Mace ta yi kashin fasassun kwalabe a Kalaba
Ta ce ta yi kashin ne bayan ta sha wani ruwan mu’ujiza
A wani yanayi mai matukar daure kai, wata mata mai matsakaitan shekaru mai suna Nkechi Blessing Nwobodo, ta yi kashin wasu fasassun kwalabe a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.
Nkechi, kamar yadda wakilinmu ya samu labari na zaune ne a garin Ifo da ke jihar Ogun.
- Ba mu da shirin kara farashin man fetur a kwanan nan – NNPCL
- An kashe dakaru 100 a kwalejin horas da sojoji a Syria
A cewar matar, a zantawarta da Aminiya ranar Juma’a, “Na biyo tawagar ’yan uwana mata a motar haya daga Igun zuwa Legas da kuma sauran wasu jihohin kasar nan za mu tafi ziyarar Ibada wani kauye da ake kira Biakpan yankin Karamar Hukumar Biase da ke jihar Kuros Riba.
“Akwai wani rafi mai ruwan mu’ujiz da ruwansa yake wucewa ta gefen wurin ibadar da muka je sauke farali na tsarin addinin mu na Kiristanci bangaren Olumba.”
Ta ci gaba da cewa, “Mun yi imani ruwan yana warkar da cutuka ko wanne irin mutum yake fama da shi da mu mabiya muka yi imani da hakan.
“Mu mabiya darikar Brotherhood wato ta Olumba Olumba Obu. Sai daukacinmu muka shiga cikin ruwan rafin muna yin kurme saboda mu samu waraka daga cututtukan da suke damun mu a jikinmu a wannan kauye.
“Dama kuma ina fama da yawan laulayi da ciwon jiki sai na yanke shawarar bari in debi ruwan ins ha in yi wanka da shi ko na samu lafiya.
“Bayan mun gama aikin ziyarar ibadar mun koma gida kwanaki kadan sai na rika jin ciwon mara da ciwon baya kafin mu baro Biakpan zuwa gida Kalaba.
“Tun Kafin ma mu gama abin da muke yi na ziyarar ibadar a Kalaba na mayar da ruwan nan da na debo.
“Daga Nan fa sai na fara jin wasu abubuwa na motsi a cikina kamar su fito, na ji na matsu, sai na yi wuf na tafi bandaki naj e na tsuguna. Ina tsugunen ne na rika jin motsin wasu abubuwa a dubura ta na sanya hannu in jawo su.
“Nan fa na tsorata saboda yadda na rika jawo abubuwan suna fadowa ne har suka gama fita ban damu ba sai na Sanya waya ta ta hannu na dauki hoton abin da na kasayar sai na ga ashe wasu balli-ballin fasassun kwalabe ne na kasayar,” in ji Nkechi.