‘Mace Mutum’ ta kaddamar da littattafai don bunkasa Adabi
kungiyar marubuta ta mata zalla mai suna ‘Mace Mutum’, ta yi taron kaddamar da litattafanta 4 a ranar Lahadin da ta gabata.Littattafan 4 wadanda aka kaddamar a zauren taro na Gidan Mumbayya da ke Kano, kungiyar ta ce ta wallafa su ne bisa hadin gwiwa da karo-karo na rubutun ’ya’yanta.Na farko daga cikin littattafan mai […]
kungiyar marubuta ta mata zalla mai suna ‘Mace Mutum’, ta yi taron kaddamar da litattafanta 4 a ranar Lahadin da ta gabata.
Littattafan 4 wadanda aka kaddamar a zauren taro na Gidan Mumbayya da ke Kano, kungiyar ta ce ta wallafa su ne bisa hadin gwiwa da karo-karo na rubutun ’ya’yanta.
Na farko daga cikin littattafan mai suna ‘Hannu da Yawa’ ya kunshi gajerun kagaggun labarai ne, wadanda ’yan kungiyar suka harhada rubuce-rubucensu waje guda. Sauran littattafai ukun kuwa sun kunshi tatsuniyoyi ne, inda littafi na biyu da na uku suke dauke da tatsuniyoyi tara-tara kowane, littafi na hudu kuma yana dauke da tatsuniyoyi 14.
Farfesa Abdallah Uba Adamu ne ya yi sharhin littattafan, ya bayyana asalin tatsuniya tare da tasirinta ga Hausawa da kuma darasi da tarbiyyar da take koya wa ’ya’yan Hausawa.
Ya ce daga littattafan tatsuniyoyi na marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da na Dokta Bukar Usman babu wani littafin da aka samu na tatsuniya kamar wadannan.
Jami’in shirye-shiryen wallafawa da kaddamar da littafin, Malam Rabiu Abu-Hidaya, ya bayyana wa Aminiya cewa, an kafa kungiyar Mace Mutum a ranar 3 ga Maris na shekarar 2013, kuma manufofinta sun hada da farfadowa da kuma tsaftace Adabi tare da ciyar da shi gaba.
Shugabar kungiyar ta Mace Mutum, Hajiya Rahma Abdulmajid ta ce sun wallafa littattafan ne don habaka Adabin Hausa, kuma labarun da ke cikin littafi na farko sun kunshi jigogi a kan abubuwan da ke addabar jama’a kamar fyade da bara da shaye-shayen kayan maye da kuma harkar daba da banga.
Dokta Aliyu Modibbo daya daga cikin wadanda suka kaddamar da littattafan ya sayi littattafan a kan kudi Naira dubu 250, shi kuma Alhaji Abdullahi Umar Tsauri (Tata Jikan Shehu), ya saya a kan Naira Miliyan biyu da rabi.
Hajiya Rabi Tanko Yakasai ce ta wakilici matar mataimakin shugaban kasa Hajiya Amina Namadi Sambo.