Mace Musulma furen Musulunci
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake da cikakkiyar siffa, wacce ba ta da tawaya ko kadan kuma har abada, Ya bayyana falalarSa ga mata da maza, kuma Ya shar’anta wa mace da ta gyara kanta da hijabi domin ta zama abin koyi wajen ladabi da kyan hali, kuma don ta kange maza game da […]
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Yake da cikakkiyar siffa, wacce ba ta da tawaya ko kadan kuma har abada, Ya bayyana falalarSa ga mata da maza, kuma Ya shar’anta wa mace da ta gyara kanta da hijabi domin ta zama abin koyi wajen ladabi da kyan hali, kuma don ta kange maza game da kallon tsiraicinta, ta yadda hakan zai sa kowa ya wayi gari cikin kyan hali. Tsira da Amincin Allah su tabbata bisa ga ManzonSa, wanda ya ce ku zauna da mata da kyakkyawar kulawa. Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku kare kanku da iyalinku daga wata wuta makamashinta mutane ne da duwatsu…”
Duk wanda ya yi riko da wasiyyar Manzo (SAW) wajen yin mu’amala da mace kamar yadda ake yin mu’amala da zinari ko azurfa, tsararriya wacce ba don komai ake tsare da su ba face don kyansu da tsadarsu (ya rabauta). Kuma kada ku yi mu’amala da ita kamar yadda kuke mu’amala da abu mai araha wanda ake samu koyaushe, wanda kuma kowa na iya samunsa duk lokacin da yake bukata. Kuma kada mu so ta zama kamar ’yar wuta, domin Manzon Allah (SAW) yana cewa “Akwai wadansu mutane, har yanzu ban gan su ba,” daga cikinsu sai ya ambaci wadansu mata wadanda in ka gan su za ka ga da kaya a jikinsu amma dai tsirara suke, karkatattu ne game da yi wa Allah biyayya, kuma masu karkatar da wasunsu ne game da bin hanyar Allah, kawunansu kai ka ce tozon rakumi ne wanda yake a karkace, Manzon Allah ya ce ba za su shiga Aljanna ba, kuma ma ba za su ji kanshin Aljannar ba.”
Ya ke ’yar uwata Musulma! Lallai abin da ake nufi da mace mai bayyana tsiraici ita ce wacce take sanya tufafi matsattsu, ko masu shara-shara ko budaddu ko gajeru ko wadda ke barin gashinta a bude kowa na gani da makamancin haka.
Amma wacce take mumina ta gaske, tsarkakarkiya, wacce take son tsarkin zuciya da kuma kamun kai, wacce ba ta yarda da abin da na ambata a baya ba sakamakonta shi ne Aljanna kamar yadda Annabi (SAW) ya ce: “Idan mace ta yi salloli biyar, kuma ta yi azumin watan Ramadan, ta kiyaye farjinta, ma’ana ta kange al’aurarta game da bayyana tsiraici da fitinuwar mutane da ita, kuma ta yi wa mijinta biyayya, za a ce da ita: “Ki shiga aljanna ta kowace kofa kike so.”
A karshe ya ke ’yar uwa mai karamci! Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Ka sanar da bayiNa, lallai Ni Mai yafewa ne kuma Mai jinkai, kuma lallai azabaTa ita ce azaba mai radadi.”
Idan kina son hanyar yafiyar Ubangiji, to ki riki sharuddan hijabi da shari’ar Musulunci ta yarda da su kamar haka:
1. Ya zamo hijabin ya rufe jiki baki daya 2. Kada hijabin ya zama ado a karan kansa 3. Ya zamo mai duhu ne ba mai shara-shara ba 4. Ya zama yalwatacce ba matsattse ba 5. Kada ya yi kama da kayan maza 6. Kuma kada ya yi kama da kayan kafirai 7. Kada kuma ki sa turare in za ki fita, domin Manzon rahama (SAW) yana cewa duk macen da ta shafa turare sannan ta fita ta wuce wadansu mutane domin su ji kanshin da take dauke da shi na turare, to ita mazinaciya ce 8. Kuma kada ki yi domin ya zama ado. Ya ’yar uwa furen Musulunci!
Sadiya ta rubuto ne daga Kano