Maciji mai kai biyu da ke sara da su ya bayyana

Masana binciken dabbobin dawa sun gano wani nau’in maciji mai kai biyu da yake amfani da su wajen sara da cizo. Kafar labarai ta Mirrow.co.uk ta ce wani mai kiwon halittun dawa J.D. Kleopfer ne ya fara sanya hoton macijin a shafin sadarwarsa na Facebook inda abin al’ajabin ya janyo hankalin jama’a da dama. An […]

Maciji mai kai biyu da ke sara da su ya bayyana

Masana binciken dabbobin dawa sun gano wani nau’in maciji mai kai biyu da yake amfani da su wajen sara da cizo.

Kafar labarai ta Mirrow.co.uk ta ce wani mai kiwon halittun dawa J.D. Kleopfer ne ya fara sanya hoton macijin a shafin sadarwarsa na Facebook inda abin al’ajabin ya janyo hankalin jama’a da dama. An samu macijin ne a wani lambun Richmond a jihar birginia da ke Amurka makon da ya gabata.

Hukumar kula da harkokin dabbobin dawa na birginia ta samu rahoton bayyanar macijin da mai kiwon jinsin halittun macizai ya sanar.

A yanzu dai haka an tafi da macijin don binciken masana a kan yadda macijin yake rayuwa da gangan jiki daya. Kleopfer ya bayyana cewa, wannan macijin abin al’ajabi ne da ba a cika samun irin wannan halittar ba, saboda ba su cika rayuwa a doron kasa ba har su yi tsawon rai, akwai kalubalen rayuwar macijin na yau da gobe.

Binciken da masanan dabbobin suka yi ya bayyana cewa, macijin na amfani da kai biyu da wurin numfashi biyu da zuciya daya sannan za iya yin sara da fitar da dafi da kowane baki.

Kleopfer ya dade yana mu’amala da macizai sama da shekara talatin shi da sauran masu mu’amala da macizai, sun ce samun irin wannan macijin ba karamin abin al’ajabi ba ne.

Masanan sun bayyana cewa, macijin ya kai tsawon inci 6 zuwa 8 yanzu haka macijin ya kai mako uku da haihuwa.

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100