Mace mai ilimi ta fi daraja- Hajiya Rabi Tahir
Hajiya Rabi Tahir ita ce Shugabar Kamfanin Harhada Magunguna na RATA da ke Jihar Borno. Kamfanin da ya shahara wajen sayar da magunguna, domin babu inda ba a sanshi ba a Jihar Borno. A zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda aka yi ta kafa wannan katafaren kamfani da fadi-tashin da ta sha a rayuwa da […]
Hajiya Rabi Tahir ita ce Shugabar Kamfanin Harhada Magunguna na RATA da ke Jihar Borno. Kamfanin da ya shahara wajen sayar da magunguna, domin babu inda ba a sanshi ba a Jihar Borno. A zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda aka yi ta kafa wannan katafaren kamfani da fadi-tashin da ta sha a rayuwa da nasarorin da ta samu da batutuwa da dama kamar haka:
Tarihinta:
Sunana Hajiya Rabi Tahir. Ni haifaffiyar Jihar Adamawa ce a karamar Hukumar Girie. Ni ce ‘ya ta fari a gidanmu amma mahaifana sun rasu. Sunan mahaifina Alkali Mu’azu Modibbo Girie, mahaifiyata kuma A’ishatu Mu’azu. Mahaifina ya haife mu mu ashirin amma yanzu mu goma sha tara muka rage saboda dayanmu ya rasu.
Na yi karatun frimare a Yola a lokacin ina zaune ne tare da Kakata. Bayan rasuwarta ne na koma wurin mahaifana. Sannan na yi karatun sakandare na Kwalejin gwamnati ta mata (G.G.C) Yola inda na kammala a shekarar1975.
Da na yi aure sai muka koma kasar Canada da zama kuma na kara wani karatun Kwaleji a can. Bayan mun dawo Najeriya ne sai na yi karatun Digiri inda n kammala a 1983 a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria (A.B.U), inda na karanci yadda ake hada magani (Pharmacy). Wannan shi ne dalilin da ya sa na tsunduma cikin harkar magani. Bayan na gama bautar kasa, na yi aikin gwamnati na tsawon watanni biyar sannan na bari na fara kasuwanci a 1987 a inda na bude kamfanin sayar da magani da ake kira RATA Pharmacy wanda fitaccen wajen sayar da magani ne yanzu haka a Maiduguri. Bayan abubuwan da suka faru a Borno na rashin tsaro da matsalar Boko Haram ne na koma gida Adamawa.
Dalilin da ya sa na karanci sarrafa magunguna:
Ni ’yar fari ce don haka mahaifina ya jawo ni a jiki sosai. A kullum yakan ce shi dai yana son sanya mu uku akan hanya. Domin in har ’yar fari da na biyu da uku suka gyaru, to sauran ma za su yi koyi da su. Kuma yana son karatu sosai. Duk da na san zan yi karatu amma ban yi tsammanin zan karanci sarrafa magunguna ba. Da na dawo daga Kanada sai Jami’a ta ce ba za ta dauke ni da sakamakon karatun da na yi a kasar waje ba don haka sai na sake yin sabon karatu. Hakan ta sa na sayi sabon takardar neman shiga Jami’a (Form). To akwai wani dan ajinmu marigayi Ahmed Dikku shi ya ba ni shawarar in karanta fannin harhada magunguna a lokacin da nake cike fom dina. Cikin ikon Allah sai na samu nasarar samun gurbi a sashen harhada magunguna a Jami’a. Kin ji yadda aka yi na tsinci kaina a wannan fanni.
Wanda na fi shakuwa a tsakanin iyayena:
A gaskiya na fi shakuwa da mahaifina fiye da mahaifiyata domin a wancan zamanin akwai wata al’ada da ake yi cewa ’yar fari ba zai zauna kusa da mahaifiyarsa ba. Ni kuma na tsinci kaina a irin wannan hali. Mahaifiyata ba ta taba kiran sunana ba har Allah Ya dauki ranta. Don haka sai mahaifina ya ja ni a jiki. Hakan ba ya nuna ba na son mahaifiyata ba ne, amma dai na fi shakuta da mahaifina fiye da ita.
