Macizai sun kori ’yan Boko Haram a dajin Sambisa
Wasu mahara biyu da ’yan banga na Sibiliyan JTF suka kama, sun ce ’yan kungiyar Boko Haram na tserewa daga dajin Sambisa zuwa sassan jihar da kasar Kamaru, saboda sarar da macizai ke yi musu a dajin. Maharan sun danganta bayyanar macizan kan asirin da iyayen ’yan matan Chibok suka yi.daya daga cikin wadanda aka […]
Wasu mahara biyu da ’yan banga na Sibiliyan JTF suka kama, sun ce ’yan kungiyar Boko Haram na tserewa daga dajin Sambisa zuwa sassan jihar da kasar Kamaru, saboda sarar da macizai ke yi musu a dajin. Maharan sun danganta bayyanar macizan kan asirin da iyayen ’yan matan Chibok suka yi.
daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Kolo Mustafa, ya ce macizai na addabarsu a dajin Sambisa, “Kuma akasarin mutanenmu sun gudu saboda yawan macizan da suka addabe mu a dajin, kuma da zarar macizan sun yi sara za su bace, wanda aka sare shi ba zai wuce kwana daya ba zai mutu, kuma an fada mana cewa mutanen Chibok ne suke turo macizan ta hanyar addu’o’i da tsafe-tsafe, don ramuwar gayyar ’ya’yansu da muka yi garkuwa da su,” inji shi.
Ya ce akasarin shugabanninsu sun gudu zuwa Kamaru, saboda idan suka tsaya a Najeriya ’yan banga da jami’an tsaro za su kama su cikin sauki, “A yayin da muka tsero nan Maiduguri wasu na zuwa kananan hukumomi ne don kila su tsira da rayuwarsu. Jiya muka zo da dare kuma muna kokarin boyewa a gine-ginen da ba a kammala ba ne kuka kama mu; amma yanzu muna rokon ku bar mu da ranmu, domin ba da son ranmu muka shiga cikin wannan kungiya ba, an kama mu da karfi ne, ni ban taba kashe kowa ba, amma abokina ya kashe mutane da dama,” inji shi.
Umar Abor da aka kama su tare ya ce “Ni da Kolo mun kashe mutane kuma mun yi yaki a shekarar 2010 a garuruwar Marte da Bama da Buni Yadi da Gwoza, daga baya muka zo Chibok, amma ba mu ga ’yan matan Chibok ba, saboda shugabanninmu ne suka san maganar ’yan matan.”
Ya ce: “Mun gudu daga dajin Sambisa ne saboda akasarin shugabanninmu sun bar dajin sakamakon sarar macizai, ba mu taba haduwa da macizai a wurin ba sai bana”