Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia
Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri’un da aka kaɗa.

A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci.
Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale.
- Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
- Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira
“Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zama kyakkyawan misali,” kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. “Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: ‘saboda ni mace ce!'”
Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba inda ta lashe kashi 58% na ƙuri’un da aka kaɗa.
Nandi-Ndaitwah ta kasance daɗaɗɗiyar ƴar jam’iyyar South West Africa People’s Organisation (Swapo) – wadda take kan mulki tun lokacin da ƙasar ta samu ƴancin kai a shekarar 1990, bayan kwashe tsawon lokaci tana fafutukar ƙwatar kanta daga Afirka ta Kudu mai fama da mulkin wariya.