Abin da ya faru da ni ina karama wanda bazan taba mantawa da shi ba:
Akwai wata rana muna sakandare sai muka saci hanya muka je auren ’yar malamarmu. Da mahaifina ya samu labari sai ya sa aka zane mu. Wannan abu ba zan taba mantawa da shi ba. Kuma tun ranar ba mu sake ba.
Halayen da na gada daga iyayena:
Ni dai abin da nake ji ake fada shi ne, hakurin da nake da shi a wajen mahaifina na koya. Domin ba ni da saurin fushi har sai abu ya munana. Hakan dai nake ji ake fadi. Mahaifiyata kuma mace ce mai kamanta gaskiya. Domin akwai ‘ya’ya da yawa a gidanmu an ba ta wannan shedar. Haka kuma nake ji ake cewa idan an zo gidana sai a ce ina kamantawa kamar mahaifiyata.
Yadda na hadu da maigidana:
Ana gobe za mu yi hutun makarantar sakandare sai na kamu da zazzabi sai aka kai ni asibiti. Ya taba aure kafin ya aure ni amma a lokacin Allah Ya yi wa matarsa rasuwa. Kuma yana da ‘ya’ya uku kuma an dame shi ya yi aure domin wadannan ‘ya’yan nasa. Sai rannan ya je Yola wajen Baffansa ya ce an dame shi ya yi aure amma bai ga macen da ta kwanta masa a rai ba. Sai baffansa ya ce “akwai wata yarinya Rabi Modibbo domin akwai wani dan uwanka da yaje yace yana so an hana shi amma da dalili. Ka je ka duba ko za ka taki sa’a”. Sai ya je asibitin da nake ya nema mu gaisa. Yayarsa t ace da ni dan uwanta na so mu gaisa. Sai ya ce tunda za mu yi hutu gobe, zai zo ya mayar da ni Girie sai nace masa to. Washegari sai nay i sammako na koma gida. Da ya zo bai same ni ba. Da ya samu labarin na koma gida sai ya dauki ‘yar uwarsa suka same ni a Girie. Ya ce da ni shi ba hira ya kawo shi ba. Aurena yake son yi. Sai ya tambaya ko ina so sai na ki yin magana. Sai ya yi shiru na wadansu mintoci daga nan ya ce zai tafi sai na ce masa in ya je wajen iyayena kada ya ce ya taba ganina. Daga baya yake gaya min cewa wannan maganar da nayi ne ya sa ya gane cewa ina so. Ni kuma ban san na fada ba. Sannan aka yi mana aure. Na haifar masa ‘ya’ya uku kuma na tadda yaransa uku muna da ‘ya’ya shida dai a yanzu haka. Kuma duk a hannuna yaran suka girma. Kuma yarana ba su san cewa ba ni na haifi yayyinsu ba sai da suka sami labari a wajen wasu.
Yadda nake kula da gida da kuma aiki:
Na dan sha wahala a lokacin da nake makaranta musamman a wajen kula da gida da miji da kuma yara. Kuma abin da nake karanta wa ba na ragwaye ba ne. Amma maigidana ya yi hakuri da ni a wadannan lokutan domin ba ya cin abinci da wuri har sai na dawo. Allah da ikonSa har na gama. Bayan na kammala bautar kasa ne na dan yi aikin watanni biyar a asibitin Jami’ar Maiduguri (UMTH) sannan na bude shagon sayar da magani Kemis (Chemist). Aikin asibiti nada wahala domin ko cikin dare aka kira ni sai na je kuma sai ya raka ni, dalilin da ya sa na bar aikin kenan. Da na bude kemis ne abubuwa suka yi mana sauki domin na san lokacin da zai koma gida don haka kafin ya koma sai na yi maza-maza na koma gida don yi mana abinci da sauran dawainiyar gida.
