Mace Manjo-Janar ta farko a Najeriya ta rasu
Macen da ta fara kaiwa matsayin Manjo-Janar a rundunar sojin Najeriya, da ma yankin Afirka ta Yamma, Aderonke Kale ta rasu tana da shekaru 84
Macen da ta fara kaiwa matsayin Manjo-Janar a rundunar sojin Najeriya, da ma yankin Afirka ta Yamma, ta kwanta dama.
Manjo-Janar Aderonke Kale (murabus), wacce ita ce mace ta farko da ta zama kwamandar asibitin soji a Najeriya ta rasu ne a ranar Laraba tana da shekaru 84.
- EFCC ta cafke garin kudi na N11m a hannun masu sayen kuri’u
- Duk wadanda muke bi bashi sai sun biya — MTN
Kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu ya ruwaito babban hafsan rundunar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja na bayyana kaduwa da rasuwar Manjo-Janar Aderonke.
Laftanar-Janar Lagbaja ya bayyana rasuwar Manjo-Janar Aderonke Kale a matsayin babban rashi ga Najeriya da ma duniyar aikin soji, inda ya bayyana yadda ta sadaukar da kanta wajen hidimta wa bil Adama, wanda ba za a taba mantawa ba.