MADALLA DA BLOOM
BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (+2348065576011) na daya daga cikin mahalarta kwas din Manhajar Bloom. Ya rubuta wannan waka, wacce ya gabatar a ranar Jumu’ar da ta gabata a yayin bikin rufe kwas din a hotel din Chelsea, Abuja. Wakar, kamar yadda ya bayyana, sadaukarwa ce ga Mr. Paul S. Frank da Madam Lily Nyariki da kuma […]
BASHIR YAHUZA MALUMFASHI (+2348065576011) na daya daga cikin mahalarta kwas din Manhajar Bloom. Ya rubuta wannan waka, wacce ya gabatar a ranar Jumu’ar da ta gabata a yayin bikin rufe kwas din a hotel din Chelsea, Abuja. Wakar, kamar yadda ya bayyana, sadaukarwa ce ga Mr. Paul S. Frank da Madam Lily Nyariki da kuma dukkan mahalarta kwas din.
1
Godiya nake ga Jallah
Babban gwani mai adala
Sarkin Muhammadu mai Risala
Bautarka ba za ni zam bari ba.
2
Yau ga mu mun daura daga
Neman ilimi ganga-ganga
Don fadakarwa babu banga
ADEA ba za ta gundura ba.
3
Wannan training ya tara manya
Croshella-USAID ta kama hanya
Paul S. Frank ya kori tsanya
Da yardar Allah aikinmu ba zai gaza ba.
4
Madam Lily jaruma daga Kenya.
Na yi tafi nai jinjina ga manya.
Roberts gwarzo ka kai ni Kenya
kwarewarku ba sai da tambaya ba.
5
Ga gwaraza nan za ni zana
Mrs. Chioma ta zo ta zauna
Claris Ujam sai kin yi gwamna
Denja Abdullahi ANA babba
6
Marubutanmu mata da maza
Khalid Imam sannunku maza
Isyaku Bala ba ka aikin banza
Fasaha, hikima ba za mu daina ba.
7
Bilkisu Yusuf mai zamani
AHA Aminatu mai matani
Ku yi rubutu gyaran zamani
Aiki kuke ba za ku gaza ba.
8
Kenneth Gibson mai rubutu
Anthonia Opara rubuta rututu
Olarike Adesanya ba ratatu
Gyaran al’umma ba kwa daina ba.
9
Ebans Mensah za ni Ghana
Kwadwo Osei zo nan mu gana
Bashir Yahuza yau za ni Ghana
Zumunci Eyo Aku ba ma gaza ba.
10
Wanga workshop mun kammala shi
Bloom Software manhajar armashi
Godiya ga Allah mun yi murmushi
Addu’ar sauka lafiya ba za mu fasa ba.