’Ya’yana:
Ina da ya’ya shida daga cikinsu akwai Chubado Tahir wadda ya kware wajen yin fida da Zainab Tahir wadda take aiki a sashen harhada magunguna na asibitin Jami’ar Maiduguri UMTH da Fatima Tahir, Uwargidan Ambasadan Najeriya da ke Saudiyya da Salahuddeen wadda yake Injiniya ne a kamfanin tatar man feturNNPC da Misbahuddeen Tahir na Kamfanin fensho na Sigma Pension da kuma Dokta Lubabatu Tahir Bawuro wadda take aiki a kamfanin NNPC da ke Kaduna. Kuma mun shaku da su matuka gaya.
Sirrin zaman aure:
Abu na farko dai shi ne soyayya amma kuma ba soyayyar waje ba. Soyayyar cikin gidan aure. Abu na biyu kuma sai da hakuri domin ko da iyaye ne ake zaune wata ran dole a saba. Domin zo mu zauna, zo mu saba ne. Allah Ya halicce mu, iyaye sun haife mu kuma
miji shi ne wanda zai ba ka wajen kwanciya da sutura da abinci, dole ne a girmama shi. Ko mun saba nakan yi kokarin in ga mun shirya. Kuma ban daga murya ta a bisa tasa, wannan shi ne girmamawa. Na yi sa’a tunda yakan shawarce ni a duk abin da zai yi. Amma a karshe dai abin da ya fadi shi muke amfani da shi. Saboda haka hakuri da girmamawa da juriya da kuma soyayya shi ne sirrin zaman aure.
kalubale:
Alhamdulillahi! Duk da yake na kasance mace babu wani abu da zan sa a gaba wanda ba zan cimma burina ba. Domin mahaifina ya ba ni tarbiyyar kasancewa tamkar da namiji wajen tashi tsaye in nema. Domin a lokacin da yake raye ko me ya faru a cikin gidanmu sai ya nemi shawarata kafin ta kowa. Akwai kanina Adamu Modibbo shi yake bi na, duk abin da na fada shi yake yi. Don haka tun farko na dauki kaina tamkar namiji, domin duk abin da namiji zai iya yi ni ma zan yi. Alhamdulillah ba ni da wani kalubale a rayuwa.
Inda nafi sha’awar zuwa hutu:
Akwai kasashe da dama da na zauna amma na fi sha’awar ziyartar Dubai. Domin suna da duk abin da za ka tarar a kasar turawa amma hankalina ya fi kwanciya a wannan kasar. Amma ina ganin don musuluncinsu ne domin wata zata iya ce maka ‘assalamu alaikum’ da sauransu.
Turaren da nafi sha’awa:
Este lauder domin maigidana ya taba ba ni kyautarsa.
Macen da ta fi burge ni:
Ina sha’awar mace mai neman na kanta, mai kwazo da hazaka da kima da kuma addini. Hasalima al’umma sun fi sha’awar macen da ta yi ilimi fiye da jahila.
Kwalliya:
Ba na daura zane sai mai sheki. Kuma ban cika daura atamfar Super ba domin na lura mata da yawa ita suka fi daurawa saboda alfahari. Na fi son daura atamfarmu ta Najeriya domin ta fi min kyau. Mace ta zama mai tsafta da kuma sanya kayan da ba zai takurata ba.
Abin da nake a rika tunawa da ni a kai:
Kamar yadda na fada a baya cewa na bude gidan sayar da a Maiduguri tun 1987 har ila yau, ina son a tuna da ni a matsayin matar da ta taimaka wajen yaki da shan miyagun kwayoyi. Akwai matasa da dama wanda muka taimaka masu wajen warkar da su daga yawan shan kwayoyi da kuma hana wadanda suke shansa ba tare da wani dalili ba. Akwai daya daga cikin irin wadannan matasa da na warkar wanda ya shiryu har ya yi karatun digiri a Jami’a, wasu kuma da na warkar sun rungumi harkar kasuwanci. Akwai almajiran da nake daukar nauyinsu tun suna kanana har su girma su mallaki hankalinsu. Kamar dai yadda nake tallafawa gajiyayyu a Maiduguri haka nake fata na yi a Jihar Adamawa don a rika tunawa da ni a irin wannan abubuwan alherin da na yi.