Mace ta maka Nuhu Ribadu da kasa a zaben fidda gwanin APC a Adamawa
Sanata Binani ta maka Nuhu Ribadu da kasa da tsohon Gwamnan Jihar da kasa
Sanata Aishatu Binani
Sanata mai wakiltar Adamawa ta Tsakiya, Aishatu Dahiru Ahmed Binani, ta maka tsohon Shugaban EFCC, Nuhu Ribadu, da kasa a zaben fidda gwani na Gwamna a jam’iyar APC a Jihar Adamawa.
Binani ta samu kuri’a 430, yayin da Nuhu Ribadu ya samu kuri’a 288.
- Dikko Umar Radda da Yakubu Lado ne ’yan takarar Gwamnan APC da PDP a Katsina
- Mai neman takarar Shugaban Kasa a NNPP ya janye wa Kwankwaso
Hakan dai na nufin Binanin ce za ta yi wa jam’iyyar ta APC takarar Gwamna a Jihar a zaben shekarar 2023 mai zuwa.
Muhammad Jibirilla Bindow, tsohon Gwamnan Jihar ya zo na uku da kuri’a 103 yayin da Abdulrazak Namdas ya zo a matsayi na hudu da kuri’a 94.
Kazalika Umar Mustapha Madawaki da Wafarniyi Theman sun zo a matsayi na biyar da na shida a zaben fidda gwanin da aka gudanar a ranar Alhamis a Jihar.