Maciji ya kashe mutum 7, 15 sun kamu da ciwon kafa

Mutum bakwai ne suka rasu sanadiyyar cizon maciji a yankin Duguri da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi yayin da wata cuta da ke dura ruwa a kafa da ake kyautata zaton cutar dundumi ce ta sake bulla a garin. Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dokta Rilwanu Muhammad ne ya sanar […]

Maciji ya kashe mutum 7, 15 sun kamu da ciwon kafa

Maciji

Mutum bakwai ne suka rasu sanadiyyar cizon maciji a yankin Duguri da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi yayin da wata cuta da ke dura ruwa a kafa da ake kyautata zaton cutar dundumi ce ta sake bulla a garin.

Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dokta Rilwanu Muhammad ne ya sanar da haka lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi.

Ya ce suna zaton cutar dundumi ce ta sake bulla a garin Bara, kasancewar yankin na daga cikin inda cutar ta bulla a shekarun baya.

Ya ce sun tura kwamitin bincike don binciko abin da ke damun mutum 15 da suka kamu da cutar ta dundumin ce ko wani ciwo daban.

Shugaban ya ce a Jihar Bauchi za a samu mutum miliyan daya da ke fama da cututtuka daban-daban, wadanda ba a cika ba su kulawa ba.

Haka kuma ya ce akwai kusan mutum biliyan daya a fadin duniya da ke fama da irin wadannan cututtuka da ba a cika ba su kulawa ba.

A cewarsa, ire-iren wadannan cututtuka, rashin tsaftar muhalli da karancin ruwan sha mai tsafta ne ke kawo su.

Ya ce a misali, a Jihar Bauchi ana fama da cutar dundumi da makanta da tsutsar ciki da cizon kare da saran maciji.

“Idan har za a kula da tsabtar muhalli kuma a samu ruwan sha mai tsabta, za a magance wadannan cututtuka,” inji shi.

Shugaban ya ce Jihar Bauchi ba da dadewa ba za ta yi ban-kwana da wadannan cututtuka, kamar yadda aka yi ban-kwana da cutar kuturta a duniya.

Ya ce gwamnati na aiki da hukumomin ba da agaji na cikin gida da na kasashen duniya, domin ba da horo ga ma’ikatan kiwon lafiya don su ba da magungunan cututtukan a kauyuka.

Ya kara da cewa gwamnati za ta gina asibitin kula da cizon maciji a yankin Duguri da nufin magance matsalar yawan cizon maciji da ake samu.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya