Mace ta kada mijinta a zabe a Amurka

Galibin ma’aurata sukan dan yi gasa cikin annashuwa, amma ga Dabid Johnson da matarsa Jennifer Johnson gasar tasu ta kai wani munzali da ba saba gani ba, inda suka fafata a zabe a jam’iyyu daban-daban. Zaben wanda kan takara ce a yankin Waterbille da ke Maine, ma’auratan sun fara fafatawa ne a farkon bana, inda […]

Mace ta kada mijinta a zabe a Amurka

Jennifer Johnson tare da mijinta David da ta kayar a zabe a garin Maine ta Amurka a ranar Talatar makon jiyaGalibin ma’aurata sukan dan yi gasa cikin annashuwa, amma ga Dabid Johnson da matarsa Jennifer Johnson gasar tasu ta kai wani munzali da ba saba gani ba, inda suka fafata a zabe a jam’iyyu daban-daban.

Zaben wanda kan takara ce a yankin Waterbille da ke Maine, ma’auratan sun fara fafatawa ne a farkon bana, inda Jennifer ta halarci wani taron masu fada a ji na Jam’iyyar Democrat kuma ta gano ba wanda ya fito takara a yankin nasu karkashin jam’iyyar.
Jennifer, mai shekara 36 matar kulle tana kaunar yadda Jam’iyyar Democrat ke gudanar da ayyukanta, kuma ta tsani a kyale dan takara ya tsaya zabe ba hamayya domin haka sai ta ba da sunanta don yin takarar.
“Babu wanda yake jin dadin yadda al’amura suke tafiya a gwamnati,” ta shaida wa TODAY.com, “amma a ce an rasa yin wani abu a kai abu ne da ke damuna,” inji ta.
Mijinta dan Jam’iyyar Republican wanda shi ma ke da dabi’ar mutum ya sauke nauyin da ke kansa, kamar da wasa sai ya ce zai tsaya takara da matar tasa. Dabid mai shekara 33 shi kadai ya fito takara a yankin a lokacin taron masu fada a ji na jam’iyyarsa.
Jennifer ta ce “Mun fara takara da juna kamar abin wasa.” Ta ce ta dauka Dabid ne zai lashe zaben saboda kasancewarsa namiji, amma maimakon haka sai ta kayar da shi, saboda jam’iyyar da take ciki.
Obama ne ya lashe kashi 65 na kuri’un da aka kada a yankinsu a zaben bara, don haka mijin ya zaci ta fi shi kwarjini a matsayinta ta ’yar takarar Jam’iyyar Democrat.
A zaben na ranar Talatar makon jiya Jennifer ta doke mijinta da kuri’a 127 inda shi kuma ya samu kuri’a 76. Suna zaune a kan kujera a gidansu sai aka kira tat a waya aka shaida mata nasarar da ta samu, ita kuma sai tad aka-tsalle ta ce, “Na ci zaben,” ta ce ta haka bayyana labarin ga mijinta. “Kuma ina jin wannan ne jawabina na samun nasara,” inji ta.
Ko me Dabid ya ce a lokacin, cewa ya yi: “Ina taya ki murna. Ina farin cikin wanda na zaba ne ya samu nasara.”
Iyalan wadanda suke da kananan ’ya’ya uku, suna iya zama abin misali ga sauran zababbun shugabanni ta kasancewa masu bambancin jam’iyya da suke auren juna. Ma’auratan dai an ce sukan tattauna al’amuran siyasa tare tare da mayar da hankali a kan inda ra’ayinsu ya zo daya, sannan Jennifer takan nemi shawarar mijinta Dabid kan hanyar da ta fi dacewa wajen hulda da ’yan jam’iyyarsa ta Republican.