Maciji ya sari wata mata da ta cije shi suka mutu tare
Wata mata da maciji ya sare ta a kasar Indiya, sai ’yan uwanta suka tursasatta ta ciji macijin, domin a tunaninsu kaifin dafin zai kasa cutar da ita. Wannan mata da ta fito daga Bihar ta hadu da ajalinta bayan da macijin mai tsananin dafi ya sare ta, amma kafin ta rasu ta gantsara masa […]
Wata mata da maciji ya sare ta a kasar Indiya, sai ’yan uwanta suka tursasatta ta ciji macijin, domin a tunaninsu kaifin dafin zai kasa cutar da ita. Wannan mata da ta fito daga Bihar ta hadu da ajalinta bayan da macijin mai tsananin dafi ya sare ta, amma kafin ta rasu ta gantsara masa cizo. |
Al’amarin dai ya auku ne a kauyen Shampur karkashin kulawar ’yan sandan gundumar Gopalganj ranar Asabar din da ta gabata.
Rahoto ya tabbatar da cewa Rajamrti Debi uwargidan Naresh Choube tana aiki a gidfansu sai maciji mai tsananin dafi ya sare ta. Da jin kukanta sai iyalan gidan suka taru suka kama macijin, sannan suka matsa mata kan lallai ta cije shi, inda ta yi ta cizonsa, har ta ji masa rauni. Daga bisani ciwonta ya tswananta sai aka kai ta asibiti tare da maciji a jaka, amma matar ta mutu nan take.
Rahotanni sun bayyana cewa matar na mutuwa suka dawo da ita gida, inda suka baro gawar maciji a kan teburin likitoci. Likitocin kuwa suka jefar da macijin a waje.
A watan da ya wuce, an ruwaito yadda waniu mutum da maciji ya sare shi ya ciji matarsa donm su mutu tare, amma likitoci suka samu ceto rayuwar mata, shi kuwa mijinyacin ya mutu. Lamarin dai ya auku ne a Bihar a wata gunduma Samaspur.