Mace mai ilimi ta fi namiji taimakon iyaye – Misis Adaline Patari

  Mis Adaline Waye Patari, Jinkan Kalaku ta Lapan ’yar jarida ce kuma gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati da ta fara aiki daga karamar ma’aikaciya har ta kai Mukaddashiyar Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) a Jihar Gombe, a zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da wasu al’amura da suka shafe ta:   Tarihin […]

Mace mai ilimi ta fi namiji taimakon iyaye – Misis Adaline Patari

 

Mis Adaline Waye Patari, Jinkan Kalaku ta Lapan ’yar jarida ce kuma gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati da ta fara aiki daga karamar ma’aikaciya har ta kai Mukaddashiyar Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) a Jihar Gombe, a zantawarta da Aminiya ta bayyana tarihinta da wasu al’amura da suka shafe ta:

 

Tarihin rayuwata

Sunana Adaline Waye Patari, ni Batangaliya ce ta Kaltungo an haife ni a garin Kaltungo a Jihar Gombe. Na  yi firamaren Nasawara da ke garin Kaltungo. Sai Kwalejin ’Yan mata ta Tarayya  (FGGC) da ke Bauchi, daga nan sai na tafi Jami’ar Maiduguri na gama a 1992. Na yi hidimar kasa (NYSC) a Jihar Imo. Bayan nan na yi Diploma a Cibiyar ’Yan jarida ta Kasa (IIJ) a tsangayarta ta Bauchi,  yanzu haka ina Digiri na biyu a Jami’a Jihar Gombe (GSU).

Aiki

Na fara aiki a kamfanin buga jaridar Trumpeter da ke Jihar Bauçhi a 1996 a matsayin wakiliya zuwa 1998. Daga 1998 na koma aiki da Hukumar Wayar da kan Jama’a ta Kasa (NOA) inda na fara da mukamin Jami’ar Watsa Labarai (PRO) har zuwa yanzu da nake rikon Daraktan Hukumar.

 

Kalubale

A matsayina ta mace maza suna ganin  idan ke mace ce ba ki iya ba, su suka iya sannan wadansu mazan ba su son a ce mace tana shugabantarsu hakan yana zama kalubale ga mata da suke jin a wani lokaci aikin ya fita a kansu.

 

Nasara

Na gode wa Allah na samu nasara domin na fara aiki ne daga karamar ma’aikaciya har na kai matakin Daraktan Riko ta Hukumar NOA, a nan  Jihar Gombe. Sannan aikina ya sa na san manyan mutane wadanda idan ba don aikin ba da ban isa zuwa kusa da inda suke ba.

 

Tufafin da suke burge ni

Na fi sha’awar sanya doguwar riga in yafa gyale sannan in yi fita irin ta mata masu kamala na ’yan Arewa inda duk wanda ya gan ni ya ga mace tagari mai mutunci.

 

Burina a rayuwa

Burina a rayuwa shi ne idan na gama aikin gwamnati in bude gidan gona da zan rika noma da kiwon dabbobi, domin suna debe mini kewa, sannan in samu dama ina taimaka wa marasa galihu.

 

Wakar da na fi so

Wakar coci ce ta Korus

 

Abincin da na fi so

Na fi sha’awar tuwon masara da miyar taushe da sauran abinci irin na gargajiya.

 

Hutu

Ba na zuwa hutu ko’ina a kauye nake hutuna tare da ’yan uwa da sauran dangi. Ba na zuwa kowane gari bare wata kasa, a nan garinmu cikin al’ummata nake yin hutuna.

 

Kungiyoyi

Ni mamba ce a Cibiyar Kwararrun Jami’an Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR),  kuma mamba a Kungiyar Ci gaban Al’ummar Tangale ta Gabas (Tangale East Debelopment Association) da kuma Kungiyar Auptra.

 

Kasashen da na je

Na je Jerusalem da Kwatono da Nijar.

 

Sarauta

Ni ce Jinkan Kalaku Lapan.

 

Shawara ga mata

A matsayina na ’ya mace ina bai wa iyaye shawarar cewa su rika sa ’ya’yansu mata a makaranta don yin ilimin zamani. Saboda zai taimaka musu wajen zaman gidan aure. Idan yarinya ba ta yi ilimi ba babu yadda za a yi ta iya yi wa ’ya’yanta tarbiyya irin wacce ake so. Domin duk wata tarbiyya daga gida takan faro. Har ila yau auren wuri ga yara ba daidai ba ne domin jikinsu bai yi kwari ba wajen haihuwa, sai ka ga yarinya ta bude ta kamu da wata cuta musamman ciwon yoyon fitsari. Sannan idan mace ta yi karatu tafi namiji tausayi wajen taimakon iyaye domin duk wani abu da za a yi a gida za ta ba da gudunmawa daidai gwargwado shi kuwa namiji daga shi sai iyalansa.

Haka talla ga ’ya’ya mata ba alheri ba ne, domin wajen talla tarbiyyar ’ya mace kan fara lalacewa domin takan hadu da mazan banza da suke koya musu maganganun batsa tun yarinya ba ta son ji har ta fara jurewa daga nan a kai matakin da da za a yi fara sa hannu a jikinta har ta kai ga in ba Allah Ya kiyaye ba ta yi abin kunya a ciki a layi. Allah Ya sauwake iyaye a kula.