Maciji ya fado kan ma’aikatan banki lokacin da suke ganawa a China
Wani maciji ya fado a kan wadansu ma’aikatan wani banki a lokacin da suke taro da safe a birnin Nanning Guangdi kudancin China. Macijin wadda mesa ce ta kai tsawon mita daya da rabi, kuma ma’aikatan bankin suna cikin tattaunawa a taronsu na safe ne sai suka ga macijin ya fado sharaf kamar yadda kafar […]
Wani maciji ya fado a kan wadansu ma’aikatan wani banki a lokacin da suke taro da safe a birnin Nanning Guangdi kudancin China.
Macijin wadda mesa ce ta kai tsawon mita daya da rabi, kuma ma’aikatan bankin suna cikin tattaunawa a taronsu na safe ne sai suka ga macijin ya fado sharaf kamar yadda kafar labarai ta CCTB+ ta China ta ruwaito.
Fadowar macijin a kan ma’aikatan bankin biyu ne ya tarwatsa taron da suke yi a lokacin.
Sauran ma’aikatan bankin sun yi firgita kan fadowar macijin wanda ya yi kokarin shigewa tsakanin kujerun bankin. An dai yi sa’a macijin bai illata wani daga cikin ma’aikatan ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan shi ne karo na biyu da maciji ke shiga reshen bankin na garin Guangdi. Sai dai hukumar ’yan sandan yankin ta ce za ta ci gaba da bincike kan yadda macijin ya shiga cikin ginin.
Masana macizai na ta binciken yadda macijin ke rayuwa a saman silin din.