Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda
Hauwa ita ce mace ta faro da ta taɓa zama Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Kano.
’Yar Jihar Kano, Hauwa Ibrahim Jibrin, ta kafa tarihin samum ƙarin girma zuwa muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda, wanda ba a taba samun ’yar Arewa da ta kai wannan matsayi ba a tarihin Najeriya.
Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya (PSC) ta yi wa Hauwa Ibrahim Jibrin karin girma ne tare da wasu manyan jami’an ’yan sanda 27, daga muƙamin Mataimakin Sufeto Janar (AIG) zuwa muƙamin Kwamishinan ’Yan Sanda.
- Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Rajab
- A biya mutanen da jirgin soji ya kai wa hari a Sakkwato diyya —PDP
Wannan ƙarin girma ya ba ta damar zama mace ta farko daga Arewacin Najeriya da ta kai wannan matsayi na Kwamishinan ’Yan Sanda.
Kafin ƙarin girman nata, ita ce Mataimakiyar Kwamishinan ’Yan Sanda mai kula da harkokin gudanarwa a Rundunar ’Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya, Abuja.
An haifi Hauwa Ibrahim Jibrin ranar 28 ga watan Oktoba, 1972, a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano.
Ta yi digiri na farko a Ilimin Siyasa, digiri na biyu a fannin Tsaro da Nazarin Dabaru. A halin yanzukuma tana karatun digirin digirgir (Ph.D).
Hukumar PSC, ƙarƙashin jagorancin Hashimu Argungu, ta ƙirƙiro jarabawa don tabbatar da ƙwarewar jami’ai kafin a ƙara musu girma.
Argungu, ya jaddada muhimmancin bunƙasa basirar ’yan sanda, musamman a fannin fasahar zamani.
Karin girman Hauwa ya nuna nagartar aikinta, wanda PSC ke maraba da ƙwararrun jami’ai a rundunar ’yan sanda.