Mace mai nauyin kilogiram 25 kacal tana ƙoƙarin rage ƙiba

Matashiyar ba ta damu da suka da cece-kucen da mutane ke yi a kanta a kafafen sada zumunta ba.

Mace mai nauyin kilogiram 25 kacal tana ƙoƙarin rage ƙiba

Wata budurwa ’yar ƙasar China, mai nauyin kilogiram 25 kacal, ta ƙudiri aniyar rage nauyinta, don sake zama siririya.

Budurwar mai suna da ‘Baby Tingzi’ wanda tsayinta ya kai sentimita 160 amma tana da nauyin kilogiram 25 kacal kuma da alama tana da niyyar rage ƙibarta.

Tana da magoya baya sama da 42,000 a kafar sada zumunta ta zamani ta Douyin, nau’in manhajar TikTok na China, waɗanda galibinsu ke nuna damuwa game da yanayin lafiyarta.

Baby Tingzi kodayaushe tana cewa ta fi son zama siririya, inda ta kara da cewa tana son sirantaka kuma hakan ba shi da wani mummunan tasiri a rayuwarta.

Budurwar wacce ta shahara kan abin da ta ke ƙauna a kafofin sada zumunta, ta fito ne daga garin Guangzhou, lardin Guangdong na ƙasar China.

A koyaushe tana sanya faifan bidiyo nata sanye da kayan kwalliya don nuna sirantakarta da yanayin jikinta kuma da alama ba ta damu da sukar jama’a ba.

A galibin bidiyonta, Baby Tinzi tana yin rawa a gaban kyamara kuma ta fito cikin kayan kwalliya, tana nuna siraran kafafunta da hannayenta.

Amma kuma takan auna nauyinta a-kai-a-kai don bayyana wa magoya bayanta nauyinta game da yadda take son rage nauyi da ƙiba.

Bayan da bidiyon Baby Tinzi ya yi ta yaɗuwa a shafukan sada zumunta na ƙasar China, da dama sun yi tsokaci cewa, mai yiwuwa ta kamu da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ne.

Idan suka ce tana buƙatar agajin gaggawa, har ma wasu sun yi mata laƙabi da ƙwarangwal na tafiya ko rawa.

“Yana da wuya a yi tunanin wani babba mai nauyin kilogiram 25,” wani mutum ya rubuta.

Wani ya ƙara da cewa, “Gaskiya ina tsoron kar ki mutu a lokacin da nake kallon wayata,” a cewar wani.