Maciji mafi girma a duniya
An gano macijin da ya fi kowane girma a duniya, a surkukin dajin da ya hade kasashen brazil da Kolombiya da wasu sassan Kudancin Amurka, d aake yi wa lakabi da Amazon (ko amazonia). tsawon macijin ya kai kafa 17. An gano wannan babbar halitta ne lokacin da ake daukar hotunan fim din BBC, mai […]
An gano macijin da ya fi kowane girma a duniya, a surkukin dajin da ya hade kasashen brazil da Kolombiya da wasu sassan Kudancin Amurka, d aake yi wa lakabi da Amazon (ko amazonia). tsawon macijin ya kai kafa 17. An gano wannan babbar halitta ne lokacin da ake daukar hotunan fim din BBC, mai taken : Alakar kabilu da Dabbobi da Ni (mutum). A nan mai gabatar da shirye-shirye a BBC Gordon Buchann tare kabilar Waorami a yankin dajin amazon da ke kasar Ecuador, inda suka rike wannan jibgegen maciji. kabilun da ke zaune a wannan yanki sun nuna wa Gordon sirrin yadda suke rayuwa a wannan kungurmin daji, ta hanyar, inda sukan yi amfani da sarewa da sanduna masu tsini, wajen farautar birai da aladun dawa. kabilun yanki na da tabbacin cewa, dabba mai cin mutane na tattare da makomar su, don haka ruhin su ke damfare da ba su muhimmanci.