Mace mafi tsufa a Jihar Sakkwato ta rasu tana da shekara 130
Wata mace da ake jin ita ce mafi yawan shekaru a Jihar Sakkwato mai suna Malama A’ishatu wadda aka fi sani da Muddu mai shekara 130 a duniya ta rasu.Marigayiya A’ishatu ta kwanta dama ne da maraicen Litinin da ta gabata, kamar yadda makusanciyarta, Hajiya Tuni da ke Unguwar Dandi a karamar Hukumar Sakkwato ta […]
Wata mace da ake jin ita ce mafi yawan shekaru a Jihar Sakkwato mai suna Malama A’ishatu wadda aka fi sani da Muddu mai shekara 130 a duniya ta rasu.
Marigayiya A’ishatu ta kwanta dama ne da maraicen Litinin da ta gabata, kamar yadda makusanciyarta, Hajiya Tuni da ke Unguwar Dandi a karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa ta bayyana, ta ce marigayiyar ta zo Sakkwato ne daga kauyen Alkammu da ke karamar Hukumar Wurno da ke jihar a 1951 a lokacin da ana fama da mawuyacin hali a Arewa.
Ta ce wahala ce ta taba su suka zo ne da mijinta Dabo da dan autanta daga cikin ’ya’ya 11 da ta haifa, kuma yanzu dan ne kawai ta bari a raye da sauran dangi na wajen dan.
Hajiya Tuni ta kara da cewa a lokacin da yunwa ta addabi mutane ne margayiyar da danta ta yanke shawarar yin sana’ar dako da gyarn gero da dawa, a kokarinta na tsayawa da kafafunta, wanda hakan ya sanya mutane ke son ta tare da girmama ta har ta bar duniya tana mace mai kamala.
Autanta Malam Usman dan Oro yanzu shi ma ya haura shekara 70 a duniya.
Jikanta Malam Aminu Usman mai shekara 45 ya ce yana da ’ya’ya 11 da jikkoki tara. “Dukkanmu muna zaune a kauye daya a karamar Hukumar Wamakko, abin burgewa ga kakata margayiya tana da shekara 130 amma ba ta manta abubuwan da suka faru can baya ba da wadanda ake ciki yanzu,” inji shi.
Wani dalibin tarihi Malam Akilu Shehu Yabo ya yi kira ga gwamnati ta rika ajiye kundin tarihin irin wadannan mutane don samun ilimi ga matasanmu kan al’amurran da suka faru a can baya.