Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da nakiya ta fashe a Neja

Nakiyar ta fashe ne sakamakon ɓoye ta da wani mutum ya yi domin amfani da ita wajen haƙar ma’adanai.

Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da nakiya ta fashe a Neja

Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon fashewar wata nakiya da wani mutum ya ɓoye a wajen domin aikin haƙar ma’adinai.

Lamarin ya yi sanadin lalacewar gidaje kusan 12 a yankin, inda ya jefa al’umma cikin tashin hankali.

Fatima Sadauki ta rasa ranta a wannan mummunan iftila’i, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kainji don duba lafiyarsu.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Shawulu Danmamman, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin, tare da tura tawagar ƙwararru zuwa wajen domin yin nazari.

Kakakin ya ce mutumin da ya adana nakiyar ya tsere, wanda rundunar ke ci gaba da nemansa.

Rundunar ta tabbatar da daidatar zaman lafiya a yankin, inda ta ce tana ci gaba da sanya ido don hana faruwar irin wannan lamari a gaba.