID-19.

Janar Olu Irefin, na halartar babban taron Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya na 2020 ne aka gano ya kamu da cutar.

Ranar Alhamis 10 ga Disamba Runduanr ta soke taron ta kuma killace mahalarta ciki har da Babban Hafsanta, Laftanar Tukur Buratai na tsawon kwana 14.

Sakamakon gwajin da aka yi wa mahalartar taron ya nuna janarori 18 na rundunar sun kamu da cutar.

18. Tsohon Shugaban NNPC Joseph Dawa

Kamfanin mai na NNPC ya sanar da rasuwar tsohon shugabansa na 16, Josehp Thlama Dawha ranar Litinin 3 ga Agusta da dare.

Shugaban NNPC, Mele Kolo Kyari ya bayyana mutuwar Joseph Dawah wanda rashin lafiya ta yi ajalinsa a matsayin babban rashi na shugaban da ya rike kamfanin  daga 2014 zuwa 2015.

19. Mahaifin Sheikh Albany Zariya

Rashin lafiya ya yi ajalin mahaifin sahararren malamin Musulunci marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya, wato malam Adam Danjuma Tela, da sanyin safiyar Laraba 18 ga watan Nuwamba.

Bayan rasuwar Malam Adam Tela sakamakon jinyar an yi masa sallar jana’izarsa a gidansa da ke unguwar Mucjiya, Sabon Garin Zariya.

20. Dan Sheikh Ja’afar

Shi ma fitaccen malamin Musulunci, marigayi Shekh Ja’afar Mahmud Adam, Allah Ya yi wa dansa Abdulmalik rasuwa.

Sheikh Gadon Kaya ya sanar cewa a ranar Asabar 10 ga Oktoba, 2020 ne Abdulmalik Sheikh Ja’far ya bakunci lahira sakamakon hatsarin mota.

Ministan Fasahar Tattalin Arziki na Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami na daga cikin wadadan suka sanar da rasuwar dan gidan shehin malamin a sakon ta’aziyar da ya wallafa ta shafinsa na Facebook.

“Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, dan Shaykh Ja’afar Mahmud Adam (RH).

“Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran ’yan uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan nasu”.

Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

21. Jakadan Najeriya a Birtaniya

Tsohon Jakadan Najeriya a kasashen Birtaniya, Amurka, da Switzerland, Adamu Muhammad ya rasu yana da shekara 83.

Ambasada Adamu ya rasu ne a ranar Alhamis 24 ga Disamba, 2020 da safe a Kaduna bayan ya yi fama da jinya.

Marigayin ya yi aiki da tsoffin shugabannin soja, sannan ya yi ritaya a lokacin tsohon Shugaba Abdulsalami Abubakar a matsayin Mashawarci a Kan Yaki Miyagun Kwayoyi da Laifukan da suka shafi Kudi.

Marigayi Adamu ya kasance jakadan Najeriya a Senegal sannan kuma ya yi aiki a Majalisar Dinkin Duniya.