Mace mai wuyar sha’ani a soyayya

Yawan fara’a bai dame ta ba idan kuna tare, amman idan wata a cikin kawayenta ta yi mata maganarka, na take fuskarta ke cika da annuri

Mace mai wuyar sha’ani a soyayya

Wadansu ’yan matan na da wuyan sha’ani! Tana son ka, amman duk rintsi ba za ta iya furta maka tana son ka ba, koda kuwa a rubuce ne; idan kuma ka yi mata kalaman soyayya da ta ji dadinsu, amsar ba ta wuce ta ce, ‘na gode’.

Tana damuwa idan ba ka kirata a waya ba, amman duk damuwar da za ta yi ba za ta dauki wayarta ta ce ita bari ta kira ka ba, dole sai dai idan kai ne ka kira ta tukunna.

Yawan fara’a bai dame ta ba idan kuna tare, amman idan wata a cikin kawayenta ta yi mata maganarka, yanzu za ka ga fuskarta ta cika da annuri.

Saboda tsananin zurfin cikinta, ta fi karfin ta baka hakuri idan tayi maka laifi, saidai ka yi fushin ka gama, ka sauko don kanka, sannan ka dawo gareta ku ci gaba daga inda kuka tsaya.

A zuciyar ta tana son ta ba ka hakurin, amman ba za ta iya ba, [saboda tana tunanin cewa] hakan kamar zubewar kima ce a gareta — [Don haka]  a wasu lokutan ma ba za ta yarda ta yi maka laifin ba.

Idan za ka yi shekara ba ka je gidansu ba, ba za ta tambaye ka yaushe za ka je ba? Sai dai kai don kanka ka ce mata za ka zo rana kaza, idan ta ga dama ta ce maka ranar ba ta nan.

Dole kai ne za ka bukaci tura iyayenka gidansu domin a yi maganar aure, shi ma sai kun yi fama kafin ta yarda ka tura din, amman ita da kanta ba za ta taba cewa ka turo ba.

Irin wadannan ’yan matan na da yawan gaske a wannan zamanin, duk wanda Allah Ya hada shi soyayya da irinsu, tabbas sai ya kasance mai tsananin hakuri da juriya, domin duk yadda ka so canza su, ba za su taba canzuwa ba, saboda halittarsu ce a haka.

Idan kuwa Allah Ya kaddara rabuwarka da su kafin aure, a nan suke shiga mawuyacin halin da babu wadanda ke sani sai na kusa da su.

A sannan suke gane girman soyayya da suke maka, a lokacin suke kuka tare da zubda hawayen rashinka da suka yi.

A lokacin suke jin ina ma ka dawo gare su domin su nuna maka kulawa da soyayyar da suka kasa baka a baya.

Sai dai kash! Bakin alkalami ya riga da ya bushe!

Shin ka taba hauwa da irin wannan macen?

 

Daga Ishaq Umar Darazo

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025