Macron ya buƙaci a dakatar da yaƙin Syria
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi kira ga ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar Syria da su mayar da wukakensu kube. Ya buƙaci a maido da zaman lafiya a kasar da ta kwashe shekaru tana fama da yakin basasa. Ba mu biya ’yan bindiga kuɗi don yin sulhu ba — Uba Sani […]
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi kira ga ɓangarorin da ke yaƙi da juna a ƙasar Syria da su mayar da wukakensu kube.
Ya buƙaci a maido da zaman lafiya a kasar da ta kwashe shekaru tana fama da yakin basasa.
- Ba mu biya ’yan bindiga kuɗi don yin sulhu ba — Uba Sani
- An ceto mutum 24 a hatsarin jirgin ruwa a Kogi
Kazalika shugaban ya kuma buƙaci da su kula da rayukan fararen hula da a koda yaushe ke zama a tsakiyar rikici idan ya ta so.
Kiran na Macron na zuwa ne bayan da mayaƙa masu jayayya da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Syria, suka ƙwace iko da kusan dukkanin yankunan Aleppo, wanda ke zama birni na biyu mafi girma a kasar.
Ƙungiyar da ke sa ido don kare haƙƙin al’umma a Syria — Syrian Observatory for Human Rights — ta ce gamayyar ƙungiyoyin tawaye ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Hayat Tahrir al-Sham sun danna zuwa birnin na Aleppo inda suka ƙwace galibin yankin na Arewacin kasar.
A halin yanzu dai gwamnan birnin da kwamandojin tsaro duk sun janye daga tsakiyar Aleppon, yayin kuma da dakarun gwamnati ke arcewa zuwa ƙauyukan da ke kewayen yankin.
Sai dai sojojin Syriar na cewa yawan mayaƙan na tawaye, ya sanya su sake salo na yaƙi, inda a yanzu suka ja daga domin yin amfani da wasu dabaru na maida martani.
A ranar Juma’a masu tada ƙayar baya suka kai hari kan birnin Aleppo, inda suka tayar da motoci biyu ɗauke da bamabamai, yayin da suka yi arangama da dakarun gwamnati a yankin Arewacin birnin.
Wannan shi ne karo na farko da dakarun adawa suka kai wa birnin hari tun bayan shekarar 2016, lokacin da aka iza ƙeyar su daga yankunan da ke makwabtaka da yankin gabashin Aleppo, biyo bayan wani gangamin dakarun gwamnatin Syriya, da Rasha, Iran da sauran ƙawayen su, suka marawa baya.